← Book details Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 161

Sashe 54

Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fita yai daga É—akin dan shi bai iya dogon magana ba.
Sai da ta ga ya fita ta je ta sa makulli a É—akin.
Box uku ne a cikin ledan da ya ajiye dan haka babban box ɗin ta fara buɗewa wanda ta ga wani Designer gown mai kyau kalar abin cikin ƙwai an shimfiɗa acikin box ɗin, ta ciro shi tana ƙara kallon sa a ido dai tsayin zai ma ta sai dai tana shakkar shigan sa jikin ta.

Ta cire rigan jikinta wanda da ƙyar ya fita. Ta saka kayan da ya kawo abin mamaki kuma ya shigeta sai dai da ke ta saman dama a matse ya ke lokacin da ta zuge zip ɗin sai ya sake matse nonuwanta wanda su ka cika suka yi fam, wannan baya ma buƙatar bra dan shi kaɗai rigan ma yana aikin bra.
Ta tsaya gaban madubi tana kallon kanta yadda rigan ya ma ta kyau sosai. Bayan ta gama jujjuyawa gaban mirror sannan ta koma wajen sauran box ɗin biyu. Ɗaya box ɗin takalmi ne shima mai kyau flat pumps wanda tana tunanin ya siya ne saboda ya ga irinsa ta ke sawa. Ɗaya ƙaramin box ɗin kuma sarƙa da ɗankunne ne ma su kyau sai sheƙi su ke.

Washe gari ƙarfe shaɗaya saura na safe ta gama shiryawa cikin kayan da ya kawo ma ta. Sai dai ba za ta iya fita ba tareda ta rufe kan ta ba. Cikin veils ɗin da ta ke da shi ta nemi wanda zai shiga da kayan ta. Wani ja ta ɗauka ta ɗaura a kanta irin ɗaurin turban ɗin nan, sai ta ɗauki wani red purse wanda ta siya wani fita shopping da ta yi ru. farko-farkon zuwanta.

Lokacin da ta fito suna tsaye a ƙasa suna jiranta, dukkan su sun yi shigan baƙin riga baƙin jeans da baƙin blazer.
Kallo ɗaya Zuhayr ya ma ta ya kauda kan sa. Kafin ta ƙariso su ka yi waje dan haka itama wajen ta bi su inda Driver ke jiran su. Ba ta sha mamaki ba lokacin da ta ga Zuhayr da Ben sun shiga baya. Bayan ya kamata ta shiga dan har lokacin Driver be kulle ba amma sai ta buɗe gidan gaba ta shiga.
Ba wanda yai magana har su ka isa inda za su je. A bakin tamfatsetsen building É—in kamfanin aka tsaya inda kafin ta buÉ—e wani da ke tsaye a wajen ya buÉ—e gidan baya inda Zuhayr ya fara fitowa, itama ganin haka ta buÉ—e ta fito.
Dukkan su uku su ka jera su ka shiga ciki tana gefen Zuhayr shi kuma Ben na gefen sa.

Zaytoonah kam duk abinda ake gudanarwa na ta ido, ta sha gaisuwa kam dan Zuhayr da ƙanwar sa ya ke introducing ɗin ta a abokanan aikin sa. Bayan an gama pleasantries aka zazzauna inda aka fara serving abinci. Table ɗin su su bakwai ne ke zaune akai, ita ɗaya ce mace. Ba abinda ta iya ci a wajen saboda wajen bai ma ta ba a takure ta ke, gashi kuma abincin tsoron ci ta ke yi saboda strictly cuisine ɗin turawa ne, tana tsoron kar ta ci ya ɓata ma ta ciki kamar yadda a gida watarana da karambani ta ci wani girkin Chef Green sai gashi awa ɗaya bayan ci ta ɓarke da gudawa.

Wata sexy Mace ce ta zo ta zauna a kujera É—aya da ya rage ba mutum kuma kujeran opposite da na Zaytoonah ya ke.

