Sashe 161
Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read
Kwana biyu su ka yi a Kwala Lampur, Malaysia sannan su ka wuce Las Vegas. Su biyun tol ɗin su su ka tafi, yaran duk sun damƙa su a Zaria. Ahil da Amir na gidan Hajiya Abu sauran kuma na Fada. Hashir da Hadid kuma a wajen Humairah ta bar su, itama Allah ya ba ta haihuwan ɗa namiji Mukhtar suna kiran shi Ayan. Sunan Daddy Auwal yai niyyan sawa amma da ya gayawa Daddy sunan da ya zaɓa sai Daddyn ya ce a fara yiwa Muntari takwara tukunna, hakan kuwa ba ƙaramin daɗi yai wa Iya ba dan Alhamdulillah Allah ya haɗa ma ta kan 'ya'yan ta.
Shi kam Muntari ranan suna da ya ji sunan sai da ya yai hawaye. Jikin sa ya samu sauƙi dan yanzu maimakon wheelchair da ya ke zama da sanda ɗaya ya ke tafiya.
Zaman sa haka ya sa Iya ta yiwa T J magana akan ya nema ma sa Mata, shima maganar dama na ran sa kawai ta rigashi fitar da shi ne. Ita ya bawa wuƙa da nama akan ta nemawa Muntarin Mata, ba a jima ba kuwa ta sama ma sa wata bazawara a Ringim kuma aka ci sa'a da aka yiwa Muntarin magana ya amince. An riga an saka rana, idan su ka dawo da ƙauyen su Mommy za a ɗaura aure.
Maganar Salman da Azma ma ta yi nisa, ba dan Mahaifinta ya ce sai ta ƙare karatu ba kafin ayi bikin da tuni anyi. Kullum Salman cikin lissafi ya ke yanzu haka yana lissafin saura wata takwas ta zama graduate, tunda idan an ƙare hutu ajin ƙarshe za ta shiga.
***
A ranan da su ka sauka a Vegas Muhsinah ta turawa Zaytoonah text akan ta sauka an samu ɗa namiji. Zaytoonah ta kirata ta dinga ma ta tsiya. Bayan ta ajiye wayan ne Galadima da ke gefe ya ce "nima har yanzu ba wani motsi ne" ya ƙare maganar yana ɗaga ma ta gira.
"Ba ni da komai Yallaɓai. Inaga ma na sallama haihuwa yanzu kam"
"Kin bani lasisin na kawo dalleliyar budurwa kenan"
"Ta zo mana. Tunda ragowa za ta samu"
"Ragowa ko?"
"Ragowa mana, ai mun riga mun ci moriyar ganga"
"Ehm ko?"
Zaytoonah ta riƙe ƙugu ta ce "sosai ma kuwa"
Ba ta ankara ba sai ji ta yi yayi sama da ita.
"Wannan nauyi da ki ka ƙara anya ba ku biyu ba ne kuwa?"
"Ka manta mu shabiyu ne"
Dariya yai itama ta saka dariyan yayinda ya sauketa akan gado a hankali. Ya ma ta rumfa ya ce "to bari a cigaba da cin moriyar ragowan"
***
Washegari da safe su ka wuce gidan Farha. Wanda ya san Farha da ba zai taɓa tunanin aure da haihuwa zai nutsar da ita ba. Gaba ɗaya ta zama reaponsible and calm woman. Ba ƙaramin so take yiwa Muhammad Chu ba and baby Ayman yana ganin gata a wajen slay Mom.
Ba su suka baro gidan ba sai yamma. Daren ranan ne kuma Ghazala ta turawa Galadima text akan an saka auren É—an ta, nan da wata biyu. Galadima ya tura ma ta reply da Allah ya sanya Alkhairi.
Farko-farkon haihuwan 'yan biyu ta yi ta damun sa da saƙonnin ban haƙuri da kira akan ya taimaka ya dawo da ita. A ƙoƙarinta na son samun shiga ne ma ta haɗiye girman kan ta ta kira Zaytoonah ta ba ta haƙurin abinda ta ma ta. Zaytoonah ta ce ta yafe.
