← Book details Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 161

Sashe 30

Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hajjo ce ta iya cewa " sannu da zuwa ya jiki?"

Maryam ta amsa da sauƙi, da ta zo za ta shiga ɗakinta ne ta ji maganar da T J ya faɗa da kuma amsar da Iya ta bayar.

TJ ya miƙawa Iya Baby Zaytoonah yana faɗin " Iya ga takwarar ki ta iso"

"Allah ya kiyaye 'yar zina ta ci babban suna kaman nawa"

Ya haɗiyi miyau da ƙyar yana kallon yadda iya ta koma gefe dan ma kar ya ɗaura ma ta baby a cinya.

Maryam na shiga É—aki ta zauna a bakin gado ta kifa kai da gwiwa. Kuka ta ke son yi amma kuma ba amfanin yin kukan ta É—ago ido tana sauke ajiyar zuciya daidai T J ya shigo É—auke da baby.

A gefenta ya shimfiÉ—a baby da ke bacci ya ce "Maryam I'm sorry"

"Ka yarda da maganar da ta faÉ—a kenan?"

"Noooo"

"Then maganar ta wuce"

Ya durƙusa gabanta ya kamo hannayenta duka biyu.
If only Iya ba mahafiyar sa ba ce. If only zai iya cewa Iya ta bar gidan su ta fita a rayuwar su.
Tunanin da ya ke yi kenan azuciyar sa. Bai san wani kalma zai faÉ—a ma ta dan ya tausasa ma ta zuciya ba. Dan haka ya cigaba da murza hannunta a hankali...

***

Kwanan su É—aya ya kai Maryam Ringim, zo ka ga murna a wajen Goggo da sauran 'yan uwan T J wanda su ke son Maryam É—in tsakani da Allah. Kowa ya ga baby sai ya ce kamannin Maryam ta É—auko sai kuma yanayin idon T J da ta ke da shi.
Goggo da kan ta ta fara yiwa baby da mai jego wanka.
Ana gobe suna Pendo ta taho daga Dutse da 'ya'yanta biyu Mustafah da Binta.
Da yamma aka yiwa Maryam ƙumshi mai kyau ja da baƙi wanda ya ƙara fito da ita.
Ko da Goggo ta ga ya zo shi ɗaya sai ta tambayeshi miyasa ya baro Iya da Hajjo a Zaria. Bai ɓoye ma ta komai ba ya sanar da ita abinda ya faru gameda sheganta Zaytoonah da Iyan ta yi.

"Ban san ya zan yi ba Goggo. Wai dama dan a samu sulhu tsakaninta da Maryam ya sa na ke son yi mata takwara kuma ta ce indai na sawa Zaytoonah suna Aisha ba ta yafe ba"

Goggo ta yi shiru na ɗan wani lokaci kafin ta ce " ka ci gaba da haƙuri Shehu, duk munin Uwa ba a chanja ta. Tunda ba ta son a ma ta takwara shikenan Allah ya raya mana Zaytoonah. Insha Allahu yadda ta ƙi ta sai yarinyar nan ta zama alkhairi ga dukkan gidan nan. Sai tauraronta ya haskaka ko'ina, kuma Iya sai ta yi dana sanin furucinta"

T J ya amsa da Amin.

Ranan suna kam anyi liyafa na gani na faÉ—a. Ko lokacin sunan Sadiq ba ayi shagalin da aka yi a sunan Zaytoonah ba.

Wasu da su ka ji sunan da yarinya ta ci sai abin ya mu su banbaraƙwai. Ga sunan su na gargajiya da aka saba ji amma an tsallake an tafi wani suna wai Zaytoonah. Wanda su ke da ilimi sosai cikin su kuwa sun yi na'am da wannan suna.

Goggo ta ce sai Maryam ta yi Arba'in kafin ta koma gida, shi dai T J bai so ba ya dai haƙura ne. Ita kuwa Maryam da ma ba ta ɗokin komawa gidan, har yau furucin da Iya ta yi na cinta.

Har Maryam ta yi Arba'in Iya ko Hajjo ba wanda ya zo Ringim. TJ kaÉ—ai ke zirya tsakanin Zaria da Ringim É—in, duk weekend zai zo ya ga Princess É—in sa.

Ana gobe za ta koma Zaria da yamma sai ga Inna Yelwa ta zo wajen Goggo da wani Yaro da ba zai wuce shekara shida ba. Wai ta kawo shi ne yai sallama da Uban sa za a kaishi Almajiranci.

Maryam ta ƙurawa yaron ido, tausayi ya ba ta. Ba ta san ɗan waye ba a gidan amma yana ɗan shigen kamanni da Usman Yayan T J shiyasa ta yi hasashen ko ɗan sa ne.

Goggo ma dai ta yi jajen wannan abu dan gani ta ke yi Auwal yayi ƙaranci. Sai dai ya za ta yi tunda dai ba ta da iko da shi.
Bayan tafiyar Inna Yelwa sai Maryam ta tambayi wacece ita.

"Mahaifiyar Hauwa ce, Hauwa marigayiya matar Manga"

"Goggo ba dai Hauwa ta rasu ba?" Ta tambaya cike da tsantsan mamaki tana ƙoƙarin tuno Hauwan, wacce ke cike da tsananin kunya. Lokacin da T J ya dawo daga bautar ƙasa Usman Manga ya auro Hauwa, shekaranta shabiyu a lokacin.
Maryam da Pendo su ka je ganin Amaryar da aka kawo daga ƙauye, bayan sun dawo ta dinga yiwa T J complain wai taya zai bari Yayan sa ya auri yarinya ƙarama haka. T J ya ce ba shi da ikon hana ɗan uwansa abin da yai niyya. A wajen su hakan ba komai ba ne. Ta dinga tausayin yarinyar kasancewa Uwargidan Usman na da masifa. Tana ɗaya daga cikin ma su aibanta Maryam lokacin da ta zo gidan.