"Sorry i'm late for the party guys" ta faÉ—a lokacin da ta zauna.

Kallon Zaytoonah ta yi ta kauda kan ta sannan ta kalli Zuhayr da ke gefen Zaytoonan ta tambayeshi wayece baƙuwar cikin su.

"A Sister" ya faÉ—a a hasale

'Yar dariya ta yi ta ce "ban san cikin 'yan uwan ka na Nigeria akwai ma su kama da doya ba"
Gaba É—aya wajen sai aka kwashe da dariya.
Zuhayr ya watsawa Matar wacce aka kira da Scarlet harara.

"Sorry Zoheer, i just express my mind, she really looked like a Yam" ta faÉ—a tana wani munafukin murmushi.

Tunda su ka fara dariya ta ke kallon su É—aya bayan É—aya har ta tsaya akan Zuhayr wanda bai yi dariya ba amma bai cewa Scarlet komai ba.

Wine cup da ke gaban Mr Morgan wanda ya zauna a gefenta ta ɗauka ta miƙe tsaye ta watsawa Scarlet a fiska ta ce
"Listen to me you old hag. My name is Zaytoonah and i'm not a YAM, but you" ta nunata da yatsa "you are a disgusting racist bitch"
Ta ja kujera ta É—au purse É—in ta ta ce "fuck you all" ta faÉ—a tana É—aga mu su yatsar ta ta tsakiya.

Tafiya ta ke yi da sauri kamar za ta tashi sama, tsanar kan ta tayi na dalilin ma biyo shi wannan Party da ta yi. Ba wai sunan ne kawai ya ba ta haushi ba sai yadda Zuhayr yai shiru bai kareta ba. Kenan shima kallon Doya ya ke ma ta?

Ji ta yi an kama hannunta, ta juyo a fusace sai ta ga Zuhayr ne. Ta yafce hannunta ta juya za ta cigaba da tafiya ya sake riƙe hannun yana faɗin "wait"

"Ka ga ka sake ni, ka sake ni dan cin mutuncin ya isa haka"

"Zaytoon..."

"Doya aka kirani a gaban ka kayi shiru, Doya fa"

"Zayt..."

"Ba sai ka yi bayani ba na san kai ma abinda ka ke ganina da shi kenan. But let me tell you i'm proud of myself, i'm proud of my chubby self"

"Lets go home" ya furta a hankali...

Har su ka iso ba wanda yai magana a gaba ta zauna kamar yadda ta zo sai dai lokaci zuwa lokaci tana É—an goge hawaye da bayan hannun ta.
Mota na tsayawa a ƙofar gidan su ta shige cikin gidan da gudu. Ta faɗa kan gado ta fashe da kuka, kuka sosai ta ke yi. Rabon da ta yi kuka saboda an ma ta maganar jikinta tanaga tun tana SS1.
Ko da auren su ba wai jimawa zai yi ba atleast ya kamata ya defending na ta a wajen nan amma yai shiru yana ji ana ma ta dariya.
Tana cikin kuka ta ji ana ƙwanƙwasa ma ta ƙofa amma sai ta ƙi buɗewa.

"Zaytoon we need to talk"

"Go away" ta faɗa da ɗan ƙarfi. Ya ƙara ƙwanƙwasawa kusan sau uku kafin ya haƙura ya tafi.

Ƙarfe bakwai na yammaci ta fito daga ɗakin ta, ta yi kukan ta yi baccin ta gaji. Ɗan karan yunwa ta ke ji dan tun safe rabonta da abinci, ɗan cookie da ke jakarta na makaranta ta cinye amma ba abinda ya ma ta. Ta fito daga ɗakinta tana tafiya a hankali dan jiri-jiri ma ta ke ji saboda yunwa. Dai-dai ɗakin da ta ke ganin Zuhayr na shiga ta tsaya ganin ƙofar ɗakin a ɗan buɗe. Ɗaki ne da ba ta taɓa shiga ba ba ta ma san ya yake ba, duk da tana fushi da shi bai hanata ɗan leƙawa ba dan ta ga miye a ɗakin ake hanata shiga tuntuni. Ba kaman ma Ben da ko kallon ɗakin ba ya so tayi.
Numfashinta ya kusa ɗaukewa lokacin da ta leƙa kan ta cikin ɗakin ta yi baya da sauri tana dafa ƙirjin ta.
"Zuhayr da Ben" ta furta a fili tana kama baki...
2/11/21, 10:04 PM - ****: 24

