← Book details Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 161

Sashe 47

Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A gigice ta fito daga mota wanda ta samu Auwal na goye da Sadiq yayinda Hajjo ke gefe tana kuka. Da ta fito ta ƙarɓi Sadiq ta ce Auwal yai tuƙin. Ita da Sadiq a baya Hajjo da Auwal na gaba.

"Mommy sanyi na ke ji" Sadiq ya faɗa yana ƙara ƙanƙame Maryam.

"Ka yi haƙuri mun kusa Asibiti" tana maganan tana cire hijabin jikinta tana ƙoƙarin lulluɓeshi da shi.

"Mommy za ki dafa min shinkafa irin na ranan?"

"Zan dafa ma ka kaji É—ana, zan dafa ma ka duk abinda za ka ci"

"Irin wannan mai red and green and yellow É—in nan. Ki ka ce carrot is red, corn is yellow and, and, and"

"Peas and green beans are green and we have our delicious..."

Ya amsa da ƙarfin sa "fried rice"

Ta yi dariya wanda ya taho da hawaye.
Hajjo na gaba ta toshe bakinta da gefen hijabinta dan kar aji kukan ta. Ta fara cire rai da Sadiq, shima ta san ba jimawa zai yi ba kamar É—ayan. Kafin Maryam ta zo suman sa sau biyu.

Maryam na jin Sadiq na wani irin shiɗewa ta fara Innalillahi tana kiran sunan sa da ƙarfi.

"Daddy" ya kira kaman shi ke kusa da shi sai kuma ya sake jiki dai-dai Auwal ya karya kwanar shiga Asibitin.

Ana tsayawa Hajjo ta fito da sauri dan ta taimakawa Maryam ta fito da Sadiq tunda ta yi nauyi yanzu.
Za ta karɓeshi Auwal ya ce ta bari zai ɗaukeshi.
Tunda ya fito da shi daga cikin motan zuciyar sa ya karye amma ya daure yana tunanin ƙila Sadiq ɗin suma yai.

Haka su ka shiga Asibitin shi da Hajjo da sauri ita kuma Mommy ta tsaya saka hijabi.
Suna tsatstsaye sun yi zuru-zuru likita ya gama duba pulse É—in sa da heartbeat ya ce "i'm sorry, he's dead"

Cikin Maryam ya murɗa ta yi ƙasa da sauri tana ƙara saboda zafi da ta ke ji.

Auwal yai kan Mommy ita kuma Hajjo ta yi kan gawan É—anta da ke kwance...

Har safiya Mommy ta kasa haihuwa dan labour ne ya taso ma ta gadan-gadan ga kuma jininta da ya hau, hakan ya sa aka fara shirin yi ma ta CS.
Lokacin da aka ciro ɗan Maryam an jima da kai gawar Sadiq Maƙabarta. Daga maƙabarta straight Muntari Asibiti ya taho inda ya samu an ciro kyakykyawan Baby Boy ɗin Maryam. Saboda Maryam ba ta farfaɗo ba dole ya tafi bayan an tabbatar ma sa da Maryam da Babyn su na nan lafiya.
Zaytoonah, Maman Fawaz da Altine wata maƙociyar su su suka zauna a Asibitin saboda sauran 'yan uwa duk ana chan ana zaman makoki...

***

*Bayan shekara É—aya*

Goye ta ke da As-Sadiq tana ɗan jijjiga shi saboda muran da ya ke yi ya sa mi shi zazzaɓi. Kuka yake yi tun ɗazu amma yanzu yayi shiru tana tunanin ma yayi bacci. C V ɗin ta ta ke son haɗawa amma kukan shi ya hanata shiyasa ta goye shi.

"Assalamu Alaikum" Zaytoonah ta yi sallama tareda shigowa cikin Falon.

"Oyoyo junior, Oyoyo"

"Yayi bacci ko?"

