← Book details Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 155 OF 161

Sashe 155

Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ƙarfe uku saura kwata Galadima ya tashi ya ɗauro Alwala ya fito. Har lokacin Zaytoonah ba ta tashi ba yaushe ma ta samu ta yi baccin bayan gwarzonta bai iya ɗaga ma ta ƙafa ba.

Sai da ya shimfiɗa sallaya kafin ya ƙariso gadon ya fara murza kunnen ta a hankali yana kiran sunan ta.

"Princess ta shi mu ribaci wannan dare"

Lokacin da ba Azumi ba ma ba ya wasa da sallar dare balle yanzu da aka shiga Azumi.

Da ƙyar ta buɗe ido dan har ga Allah bacci ne a idonta sosai.
Sai da ya tabbatar ta tashi ta shiga banɗaki kafin ya ƙarisa wajen sallaya ya tada sallah.

Allah na gani raka biyu kawai ta yi ta ɗan yi addu'a kaɗan ta kwanta akan sallayar. Shikam da ya gama nafilfilun ƙur'ani ya ɗauka ya fara karatu. Sallar dare da yawan tilawa shi ya sani na ɗaya daga cikin abinda ya ke zama ma sa kariya daga sharrin maƙiya. Ya sani yanada maƙiya na kusa da na nesa but amma a duk lokacin da yai addu'a ya haɗasu da Allah yana da yaƙinin babu wanda ya isa ya cutar da shi. Tun lokacin da tsohon Galadiman gari ya rasu aka fara raɗe-raɗen za a bashi ya shiga cikin wani tsanani dan yau lafiya gobe babu haka ya dinga fama a lokacin hakan ya sa Malamin da ya ke ɗaukan karatu a wajen sa ya ce ya dinga yin alwala kafin ya kwanta sannan ya tashi da dare yai sallah ko da raka'a biyu ne kacal. And a hankali jikin sa yai sauƙi, wasu ƙulle-ƙulle da ake shirin yi duk Allah ya wargaza su.

Sai ƙarfe huɗu da rabi ya tashi Zaytoonah dan su ci suhur duk da shi ba ma'abocin cin abu mai nauyi ba ne.

Washegari Humairah ne ta kawo ma ta Alinah dan 'yan biyu kam sai su Mommy sun wuce Makkah za'a kawo ma ta su.
Galadima gani yai har su ka shirya har su ka shiga mota su ka yi nisa bai ga an bawa Alinah abinci ba. ya ce " ni kan 'yar tawa Azumin dole ki ka sa ta ne?. Wannan horon yunwan yai yawa"

Murmushi ta yi sannan ta kamo hannunsa ta ɗaura a ƙasan cikin ta ta ce "na yayeta saboda ƙanin ta na bani wahala"

Galadima ya zaro ido waje.
Ta sani ba dan Azumi ba, ba kuma dan kar Dreba ya ganshi ba da ba abinda zai hana shi kissing É—in ta.

"Alhamdulillah, Alhamdulillah"
2/11/21, 10:04 PM - ****: 75

Bismillahir Rahmanir Rahim

*The wedding*

"Ki zauna Ghazala"

"Abu Razz Dan Allah ka yi haƙuri. Na yi nadama, na tuba. Ka maidami ɗakina dan Allah" ta ƙarisa maganar tana matsar hawaye.

Sau É—aya ya kalleta sannan ya kauda kai ya ce "ki tashi ki zauna ba na son wannan tsugunnon"

Tunda ta shigo ta ajiye jaka ta saka gwiwowinta ƙasa ta fara bashi haƙuri.

Da ƙyar Ghazala ta miƙe ta zauna akan kujera tana fuskantar mutumin da a duniya ba abinda ta ke so da ya wuce ta sake komawa gidan sa.

Bai yi magana ba sai ma rubutu da ya cigaba da yi.