Bismillahir Rahmanir Rahim

Nigeria

A ɓangaren Alhaji Muntari tunda aka yi auren Zaytoonah ya kasa zaune ya kasa tsaye. Da ita ya dogara wajen samun Maryam amma komai ya zo ya warware. Cikin ƙanƙanin lokaci ya haukace da neman mafita wa Kan sa. Bayan wani lokaci ya barwa kan sa zaɓin yiwa Maryam asiri dan ta so shi. Ɗantani ya nema don su sake zuwa wajen Malam Yusha'u wanda yai wa T J kurciya. Sai dai Ɗantani ya ce ma sa Malam ya bar ƙasar Chad kuma bai san inda ya koma ba, shima bayan sun je da Alhaji Muntari ya sake zuwa dan a yiwa wani aiki amma bai sameshi ba. Ance ma sa Malam ba ya zaman waje ɗaya ya jima, da ya ɗan kwana biyu sai yai gaba haka ya ke yi.
Muntari ya shiga wani sabon tashin hankali haɗe da danasanin yin asirin tun lokacin da aka yiwa Tijjani. Ko da ya ke ya ɗauka za ta so shi ne idan ta rasa T J to yanzu babu T J ɗin amma ta ƙi amincewa da shi.

Ƙarshe dai gidan jiya ya koma neman Malaman tsubbu da bokaye amma shiru ka ji. Cikin haka ne shagunan sa biyu a Kano su ka ƙone, hakan ya ɗaga ma sa hankali matuƙa dan yayi asarar dukiya dayawa...

Dawowan ta kenan daga school inda ta biya makarantar su Junior ta É—auko shi wanda shima ya fara Pre-Nursery.
Tana shirin buɗe ƙofa Junior na buga food flask ɗin sa a jikin ƙofar ta ji an kira sunan ta "Hajiya Maryam"
Ta juyo a tsorace dan ba ta ji takun mutum ba. Tana juyawa aka sa mata hankerchief aka rufe ma ta baki. Cikin abinda bai fi 30secs ba ta sume mutumin ya janyeta yai wajen da su ka parker Mota da ita. Kafin Maryam ta shigo gidan ta ga motar da aka parker wanda ta yi tunanin ko maƙotan su ne su ka yi baƙi.
Shi kam Junior ganin ana tafiya da Mommyn sa sai ya sa kuka. Ya yi kukan har ya gaji dan haka sai ya fara wasa-wasa a ƙofar gidan duk ya ɓata uniform ɗin sa. A haka Salman ya dawo daga Makaranta ya sameshi ya tambayeshi ina Mommy ya ce bai sani ba.
"Junior ba ita ta kawo ka gida ba?"

"Wani ne ya tafi da Mommy" ya faÉ—a yana sa yatsa a baki.

Salman ya zaro ido yana jawo yaron jikin sa " Junior waye ya tafi da Mommy?, wani kaya ya sa" Junior sai ya tsorata ya sa kuka. Sai a lokacin ma Salman ɗin ya lura da Jakar Mommy da ya faɗi ga key kuma a jikin ƙofa. Ya ɗau jakar ya fara dubawa. Wayanta, ATM, ID card da key ɗin motar ta duk suna ciki. Ya kama salati ya ɗau wayan yana ƙoƙarin kiran numbar Auwal...
Chapter 54 · 0% Book details