← Book details Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 161

Sashe 48

Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana so ta ce masa Lagos yayi nisa amma ta yi shiru dan ta san dan ta yi magana ya aikata abunda ya aikata. Kwanakin baya da ya sa mutane haya a gidan T J ido ta zuba ma sa, shi da kan sa ya zo ya ke cewa yayi hakan ne saboda kar a bar gida ba kowa, kuma abinda ake samu za a toshe wani hidiman da shi. Ta ce ma sa Allah ya kyauta.

"Ka ce tafiyar nan da sati biyu ko?"

"Yes"

Ta yi murmushi ta ce " Insha Allahu za ta shirya kafin nan. Idan babu wani abu za ka iya tafiya"

Ba haka ya so ba, ya so ta damu ne har ta roƙe shi akan ya janye maganar sa, shi kuma yai amfani da hakan ya ƙara jawota gareshi. Ya gane 'ya'yanta su ne weakness ɗin ta.
Gwiwa a sace ya tashi ya fita.

Sai bayan ta tabbatar a makarantar su Zaytoonan gameda transfer ɗin kafin ta samu Zaytoonah da maganar. Ba wai dan tana son tafiyar Zaytoonah ba ne a'a, sai dai dan ta ƙure iskancin Muntari da renin hankali.

As expected kuka Zaytoonah ta dinga yi akan ba za ta je boarding ba, boarding ɗin ma Lagos ga uwa uba ba ta son tafiya ta bar Maryam saboda zamanta a gida ba ƙaramin ragewa Maryam ayyuka ta ke yi ba.

Maryam kam tun tana lallashi har ta rabu da ita ta ce kar ta shirya, ita da Uncle É—in ta ne ba ruwanta a ciki.
Daga baya kuma da ta ga lokacin ya ƙarato Zaytoonah ba ta saki ranta ba sai ta koma yi ma ta nasiha tareda nuna ma ta cewa shekara ɗaya ce kawai za ta yi, shikenan ta gama...

Free pages zai ƙare a pg20 Insha Allah

*Don samun daman karanta cigaban labarin za a biya 300 ta account number kamar haka:*
3099546325
Firstbank
Azizat Hamza
*ko kuma katin MTN na 300 zuwa ga wannan numbar 08137311900*
Za'a tura Shaidar biya zuwa ga wannan numbar still 08137311900 ko kuma ma dai domin ƙarin bayani za a iya tuntuɓar numban, preferably chat ko text.
*Allah ya ba da ikon biya amin*
2/11/21, 10:04 PM - ****: *Chronicles of*
*...... ...... .......ZAYTOONAH*

https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref

𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊©
*(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*

Rubutawa.....Azizat
Wattpad@Azi_zat

*Last Free page*
*20-Mrs Zaytoonah*

Bismillahir Rahmanir Rahim

Shirye-shirye ake yi na zuwa graduation ɗin Zaytoonah. Jiya Muntari ya kawo ma ta ticket ɗin jirgi amma ta yi banza da shi ta ce ya kwashe tsiyar sa ba ta so. Ta riga ta tsara tafiyar tuntuni dan haka ba ta buƙatar taimakon sa, da gayya ya tura 'yarta gari mai nisa dan kar ta dinga zuwa ma ta visiting. A Kaduna za su je su shiga babbar Mota da zai kai su Lagos. Hatta inda za su sauka sai da ta tsara shi kafin ta ɗau aniyar tafiyar. Gidan wata ƙwarta ne da su ka yi Law school tare a Abuja. Lokacin da su ka yi Law school ɗin ba ta yi aure ba amma yanzu aure ya kai ta zama a garin Lagos.

Dukkan su sabbin É—inkuna su ka yi har Auwal ma, Salman da Junior É—inki iri É—aya ta mu su.