"Eh"

"Je ki cire uniform ki zo ki karɓeshi"

Da gudu ta shiga É—akinta. Dan ita ce uwar renon junior. Shima kaman Sadiq da ya rasu Abubakar As-Sadiq aka sa ma sa sai dai junior su ke kiran shi. Bayan haihuwar sa abubuwa da dama sun faru ciki kuwa har da raba auren Tijjani da Hajjo.
Rashin T J da rasuwan Sadiq ba ƙaramin giɓi ya kawo a rayuwar Hajjo ba. Gidan ya ma ta faɗi, kaɗaici ya isheta ta dawo ma sai dai ta je ta wuni a gidan Muntari duk dan ta kasance da Humairah amma ita kuma baya-baya ta ke yi da ita. Wata takwas da rasuwan Sadiq watarana Maryam ta dawo daga Ta'aziya ta haɗu da Hajjo a gidan ta. Ba ta yi mamaki ba tunda tun da aka yi arba'in ɗin Sadiq lokaci zuwa lokaci ta kan zo su gaisa.

"Mommyn Zaytoonah zan koma ƙauye"

"Ban gane ba, Mi za ki yi a ƙauye?"

Hajjo ta sunkuyar da kai ta ce " ba ni da wani sauran kwanciyar hankali a nan. Har yanzu Baban su shiru ba labarin sa, na yanke shawaran zan je kotu a raba aurenmu. Ko da Hamma zai dawo yau cewa zan yi ya sake ni, tun farko son zuciya ya sa na zauna tunda ya min bayanin za mu dinga haifan 'ya'ya ma su sickler idan muna tare. Duk wahalhalun da mu ka sha akan Sadiq ƙarshe shima sai da ya tafi" ta ƙarisa maganar tana share hawaye.

"Hajjo ki yi haƙuri dan Allah, ina da yaƙinin Daddyn su ya kusa dawowa. Ba za ku sake haifan sickler Insha Allahu, ga Humairah nan lafiyar ta ƙalau"

"Ki shige min gaba kawai na samu yadda zan yi a raba auren nan. Na riga na tsayar da magana"

Duk yadda Maryam ta dinga ƙoƙarin convincing ɗin Hajjo ta ƙi yarda. Ƙarshe dai dole Maryam ɗin ta yarda da decision ɗin ta...

Cikin ƙanƙanin lokaci aka raba auren Hajara da Tijjani bisa dalilin an rasa Tijjani kusan shekara biyu, ko yana raye ko baya raye ba a sani ba.

Bayan komai ya kammala ne Maryam ta zaunar da Hajjo ta ba ta shawara akan gara ta zauna a Ringim ta nemi sana'a ta fara yi tunda dai ta wajen Uwa ta haÉ—a jini da T J, ba wanda zai hanata zama a family house É—in su T J É—in.

"Kin ga zama shiru ba daÉ—i. Ga dubu goma nan ki je ki yi tunanin sana'ar da za ki fara idan kin je"

Hajjo ta fashe da kuka. Ba ta taɓa jin zafin rashin makarantar ta ba irin na yau. A lokacin da T J ya dage sai ta yi karatu ta ƙi yau ga ranan karatu. Da tana da kwali ko da na sakandare ne za ta samu wani aikin da za ta dingayi a wata tana samun kuɗi. Ita tun asali ba abinda ta ke yi, sa'ilin da ta ke budurwa ne ma take ɗan taɓa kitso haka.

"Ki yafe min Mommyn Zaytoonah, duk abubuwan da na miki ki yafe min dan Allah"

Maryam ta ce ta yafe ita ba ta riƙeta da komai ba. Tausayin ma Hajjon ta ke yi sosai fiye da kan ta. Gara ita tana aiki amma Hajjo fa, ta yi zaman birni ne kawai amma har yau ba ta waye ba.

Sati guda da yin haka Hajjo ta koma Ringim da zama. Auwal ya dawo gidan Maryam da zama aka kulle wancan gidan.
Wata biyu da haka sai ga Auwal ya zo ya samu Maryam da cewa ya ga wasu suna parking cikin gidan da ya tambaya su ka ce ma sa haya su ka karɓa a wajen Alhaji Muntari.