"Ranka shi daÉ—e abinda ya faru sharrin shaiÉ—an ne, kowanni ÆŠan Adam yanada rauni. Ka yafemin Dan Allah"

"Wallahi duk abinda ka ke so idan na shigo zan yi. Dan ƙaunar Allah da Manzon sa ka rufa min asiri ka maida ni"

Ajiye biron hannun sa yai ya ɗago ido ya dubi Ghazala da kyau. Kallo ɗaya ya ma ta ya san ba ƙaramin rama ta yi ba.

"Na riga na yafe miki Ghazala, yanzu tsakanin ki ne da Allah da kuma Zaytoon da ki ka zalunta kuma ba na tunanin kin roƙi gafarar ta har yanzu"

"Idan ma tsugunnawa ka ke so na yi a gabanta na ba ta haƙuri Wallahi zan yi" Ghazala ta yi saurin katse shi.

"Ka da ki roƙeta dan ni, ki roƙeta da zuciya ɗaya saboda kin ma ta laifi. Ki roƙe ta tsakani da Allah"

"Zan yi, wallahi zan yi"

Shirun da ta ga yayi ne ya sa ta tattaro duk wani ƙwarin gwiwa da ta ke da shi ta ce "Abu Razz ka maida ni kenan?"

"Allah ya baki wani mijin wanda zai zauna da ke yadda ki ke so Ghazalah"

"Ranka shi daÉ—e..."

***

Mommy da Daddy ne su ka je yiwa su Iya sallama saboda gobe jirgin su zai tashi.

Daddy da Muntari ke taɗi sama-sama dan har yanzu Muntarin ya kasa sakewa jiki da shi. Yayinda Mommy ta buge da danna waya dan Iya ta koma ɗaki. Ƙafarta ke damunta shiyasa da su ka gama gaisawa ta wuce ɗaki ta kwanta.

"Hamma ina da magana" Muntari ya faÉ—a yana danna yatsun sa.

"Bismillah, minene?"

"Na so dai sai kun dawo na gaya ma ka amma yaron nan kaman zai yi min kuka jiya wai dole na faÉ—a maka kafin ku tafi"

Daddy ya tattaro dukkan hankalin sa ya bawa Muntari.

"Auwal ne ya ce na nema ma sa auren Humairah a wajen ka"

"Ka ji min wani zance a nan. Mukhtar Humairah ai 'yar ka ce. Ni miye nawa a ciki"

"Hamma..."

"Nkiru kin ji maganar da mu ke?"

Mommy ta girgiza kai

"Wai First son É—in ki ke son Humairah shine Mukhtar ke min maganar. Ki gaya ma sa Humairah dai 'yar sa ce, ni ba abinda zan ce a nan"

Muntari yai shiru saboda wannan matsayi da Hamman na shi ya bashi, bayan duk aika-aikar da ya ma sa.

Kafin su tafi sai da aka tsaida magana akan za ayi biki zuwa sati biyu bayan sallar layya. Inda Daddy ya ce ya barwa Muntari ragaman yin komai dan shi ya fi chanchanta ya aurar da Humairah.

Bayan tafiyar su, Mommy ta kira Auwal tana tsokalar shi akan yai haƙuri ba za ta bashi Humairah ba. 'Yar ta ba za ta auri Barrister ba.

"Mommy kar ki sa jini na ya hau, mi Daddy ya ce Dan Allah?"

Mommy ta yi murmushi ta ce ya cigabanda shirye shirye dan an sa biki roughly nan da wata uku ma su zuwa.

Ta riga ta san da maganar dan lokacin da ya ji hiran Muntari da Iya akan saurayin Humairan da ke son turowa gida shine ya samu Mommy da maganar ita kuma ta ce yai wa Muntatin magana dan shi ne yanzu Uba ga Humairah. Anyi wannan maganar ne tun kafin T J ya dawo.

Washegari kuwa T J da Maryam su ka wuce Makkah dan yin Umara.