Ana gobe za su tafi ta je gidan Muntari ta yiwa Hanne sallama wacce yanzu zaman ƙaddara kawai ta ke da Muntari. Lokacin da ta ke da cikin Maryam ta gano Muntari Maryam ɗin Tijjani ya ke so. Hotunan ta birjik a kan gadon sa watarana da ta shiga ɗakin sa za ta kira shi saboda yayi baƙi.
Tana cikin duba hotunan ya fito daga banÉ—aki.
Hawaye fal a idonta ta ce "yanzu dama duk wannan haukar da ka ke yi akan Maryam ashe Anty Maryam É—in Hamma Tijjani ka ke so?"

"Ba na son shishshigi ki tashi ki bar min É—aki"

"Haba Muntari ka ji tsoron Allah. Ka san fa tana da aure kuma Yayan ka ta aura amma ka gaza haƙura da ita ba wallahi ka ji kunya"

"Kar ki sake min maganar banza Hannatu, zan mugun saɓa miki"

"Tir da wannan halin rashin kunyar na ka, haba Muntari ko kunyar nan ta Fulani ba ka da ita balle ta musulunci. Matar Yayan ka fa, Matar Yayan ka Uwa É—aya Uba É—aya"

Harzuƙa yai da kalamanta ya shiga dukanta. Ihun ta da Iya ta ji ne ya sa ta haura sama da sauri ta je ta samu Muntari na dukan Hanne wanda sai da aka haɗa da zuwa Asibiti saboda jini da ya fara fitowa daga gabanta. Da rabon Maryam za ta zo duniya ne da ta mutu tun a ciki a lokacin.
Lokacin Iya ta yi fushi sosai da Muntari amma ba ruwan sa ko haƙuri bai ba ta ba, bai kuma nuna ya damu ba. Daga baya kuma a cikin shekarar ya biya ma ta Umara nan da nan zance ya wuce a wajen Hajiya Iya. Lokacin da ta dawo sai da ta je Ringim ta yi sati biyar kafin ta dawo. Ana zuwa ana ma ta barka sai burga ta ke yi a dole ita Hajiya. Wani abun idan Iya ta yi sai ka kama baki saboda shirme ne kawai da jahilci. A lokacin kuwa an samu cikin 'yan uwa dayawa da su ka yi tallen 'ya'yan su ko za ta haɗasu Aure da Muntari amma ta sani ko ta amince ma kunya za ta sha dan Muntari ba Tijjani ba ne, Hanne ma da ya yake zama da ita balle a masa zancen ƙarin aure.

Da ke Allah ne ke kiran bayin sa a shekara na gaba da Iya ta je Umara Goggo ta je Hajji. Mijin jikanta Asma'u ne ya biya mu su ita da Asma'un da mahaifiyar sa da wata yayar sa su ka yi tafiyar ayari.
Ikon Allah sai kallo domin kuwa ganin Goggo ta je Hajji ya sa tsohon kishi da Hassadar Iya ya tashi. Ta shiga yiwa Muntari maganar itama na son zuwa Hajji. Da farko bai kulata ba daga baya kuma da 'yan mutuncin su ka shigeshi sai ya biya ma ta. Yanzu haka kwanan ta biyu da dawowa daga Hajjin ta wuce Ringim satin ta É—aya ma a chan.

Maryam da ta je wajen Hanne ne ta ke ma ta tsegumin komai. Maryam ta ce ita Iya ta daina ba ta mamaki tausayi ma ta ke ba ta. Su na cikin hiran ne sai ga Humairah ta shigo gidan tana ganin su zaune amma ta kauda kai za ta wuce su, Hanne ta ce "yanzu Humairah cewa za ki yi ba ki ganmu ba? Idan ni ba za ki gaisheni ba Mommyn ki fa?"

Ta wani juyo a yangance ta ce "Sannu Mommyn Zaytoonah"

Maryam ta ce "Sannu Humairah ya karatu?"

"Ƙalau" ta faɗa ta wuce ba tareda ta yiwa Hanne magana ba.