A ranan kuwa ta turawa Galadima text akan tunda Zaytoonah ta yafe ma ta ai yanzu kam ba sauran wata matsala zai iya dawo da ita. Abin ya bawa Galadima dariya, shi kaɗai ya ci dariyan sa ya ƙoshi dan ya san idan Zaytoonah ta ji yanzu itama za ta hau jirgin kishi.
Bayan ya gama dariyan kuwa ya tura ma ta saƙon da ya hana ta bacci.
*Sorry, kin riga kin yi wasa da damar ki. Ina mi ki addu'ar Allah ya ba ki miji wanda ya fini*
"Kutumar chan, wani mijin zan samu da ya fika? Wani mijin?"
Sai dai babu mai ba ta amsar tambayarta. Ita É—in dai da ta tambaya, still ita za ta ba wa kan ta amsa.
Mummunan ƙarshe da Hajia Ajwa ta yi ya sa ta ma dena tunanin sake biyewa Hajiya Safara'u wajen neman magani. Hajiya Ajwa ta zo ta yi mutuwar ƙasƙanci ne kafin ta mutu jikin ta yayi wani irin kumburi, wasu munanan ƙuraje ma su fitar da ruwan ɗiwa mai wari su ka mamaye jikin ta. Auren 'yarta Mubaraka da Yusuf da ba ta so kuwa anyi kuma kafin ta rasun ma Mubarakar ta haifi ɗa namiji su ka yiwa Galadima mai suna. Shalelen mijin na ta kuwa da ta dinga bin tafarkin sheɗan saboda shi kafin ta mutu yana nan zaune da matan sa biyu lafiya-lafiya dan bayan Uwargidan sa Hajiya Fatima da ya dawo da ita ya auri wata budurwa Shamsiyya 'yar ƙabilar Nupe.
(Babu namijin da ya chanchanci ki bijirewa Allah saboda shi. Babu namijin da ya kai ki watsar da ilimin ki da tauhidin ki saboda shi)
Ghazala kusan shekara ta yi tana bibiyar Galadima akan ya maida ta. Bayan 'yan uwa har da abokan sa na kusa da shi duk ta bi ƙafan su amma all in vain. Ta riga ta rasa shi kenan, har abada.
***
Ruwan sama ake tsalawa kamar da bakin ƙwarya a ƙauyen Okwuohia. Sallama su Mommy su ka zo yi mu su bayan sun sake duba yadda ake ta kan gudanar da Asibiti da kuma Makarantar da aka buɗe. Washegari za su wuce Owerri daga nan su hau jirgi su koma Kaduna then to Zaria.
Zuwa ƙarfe tara na dare ruwan ya fara tsagaita.
Bayan sun gama cin abinci Maryam ta ce wa T J tana da surprise É—in da za ta bashi. Cewa ta yi ya fita daga É—akin za ta kira shi idan ta gama shiryawa.
T J ya koma falo ya zauna yana jiran surprise É—in, cikin É—an mintuna da yai a wajen kafin kiran Maryam ya shigo sai da yai ta tunani kala-kala ciki kuwa harda hasashowa ko dai Maryam na da ciki ne, zuciyar sa ta ce kai ba ciki ba ne. Ciki bayan ta fara bawa shekaru hamsin baya, but you never know. Ba abinda Allah ba zai iya yi ba.
Ya zo yai tunanin ko dai Zaytoonah ce ke da cikin ko kuma Humairah. Ko kuma ma dai ta ji labarin ana son a awarding na shi professorship ne.
A hankali ya buɗe ɗakin kamar mai tsoron wani abu. Ya shiga ciki jiki a sanyaye, sai dai fiskar sa da ke ɗauke da fargaba ne ya koma wasai lokacin da ya ci karo da matar sa da ta yi shiga na 'yan matan ƙabilar Igbo.
"Na ce barin tuna ma ka da yadda komai ya fara, once upon a time in December 1985"
Wayar hannunta ta ajiye bakin gado lokacin da ta kunna waƙar su ta igbo wanda ke ɗauke da beat irin na gargajiya.
T J ya sake baki da hanci da ido duka yana kallon yadda Maryam ta ke bin beat ɗin waƙar a hankali tana rawan Atilogwu.