"Allah shi kyauta" ta ce dan ta riga taga take-taken Muntari tun bayan da aka raba auren Hajjo.

Ba za ta manta da maganar sa ba safiyar wata Asabat *"Maryam ke ma fa har yanzu kina da ƙuruciyar ki. Shekara biyu ba wasa ba ne kina da damar ɗaukan matakin irin na Hajjo"*

*"idan ka gama maganar banzan ka ka tashi ka bar min gida"* ta faÉ—a tana tashi daga falon.

Tundaga lokacin ya ɗau saran zuwa akai-akai ya fake da cewa ya zo duba 'ya'yan sa ne tunda yanzu hakkin su na kan sa. Indai yaran na nan za ta shige ɗaki ta bar su da shi idan ba sa nan kuma ta shige ɗaki ta sa key idan ya gaji da zama ya tafi. Ba ta son kula shi dan abubuwan da ke kanta sun yi yawa balle ta tsaya ɓata lokaci akan wani banza wai shi Muntari.
Wani lokaci har 'yar sa Maryam ya ke kawowa wai ta gaisa da yayyen ta. Kafin ya kawo maganar banzan nan ta kan kula yarinyar duk da ta san saboda ita ya sa ma ta sunan Maryam. Watan Junior biyu da sati biyu Hanne ta haihu tun a Asibitin ya kira Maryam yana ce ma ta Hanne ta sauka an samu takwarar ta mai suna Maryam...

Bayan ta gama haÉ—a CV É—in ta ta kai gidan Alhaji Iliyasu Mai Auduga wanda shi ya aiko ta kai ma sa. Vacancy aka ba shi har guda biyu a Nuhu Bamalli Polytechnic shine da ya haÉ—u da Auwal a masallaci ya ce ya cewa Maryam ta zo yana neman ta.
Lokacin da Auwal ya gaya ma ta saƙon Alhaji Iliyasu ba ta kawo komai a ranta ba duba da kyakykyawar alaƙar da ke tsakanin sa da T J. Lokacin ɓatan T J da ya yi wata uku lokacin da Alhaji Iliyasu ya dawo daga Hajji dubu Hamsin ya aiko ma ta tareda buhun shinkafa da rabin buhun sugar da jarkan man gyaɗa da na manja guda bibbiyu ya ce su raba ita da Hajjo. Ɗan tsohon ya damu da ɓatar mai sunan Shehu ba kaɗan ba. Duk da matsayin Uba ya ke ga TJ amma yadda su ke mu'amala ka ɗauka abokai ne.

Bayan ya ma ta maganar aikin koyarwa sai da ta je gida ta nitsu ta yi shawara da zuciyarta ta kuma yi addu'a kafin ta amince da maganar...

***

A gida ya sameta ita É—aya a falo tana haÉ—awa students É—in ta note É—in da za ta yi wa students É—in ta gobe a class. Junior na wajen Zaytoonah a É—aki tana mi shi wasa.

Fiska a murtuke ta amsa sallamar sa. Ko gaisheshi ba ta yi ba ta cigaba da abin da ta ke yi.

"Ina Zaytoonah?"
Ta ji abinda ya ce amma ta shareshi.

"To dama Makaranta ne na chanja ma ta, ta fara shiri nan da sati biyu ce tafiyar" ya ajiye wasu takardu a saman takardan da Maryam ke dubawa.

Ta É—ago ta kalleshi sannan ta É—au takardan ta fara dubawa. Takardan transfer ce daga makarantar da Zaytoonah ta ke zuwa wata makaranta da ke Lagos. Not just makaranta, boarding school ne.

"Amma ka san SS3 kawai ya rage ma ta shine za ka je ka wahalar da kan ka wajen kai ta boarding school"

"Na sani, so na ke ta yi hankali, zama a gida ya sa ta sangarce dayawa"
Chapter 47 · 0% Book details