"Hauwa ta rasu ai ya kwana biyu, lokacin kina Makaranta ne shiyasa ba ki sani ba"

Maryam ta ce Allah ya jiƙanta Goggo ta amsa da Amin.

Washegari da T J ya zo ta ma sa maganar Auwal da za akai Almajiranci da rashin dacewar hakan. Tunda mahaifiyar sa ta rasu Kakarsa ta tafi da shi ƙauye ta cigaba da renon sa. Ko girma bai yi ba wai za a kaishi wani gari Almajiranci.

Ganin Maryam ta damu da yaron ne ya sa yai wa Yayan sa magana akan yana so a bashi Auwal. Usman ya ce ai Auwal ɗan sa ne ba komai. Tareda shi su ka je ƙauye su ka karɓo Auwal ɗin, sun samu ma ana jiran isowan Malamin da zai tafi da shi ne, da rabon dai Auwal ba zai yi Almajiranci ba shiyasa su ka riga Malam zuwa.

Maryam ta ji daɗi da T J ya damƙa ma ta Amanar Auwal har yana tsokalarta wai ta zama uwar biyu, ga Baby Zayt ga kuma Auwal. Haka su ka tarkata su ka tafi da shi Zaria.
As expected sai da Iya ta yi bore akan ba ta yarda Auwal ya zauna a wajen Maryam ba. Haƙuri ya ba wa Maryam sannan ya damƙawa Hajjo amanar Auwal amma a gaban Iya ta ce ba za ta iya riƙe shi ba itama fama ta ke da kanta wai ciki gareta.
Ƙarshe dai ɗakin Iya aka ajiyeshi.

Zaman na su dai gashi nan gashi nan ne.
Maryam na kaffa-kaffa da iya amma duk da haka kullum sai ta zageta ga habaici. Zaytoonah kuwa ko sau ɗaya ba ta taɓa ɗaukan ta ba.
Da farko Iya ƙin cin girkin Maryam ta ke yi, sai ranan da Hajjo ta yi biris ta ce indai Iya ba za ta ci girkin Maryam ba to sai dai in ta shiga kitchen ta dafawa kan ta amma ba za ta ma ta wani girki ba. Iya ta ture abinci gefe ta hau fushi, da yunwa ta isheta ta ce Auwal ya je ya ɗauko ma ta abincin. Daga nan labari ya sha banban dan sai dai ta mutu amma Maryam ta fi Hajjo iya girki nesa ba kusa ba. Ko ita Iyan ba za ta iya sarrafa abinci kaman yadda Maryam ke yi ba.
Daga nan kuma Iya ta samu tsirface tsirface duk dan ta muzgunawa Maryam. Ta ce abu kaza za ta ci a'a abu kaza bai ma ta ba wani abu daban da babu shi a gidan za ta ci. A haka dai Maryam ke daurewa tana binta sau da ƙafa. Daga baya kuwa sai Iya ta kira Maryam ɗin ta ce da ranan girkinta da ba nata ba ita za ta dinga yi har sai Hajjo ta sauka, ana maganan wata biyar a gaba.
Maryam ta ce ta ji. Ganin anyi sati tana girki T J bai yi magana ba ya sa ta san da yardar shi kenan Iya ta saka wannan doka.

Ranan tana ba wa Zaytoonah nono sai ga Auwal ya shigo da gudu, dawowar sa kenan daga makaranta. Kusan dai Auwal kwana kawai ya ke yi a É—akin Iya amma Maryam ita ce É—awainiyar sa wanka da wankin sa duk ita ce.

"Mommy wai gashi inji Baban Lucas ya ce na baki" ya faɗa yana miƙa ma ta wani ƙaton envelop.

Ta amshi envelop É—in tana tambayar sa a ina su ka haÉ—u ya ce ya zo zai shiga gida ne ya kirashi ya bashi wai ya kai wa Mommyn sa.

Sai da ta gama feeding Zaytoonah ta kwantar da ita sannan ta buÉ—e envelop É—in ta fara dubawa nan ta ke fiskarta ya washe da murmushi.

"Mommy goya min ita" muryan Auwal ya fargar da ita

"Ba yanzu ba, je ka cire uniform É—inka ka sa kaya sai ka zo na zuba ma abinci"

Ya ce to sannan ya fita da gudu...

Da dare ta nunawa T J takardan samun aiki da aka kawo ma ta, wanda aikin ma ta nema ne ba tareda sanin T J ba.

"Maryam yaushe wannan?"

"You are too busy Barkindo, ka dena damuwa da halin da na ke ciki balle ka san mi na ke buƙata"

"Maryam ki min uzuri dan Allah. Aikin ginin da na ke yi duk shi ya ke É—auke mun hankali"

"Zan koma Kaduna da zama, zan dinga zuwa mu ku a weekend. Idan kana so zan iya tafiya da Auwal"

Yai sokoko yana kallonta har ta gama bayani.

"Maryam ina za ki tafi min da 'ya? Maryam dududu nawa Princess ta ke za ki tafi da ita wani gari aiki. Besides aikin kotu fa, a ina za ki dinga ajiyeta?"

"I knew it, i knew it. Saboda matar ka na da tsohon ciki kar Nanny ta tafi ta bar ta da wahala"

"Maryam..."

"Tijjani please. Ba sai ka yi wani ƙarin bayani ba na fahimci komai"
Chapter 30 · 0% Book details