Sashe 12
Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Alhaji Isa, Baffah da Baffah Umar da Baffah Jibrillah su suka je amsa kiran Sarki. Ƙara ce dai Muntari ya kawo, nan Sarki ya ji ta bakin Alhaji Isa gameda duk abunda ya ke faruwa.
Sarki ya fara yiwa Muntari nasiha akan rashin kunya da yai wa iyayen sa amma Muntari ya ɓare baki ya ce indai a fada ma ba za a masa adalci ba zai kai kotu. Wani dogari ne ya doki bakinsa da dorina sai da gefen bakinsa ya fashe ya sake zuba ma sa a baya. Sarki ya ce ya tsaya haka.
Alhaji Isa ya ce idan dai Sarki ya yarda yana so a É—aura auren Maryam da Tijjani a gaban Muntari saboda a rufe maganar.
Fadawa su ka yi na'am da maganar.
Nan ta ke Alhaji ya ba da sadaki aka É—aura auren *Tijjani Abubakar Modibbo Djibo* da kuma Amaryarsa *Maryam Nkiru Uzodinma*
Wanda Maimartaba Sarkin Ringim ya zama Waliyyin Amarya shi kuma Alhaji Isa Wakilin Ango.
Har aka gama É—aura auren Muntari bai bar hawaye ba. Shikenan ya rasa Maryam, yarinyar da tunda ya fara ganinta kullum sai yayi mafarkinta, shikenan ya rasa masoyiyar sa.
***
Duk bayanin da ake ma ta ba wani ganewa ta ke ba, maganar farko ita ta mamaye ilahirin jikinta wai an ɗaura aurenta da Teejay. Wani farinciki ta ke ji wanda ke ratsa duk wani kafa na jikinta, rabonta da irin farinciki haka tun iyayenta na raye. Auren ya ma ta banbaraƙwai tunda ita ko T J ba sa wajen aka ɗaura auren, sai kuma ta tuna irin auren su kenan ba kaman wanda ta sani da ake yi a church ko kotu ba...
Kwanakin da su ka shige ana nutsar da ita gameda addini tareda gyarata da Goggo ta farayi a matsayinta na Amarya. Wasu abubuwan kam tun tana mamakin su har ta dena. Kowa yayi na'am da auren banda Iya wacce ke ganin kamar wata ƙungurman Arniya Bamagujiya aka aurawa Tijjani. Ba ma wannan ba tun da aka yi wannan rikicin da Muntari ya tafi ba a ji ɗuriyar sa ba, ko sallama bai wa Iya ba ya tafi. Baffa kuwa ya ce kar wanda ya ƙara tada zancen abun da ya faru, idan Muntari yayi hankali zai dawo ya nemi gafaran iyayensa bisa wannan tonon asiri da ya mu su.
Sati ɗaya ake tunanin T J ya rage ya dawo gida kamar yadda ya sabayi amma bai zo a satin ba. Sai su ka ɗauka sai ƙarshen wata zai zo. Rashin zuwan sa ya sa Amarya Maryam ta ƙara jin wani matsanancin kewar sa daga ƙarshe kuma ta fara fushi da shi.
Labarin musuluntar Nkiru ya sa su Okafor da ma church members ɗin su suka shiga alhini, sun je har gida suna neman ta ba su dama su zauna da ita a tattauna amma ta ƙi ba su dama dole haka su ka tafi, gashi ana hutu balle su je su ritsata a makaranta. Yadda dai su ke tsoro tun farko sai da hakan ya faru. Pastor dai gaba ɗaya ya ɗaurawa Okafor laifi dan gani ya ke da bai yi yunƙurin yiwa Nkiru fyaɗe ba da ba za ta guje shi ba ƙarshe har ta zo ta dena zuwa church...
