← Book details Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 161

Sashe 72

Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya jima yana tattaunawa da su kafin daga baya ya tafi bayan ya yi mu su addu'ar samun nasara. Zuhayr baya buƙatan taimako indai na kuɗi ne ko connections dan ya fi Uncle Aliyu komai sai dai ko ba komai a lokaci irin wannan mutum ya kan ji daɗi idan ya samu support na 'yan uwan sa, shiyasa ma Uncle Aliyun ya zo dan ya nuna mu su ya damu da ɗan Yayan na sa.

Kullum sai Likita ta zo ta dubata kamar yadda Zuhayr ya buƙata kuma a wani zuwa da ta yi ne aka ma ta scanning inda ta gaya mu su cikin Zaytoonah satin sa shida. Zuhayr felt very happy, he cant wait to see his child.

John Torres shine shugaban Lab ɗin da aka ayi autopsy na gawan Linda Cannel kuma shi yai investigation ɗin. Mutum ne da ko kaɗan baya son musulmai ba dan komai ba kuwa sai saboda abinda ya faru 9/11 a shekarar 2001, inda aka kai hari a twin tower na ƙasar America wanda ya hallaka kusan mutane dubu uku da wani abu.
Ɗan John mai suna Samuel yana ɗaya daga cikin sojojin da su ka rasa ran su a wannan lokaci. Da ke ana alaƙanta harin da cewa musulmai ne su ka yi ƙarƙashin jagorancin Usama Bin Laden sai abin ya ƙarawa musulmai baƙin jini a idon mutanen America.

Da farko John bai san wa ake tuhuma da kisan ba shiyasa ya fara haɗa report na gaskiya. Amma a rana ta biyu da aka kawo gawan sai ga anonymous caller ya kirashi inda ya ma sa zancen duk yadda za ayi kar ya ba da report na gaskiya saboda wacce ta yi kisan musulma ce kuma da alama ana so a wanketa daga wannan laifi da ta aikata. Ya faɗa ma sa exact time da ya ke so ya saka cewa Linda ta mutu. Ƙiyayyar musulunci da ke ran John sai ta mamaye zuciyar sa. Ya nemo hotunan labarin a computer ɗin sa inda a nan ya ga hoton Zaytoonah lokacin da fito da ita daga gidan tana tsaye an sa ma ta ankwa a hannunta. Gyalen da ta yi rolling kan ta da shi kaɗai ya isheshi shaidar cewa ita musulmace. Ransa ya ƙara ɓaci dan haka ko tuna cewa laifi zai aikata bai yi ba dan haka washegari da ya koma office sai ya sake rubuta wani report ɗin ya jirkita komai kamar yadda Anonymous caller ya ce, ya maida report ɗin zuwa abinda zai implicating Zaytoonah.

Gobe za a kawo post motem report daga Lab dan haka tsoro da fargaba ya sa Zaytoonah a gaba duk yadda Zuhayr ya so ta kwantar da hankalinta ta yi bacci hakan bai yiwu ba.
"Zaytoon for our Baby's sake ki kwantar da hankalin ki please"

Ita fa mantawa ta ke yi da wani wai tana É—auke da baby a cikinta. Ba wani chanji a tattare da ita, ko cikinta ba ta ga ya taso ba. Abinda za ta iya faÉ—i shine tun ma kafin ta san tanada cikin tana yawan jin kasala amma kusan komai za ta iya cewa normal ta ke sai yanzu kuma da damuwa ya zo ya sa ta a gaba.

"Ok bari mu yi abu É—aya. Ki bani labarin ki sai na baki nawa, na san kafin ma na gama nawa labarin kin yi bacci"

"A'a kai ka fara bani labarin ka"

Tana manne jikinsa ya shiga ba ta labarin rayuwar sa. Yadda ya rasa iyayen sa tun bai wani girma ba, yadda yai fama da rayuwa har ya zama abinda ya zama. Tun kafin ya gama high school ya fara sauye-sauye a gidan gonan iyayen sa wanda ya sa cikin shekaru biyu su ka samu haɓaka sosai da wannan riba da su ka samu ya ɗeba duka kuɗin ya zuba jari a wani kamfani da ta ke haƙo ma'adanai na gold da silver. By the time ya gama degree a university already shi da Ben suna da plan na abinda za su fara dan haka da kuɗin da ya taru na hannun jarin da ya ke da shi da kuma wasu kuɗi da Ya karɓa a wajen Kakan sa Mr Haddish ya samu ya buɗe kamfanin sa. Cikin shekaru biyar kamfanin ta haɓaka ta samu cigaba sosai, and @ 25yrs he's already a millionaire. Yanzu da ya ke shekaru 34 ana irgashi cikin mutum goma da su ka fi kowa kuɗi a Las Vegas. A Jahar Nevada gaba ɗaya ma idan ana irga top 25 sunan sa yana faɗawa ciki. Ba dan ya ji maganar Alinah ba da yanzu ma ya fi haka, a da yanada hannun jari a wani babban Casino da ke Vegas ɗin, inda ake buga chacha a sha giya ayi duk wani baɗala. Amma shigowar Alinah rayuwar sa da ta nuna ma sa haramcin hakan sai ya siyar da hannun jarin, bisa shawarar Alinah sai yai amfani da kuɗin wajen turawa refuge camps na 'yan gudun hijira.