Ikon Allah kenan, kaman yau ne fa ya ga wata budurwa tana rawa irin wannan tareda wasu 'yan mata. Yadda yarinyar ta ɗauke ma sa hankali a lokacin hakama wannan mata ta ɗauke ma sa hankali yanzu. Shekarun da su ka ja bai sa wani abu cikin son da ya ke ma ta ya ragu ba sai ma ƙaruwa da yai. Bai taɓa sanin cewa ƙaddarar samun mar'atus saliha shi ne ya sa aka tura shi bautar ƙasa jahar Imo ba. Bai taɓa sanin ƙaddarar haɗuwa da uwar 'ya'yan sa ne ya sa ya bi Eze zuwa kallon bikin Mbom-uzo a ƙauyen Okwuohia ba. Bai taɓa sanin cewa taho da Mary-Nkiru zuwa Ringim shine best decision ɗin da yai a duniya ba. But now he knows one thing, Allah ya bashi kyauta mai daraja a duniya, and wannan mata yana fata Allah ya haɗa fuskokin su a Aljannah.
A chan Las Vegas kuwa Galadima ne ya zubawa wani hoto da ya tsinta ido, cikin wani drawer ya ga hoton.
Zaytoonah ne sanye da kayan ballet dance, ta chaka ƙafa ta buɗa hannayen ta kaman mai shirin furkawa sama.
Zaytoonah da ta fito daga wanka ta sameshi yana kallon hoton.
"Wani hoto ne wannan?"
"Ba ki taɓa gaya min ke Ballerina ba ce" ya faɗa yana ɗaga ma ta hoton
"That was then ai, tun ma fa kafin na haifi su Hadid ne"
"To yau Allah ya kamaki, sai a min rawan na gani"
"TabÉ—i! Ka san yaushe rabon na yi rawan ballet kuwa?"
"Ban san wannan ba, all i know shine i want to see you dance for me"
Duk yadda ta so ta zille Galadima bai barta ba, ala dole ta nemi riga da wando ta saka. Cikin soft theme music da ta ke da shi a wayarta ta kunna ta fara yin rawan. With every step da ta ke yi Galadima stood there silently watching her in awe.
Tunanin tsohon mijin ta ne ya zo ma ta, yadda ya dinga supporting ɗin ta all through rayuwan su tare. Ta tuna ranan da ta yi ma sa rawan ballet na ƙarshe yadda ya dinga murmushi cikin jin daɗi. Yanzu ma murmushin Galadima ke yi har da ɗaga ma ta babbar yatsar sa yana ma ta thumbs up. She's so lucky da Allah ya haɗata da maza biyu ma su tsananin son ta, not only that. Su ɗin mazaje ne na ƙwarai.
Hajijiyan da ta fara ji ne ya sa ta yi saurin dakatar da rawan. Galadima yai saurin zuwa ya rungumeta jikin sa.
"I'm proud of you Zaytoon" Galadima ya faÉ—a a hankali.
Hawaye ya fara zubowa a idonta a lokacin da muryan Zuhayr ya doki kunnen ta " I'm proud of you Zaytoon. Daga yanzu ina so ki yi ƙoƙarin zama duk abinda ki ke so a rayuwar ki, with courage and confidence. Ka da ki taɓa bari wai ƙibar ki ya hanaki yin wani abu da ki ke so. You are beautiful just the way you are and i love you just the way you are"
Muryan Galadima ne ya fargar da ita daga tunanin da ta ke yi inda ya ke cewa
"I love you Zaytoon, ina alfahari da kasancewar ki mata ta. Allah Ubangiji ya haɗa fuskokin mu a gidan Aljannah. Ina son kasancewa da ke har ƙarshen rayuwa ta and even beyond. Allah ya ƙara mi ki Albarka Zaytoon"
Zaytoonah ta amsa da Amin zuciyar ta cike da farin ciki. Duk yadda rayuwa ya juya da ita, daga ƙarshe ba abinda za ta ce sai dai Alhamdulillah!!!
*Alhamdulillah. A nan na kawo ƙarshen labarin Chronicles of Zaytoonah*