Ranan ashirin da tara ga watan october 1986 T J ya dawo gida, tunda ya fara masters program na shi wannan ne karo na farko da yai wata É—aya ba tareda ya zo gida ba. Hakan ya faru kuwa saboda wani gasan Maths na sakandare schools da ake yi a garin Kaduna wanda aka sa shi cikin Alkalai hakan ya sa gaba É—aya bai samu ya zo ba.
As usual ɗakinsa ya shiga ya ajiye jaka sannan ya wuce ɗakin Goggo, mutum biyu ya gani suna sallah a ɗakin bai tsaya gane waye ba ne saboda babu wuta fitila aka kunna a ɗakin, kai tsaye ya wuce ɗakin Yadikko wacce itama ke sallar Isha'i dan haka ya wuce ɗakin Iya. Ɗan amsa gaisuwar na sa da ta ke yi da yau bai samu ba, ya fi sau goma yana gaisheta ta yi banza da shi ƙarshe ta ce ya bar ma ta ɗaki. Ya fice daga ɗakin sumu-sumu, yana tunanin me kuma ya faru.
Ya yi sallah a hanya dan haka ya koma ɗaki ya cire kayan sa ya saka jallabiya ya fito ƙofar gida. A nan 'yan uwansa da su ka dawo daga masallaci ke ma sa barka da dawowa wasu kuma su na tsokalar sa Ango- Ango. Gaba ɗaya sai ya rikice, ba dai Baffah ya ma sa auren ba, ai shekara ɗayan da ya nema ba ta cika ba. Ganin Baffan na dawowa ne ya sa shi zare jiki ya je wajen sa yana gaisheshi. Tare su ka shiga gida inda su ka yi masauki a ɗakin Baffan.
Zuciyar sa harbawa ta ke da sauri-sauri saboda abunda ya ji a ƙofar gida.
Baffah na sane da yadda Tijjani ya ke a zabure amma ya dake yai ta jansa da hira sai daga baya ya fara ma sa bayani.
"Shehu kafin zuwan ka akwai wasu abubuwa da su ka faru, ba na so na yi tone-tone saboda ba abinda hakan zai haifar sai fitina. Na san duk hukuncin da na yanke kai mai karɓan shi hannu bibbiyu ne shiyasa ni da iyayen ka muka yanke wannan hukunci. An riga an gyara mu ku ɗakin da za ku zauna, ba a dai gama saka ma ta kaya a ciki ba amma a hankali za a sa komai tunda abune da ya zo a gaggauce. Sai ka yi haƙuri da ɗaurin auren da hidiman duk anyi babu kai"
Da Baffah zai kalli T J da kyau da zai ga yadda jikinsa ke rawa, ga gumi na tsatstsafo ma sa duk da kuwa akwai sanyi a garin.
"Maryam 'ya ta ce, ina fata za ka riƙemin ita Amana duk da na san kana ƙoƙarin hakan tunma kafin a aura ma ka ita. Allah ya baku zaman lafiya ya baku zuri'a ɗayyiba. Zan yiwa Goggon ka magana a buɗe mu ku ɗakin dan babu amfanin wani jinkiri tunda kai ba mai zama ba ne"
"Insha Allahu Baffah" abinda T J ya iya faɗa kenan ya miƙe ya fita baya ma gani da kyau. Yana zuwa ɗakinsa ya kwanta yijif sai ga hawaye a idanun sa. Duk wani ɗokin ganin Nkiru da ya ke yi yanzu danasanin dawowa gida ma yake yi. Ta ina zai fara rayuwa da wata Maryam? Ta ina zai fara zaman aure da wata wanda ko sanin ita wacece bai yi ba, he has always challenged irin auren da ake mu su, auren haɗin gida duk da ma yanzu ana ɗan bari a saba kaɗan kafin ayi auren amma shi duk cikin cousins ɗinsa babu wacce zai iya cewa tana burgeshi balle har yai tunanin zaman aure da ita. Wani zazzaɓi ne ya rufe shi lokaci guda...