Har lokacin da ya gama labarin sa ba ta yi bacci ba idon ta garau. Ta jinjina ma sa na rasuwar iyayen sa wanda hakan ya tuno ma ta da na ta uban. A hankali ta soma bashi labarin soyayyar iyayenta, labari ne da ta taso da shi saboda yadda Daddy ke karanto ma ta shi a duk lokacin da ta buƙaci ya ba ta labari mai daɗi. Da farko ma ba ta ɗauka labarin iyayenta ba ne sai da ta fara wayo ta gane saboda koyaushe labarin Ɗan Fulani da Inkiru Inyamura ne taken labarin. Ta faɗa ma sa komai da ta sani har zuwa rasa mahaifin su da aka yi har yau babu shi ba labarin sa.
Jikin Zuhayr yai sanyi, yanaji tana kuka lokacin da ta ke nanata yadda ta ke son Daddynta da yadda ta yi missing ɗin ta amma bai hanata kukan ba sai ma kwanta da kanta da yai a ƙirjin sa yana ɗan bubbuga bayanta a hankali. Ta jima tana shesheƙar kuka kafin daga baya ya ji shiru ashe ta yi bacci ne. A wannan daren ya ɗau alkawarin nemo ma ta mahaifinta ya kuma yi alkawarin sai ya nemo Uncle ɗin Mommy ya gurfanar da shi a kotu ya sa an hukuntashi bisa laifuffukan sa...

***
Allah ba azzalumin bawa ba ne. Haka nan duk abinda Allah ya rubuta babu mai iya chajashi.

A yayinda John Torres da Ben su ka yi niyyar tarwatsa Zaytoonah. Allah bai ba su dama ba, hakan ba ya cikin ƙaddararta, baya cikin abinda Allah ya nufa gareta shiyasa ko da sama da ƙasa za su haɗu ba za a samu damar cin galaba a kan ta ba.

John da ya fito daga gida zai tafi Lab kafin daga nan Idan police sun zo ya damƙa mu su report sai kawai yai hatsari a hanya. Aka wuce da shi Asibiti saboda raunuka da ya ji sosai.
Hatsarin sa ba zai sa a fasa abinda aka yi niyya ba tunda yana da assistant kuma an riga an gama komai dama akan gawar report kawai za a bayar.

Inda Mr Torres ya ke ajiye files na shi kaf assistant ɗin sa ta duba amma ba ta ga file ɗin gawa mai lamba 50879 ba dan haka ta buɗe computer dan ta sake printing ɗin sa tunda duk wani report akan computer ake ajiyewa kafin a ajiye printed copy ɗin a cikin file. Tana duba date ɗin da aka kawo gawan ta ga report na farko da Mr Torres ya fara yi dan haka ta yi saurin printing ɗin sa ta kai office ɗin Deputy ɗin Mr Torres wanda ya karanta report ɗin ya ga ba matsala tunda duk da ba shi yai aiki akan gawan ba amma ya bibiyi labarin gawar a wajen wani intern da ya taya Mr Torres aikin. Bayan ya duba ya sa hannu sannan ya buga stamp ya miƙa ma ta...

"Na baki abinda zai sa ki nitsuwa?" Ya faɗa yana ƙyafta ma ta ido lokacin da su ka sauko ka sa ya ga tana ajiyar zuciya akai-akai saboda fargaba.

"Zuhayr ina tsoro"
Matsowa yai daf da ita ya ce "barin baki maganin tsoro to"

Ta buÉ—e baki za ta yi magana ya ce "rufe idon ki"

"Ni kam"

"Babu jayayya kirufe ido kawai"

Tana rufe ido ta ji saukar lips É—in sa akan na ta wanda ya sa ta waro iso waje.
A hankali ya shiga kissing ɗinta softly, da farko lips ɗin ƙasa ya ke tsotsa daga baya ya koma na sama ya cigaba da tsotsa slowly kafin daga baya ya chanja salon ya kamo harshenta ya fara tsotsa.
Zaytoonah wata duniya ta shiga na daban, sau biyu da ya taɓa kissing ɗin ta duk briefly ne amma wannan kam a yadda su ke tafiya ƙila za su shekara ne a wajen dan ba shi da niyyar dena wannan soyayyar.

Ƙaran fashewar glass ne ya dawo da su duniyar da su ke ciki ta ainihi.

Ben ne tsaye wajen dining yana huci kamar wani tsohon maye.

Zuhayr ya kalle shi ya ce "are you Ok?"

"Yeah" ya furta kaman zai yi kuka.
Wani abu ne ya tokare shi a zuciya lokacin da ya ga Zuhayr ya juya ga Zaytoonah yana ma ta magana. Da Zuhayr ɗin da ya sani da ne da gudu zai yi ya ƙariso inda ya ke ya tabbatar babu abinda ya sameshi. Amma wannan bai damu ba.

"See, na faÉ—a miki inada maganin cire tsoro"

Da sauri ta rufe fiskarta da tafukan hannunta biyu.

"Idan kina son maganin cire kunya ma ina da shi"

Ba tareda ta buÉ—e fiskarta ba ta fara girgiza ma sa kai.
"Na baki ne?"

"A'a ba na so" ta faÉ—a da sauri bayan ta buÉ—e fiskar.
Shi kuwa sai ya fara dariya hakan ya sa ta wuce gaba za ta fita yai saurin riƙo hannun ta yana faɗin "not so fast Baby girl".

Yau ma kamar koyaushe sai da 'yan Jarida su ka cike bakin station É—in ana jiran su. Amma ba su kula kowa ba su ka shige ciki.
Chapter 72 · 0% Book details