***

Tana shigowa falo ta jefa jakarta kan kujera ta kwantar da Alinah da ke bacci sannan ta zaunaa ƙasa ta miƙe ƙafafuwa. Ba kowa a gidan ta sani tunda yanzu Maman Tope ne kaɗai ke mu su aiki dan tuni Galadima ya sallami Atika sanda ta dawo gidan ma ba ta sameta ba. Maman ta tafi ƙauyen su saboda rasuwar da aka mu su.

Ba wai hanata Azumi da likitan yai ba ne ya sa ta damuwa sai dai sakamakon ultrasound da aka ma ta ne ya sa duk jikin ta yai sanyi.

"Insha Allahu za ki haifa mana 'yan biyu lafiya nan da wata bakwai" Likitan ya faɗa yana murmushi. Babban Likita ne da Galadima ya haɗata da shi, ba ta san takamaimai alaƙar su ba amma matsayin ƙani ya ke ga Galadima.

Sake haihuwan 'yan biyu ba shine matsalar ba, matsalarta shine kada ace ta haifi mata. Za ta so haihuwar 'yan biyu mata amma kuma da ta tuna cewa Galadima ba shi da É—a namiji sai ta ji jikin ta yayi sanyi.

"Doctor maza ne ko mata?" Ta tambayi likitan bayan ta gama farkawa daga tunanin da ta ke.

"Mommyn Alinah its too early to tell gaskiya, sai gaba"

Kaman shima ya ankara da abinda ta ke tunani sai ta ji ya ce "na tabbata Yaya ba shi da ra'ayin fifita 'ya'ya maza akan mata. Duk wanda Allah ya bashi zai karɓesu hannu bibbiyu. Ki godewa Allah domin akwai wanda ko mata-maza ne suna so saboda Allah bai ba su ba"

Ta dai sake fiska kam kafin ta bar office É—in sa amma lokacin da ta shiga mota ta sake duba result É—in da ke hannunta sai ta sake shiga damuwa.

Ko da ace dai-dai da wasa Galadima bai taɓa nuna ma ta cewa yana son haihuwan ɗa namiji ba but cikin 'yan kwanakin nan idan ta ga yana yiwa 'yan biyu wasa sai ta ji kaman yana fata a ransa cewa shima Allah ya bashi 'ya'ya maza ne.

Zuwa lokacin da yaran su ka dawo daga makaranta ta riga ta É—auke abin a ranta ta dawo da walwalarta.

Da yamma ita da Raziya su ka shiga kitchen su ka É—aura abincin buÉ—a baki. Allah ya sa ma Raziyan ba ta Azumi da ba abin da za ta iyayi, yarinyar akwai raki.

Ta yi zaton Likita ya gaya mi shi komai shiyasa ta yi shiru da bakinta tana jira ta ji ya taso da maganar amma shiru. Dan da ya dawo daga sallar taraweeh ya sha tea sai ya shiga library É—in sa ya fara aiki.

Ƙarfe shaɗaya da minti shida ya shigo ɗakin sa. Ya shiga banɗaki ya kama ruwa, yai alwala sannan ya fito.

Ba ta yi bacci ba dan tuntuni shi ta ke jira amma kuma yana shigowa ta yi saurin rufe idonta kamar mai bacci.

Jawota jikin sa yai sosai-sosai sannan ya ma ta magana a dai-dai kunnen ta kamar mai raÉ—a.

"Ya jikin na ki ? Mi Likita ya ce"

Kamar ba za ta amsa ba sai dai kuma ta sani wahala kawai za ta bawa kan ta dan ta san ya san ba ta yi bacci ba.

"Alhamdulillah da sauƙi, Likita ya ce na ajiye Azumi na wani lokaci"

"Ai dama na gaya miki ki ajiye amma ki ka yi kunnen ƙashi"

Ta yi murmushi mai ciwo dan ba ta san tana za ta fara ma sa bayanin abinda ke cikinta ba da kuma tsoron da ta ke ji.
Chapter 155 · 0% Book details