Tunda Baffah ya sanar da Goggo cewa a tura Maryam ɗakin mijinta ba ya son wani hayaniya ta sa Maryam ta je ta yi wanka. Da ta dawo cikin sababbin kayan da aka ɗinka ma ta ta zaɓa ma ta ɗaya ta saka aka feshe ta da turare, aka yafa mata gyale aka rufe fiskarta Goggo, Yadikko, Pendo da Inna Zulai su ka raka Maryam ɗakin ta ana tafiya Inna Zulai da Yadikko na ta guɗa.
ÆŠakin dama a gyare ya ke, addu'a kawai su ka ma ta su ka fito dan ba sa jin turanci balle su ma ta nasiha.
Shiru-shiru Tijjani zai zo bai zo ba har ƙarfe goma. Tun Maryam na gyangyaɗi har ta kwanta sosai akan gado ta fara bacci garin da sanyi saboda iskar damina da ke kaɗawa hadari ne ma ya taso a garin.
T J na kwance a ɗakin yana rawan ɗari ƙaninsa wanda su ke 'ya'yan Baffanu ya shigo ɗakin. Shi ma farkon shekaran da za a shiga za a ma sa aure. Tsakanin sa da T J shekara ɗaya ne.
Ganin yadda T J ya ke rawan ɗari hakan ya sa shi ƙarasowa ɗakin da gudu.
"Lafiya, mi ya faru?"
T J ya ce "ka ce Yusha'u ya zo ya min allura Dan Allah"
"Hamma ko dai tsoron haÉ—uwa da Amarya ne? Ni na É—auka ko ciwo ka ke yi aka ce an É—aura ma ka aure da Maryam a take za ka warke"
"Dan Allah ka je, idan ba za ka je ba ko su Ƙasimu ka aike su"
"Ba Yusha'un da za a kira, ga kaza nan na siyo maka kaje Amarya ta maka maganin zazzaɓi"
"Ba za ka gane bane Suleman, Dan Allah ko magani ne ka siyo min"
"Ikon Allah. Na É—auka za a raba dare ana soyayya ashe duk shirme ne. Gaskiya abin Babba ne. Barin je na kira Yusha'un"
Har zai fita sai T J ya ce " wai dan Allah Suleman wace Maryam É—in aka aura min?"
Sai lokacin Suleman ya gane abinda ke damun T J ashe bai san wa aka aura ma sa ba.
Ya dawo gefensa yana cewa kafin ya gaya ma sa sai ya bashi tukwici.
T J yai tsaki yana dafa kan sa da ke wani irin sarawa.
"Hamma kar ka kashe kan ka fa. BoÉ—É—iyonka aka aura ma ka"
T J ya É—aga rinannun idanun sa ya kalleshi ya ce " ba na son shirme"
"Aradun Allah BoÉ—É—iyo ce, ai musulunta ta yi shine su Baffah su ka aura ma ka ita"
Kafin ya ƙare maganar tuni T J ya miƙe tsaye. Suleman ya sa dariya
"Dan Allah ban da wasa kar zuciyata ta buga, ka faÉ—amin gaskiya" yana magana yana jin wani jiri-jiri.
"Na rantse da Allah Hamma"
Tijjani ya sa kai zai fita Suleman ya riƙeshi ya ce "ga gudummawa" ya miƙa ma sa ledar gasashshiyar kaza.
A hankali ya buɗe ƙofar ɗakin yana tantamar maganar da Suleman ya faɗa. Ankawo wuta dan haka ɗakin tarr ya ke da haske. A hankali ya ƙarisa bakin gadon ya ƙurawa yarinyar da ke kwance kan gadon ido bai san lokacin da dariya ya ƙubuce ma sa ba yanayi yana hawaye. Ya ranƙwafo ya kwanta gefenta ya sa hannu ya shafa kumatunta.
"Inkiru" ya kira a hankali yana cigaba da shafa fiskarta.