"Humairah ce ta zama haka?" Maryam ta faÉ—a tana kallon Hanne"

"Ai Anty Maryam kaɗan ma ki ka gani, a gidan nan ba mai gaya ma ta magana ta ji idan ba Muntari ba shi kuma ba ruwansa da tarbiyyan ta. Shi dai kawai indai kuɗi ta ke buƙata zai ba ta. Yanzu haka wata ƙatuwar wayar blackberry ya siya ma ta"

Maryam ta ce Allah ya kyauta...

Zaytoonah ba ƙaramin jin daɗi ta yi ba ganin dukka 'yan gidan su sun zo ma ta. Sai nan nan ta ke da su, tana nunawa manyan ƙawayenta iyayenta. Anci an sha kuma an yi hotuna. Zaytoonah ta karɓi kyaututtuka har guda uku wanda ya sa Maryam ta yi farinciki da chanjawar 'yar tata. Atleast ba ta bari ɓatar Mahaifinsu ya dawo da ita baya ba.
Bayan kwana biyu da yin graduation É—in dukkan su suka dawo gida.

Bayan ta huta ta tafi hutu Ringim dan ta jima ma ba ta je ba. Mutum biyu su ke sa ta farinciki su ke kuma sa ta É—okin zuwa Ringim É—in wato Yadikko da Goggo. To Yadikko ta rasu saura Goggo, da ta je ma a É—akinta ta sauka ta dinga ma ta tsiya wai ta zama gurguwa tunda ba ta iya tafiya mai nisa sai da sanda.

A kwananta na biyar da zuwa gidan da yammaci tana farfajiyyan gidan tana yiwa Goggo yankan farce, wasu mata na wanke masara mai yawa dan zai yi rabin buhu za su jiƙashi saboda a bushar a niƙa shi saboda garin tuwo.
Tana yiwa Goggo yankan farce tana tanka mu su saboda surutun su da gulman su yayi yawa sai ga yaro yayi sallama wai ana kiran Zaytoonah. Zaytoonah ta ce waye? yaron ya ce bai sani ba.
"Ka ce ma sa ba ta nan"

"Ke kuma kin yi mashinshini za ki kore shi? Ki ka sani ko shi ne Angon"

"Allah ya kiyaye. Ba Mashinshini ba Mai lashe mutane na samu"

"Allah ya baki haƙuri jikar Iya da Goggo, 'ya a wajen Boɗɗiyon Tijjani"

"Gyara maganar ki na baki ƙwandala. Jika ce a wajen Goggo da Baffah Habu Allah ya jiƙan rai" tana maganar kuma sai ga Iya ta fito daga ɗaki kuma sarai ta ji mi Zaytoonah ta ce. Ranta ya sosu da maganar Zaytoonan amma ya za ta yi tunda koma mi Zaytoonah ta ce ita ta jawa kan ta...

Washegari ma sai ga shi an sake aikowa wai Zaytoonah ta fito. Wannan karan kam so ta ke ta ga wani É—an iskan ne ke neman faÉ—an ta.

"Ehen, miye ka ke nemana?" ta faɗa tana riƙe ƙugu.

Sai wani sunne kai ya ke yi irin kunyar nan.
"Idan ba ka da abin faɗa ni zan shiga ciki kuma idan ka ƙara sawa a kirani tafasashshen ruwan zafi zan zo na zuba ma ka"

"Dama Baffa Muntari ne ya ce na zo mu dai-dai ta"

Ta fashe da dariya har da riƙe ciki. Sai da ta yi mai isharta kafin ta ce "mu dai-dai ta, Kaji ka ke sayarwa ko Raguna?"

Ya É—an É—ago ya kalleta amma yadda ta tsareshi da ido ya sa shi sunkuyar da kai ya ce "shi ne ya turoni wai mu yi zance mu fahimci juna"
Chapter 48 · 0% Book details