← Book details Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 123 OF 161

Sashe 123

Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Mommy anya zan iya zuwa inda ya ke after all he did to you"

"Ba na son shirme, he's a father to you Adaeze. Abinda ya min bai shafe ki ba, ki je ku gaisa Salman na chan"

Bayan ta gama ƙunƙunin dai dole ta tashi ta fita zuwa gidan.

Zaytoonah kam kallon farko tsorata ta yi da Uncle Muntari wanda ganin ta ya sa shi waƙe haƙora. A iya sanin da ta yi mi shi za a iya cewa yanzu ya koma kashi ɗaya cikin huɗu. Kallo ɗaya tsoho mai shekaru tamanin zuwa casa'in za ka bashi. Ko Alhaji Iliyasu da ya bawa shekarun casa'in baya bai yi wannan tsufa da lalacewar ba.

"Banda kuka Gimbiya, zo na ji É—umin ki"

Zaytoonah ta ƙarisa wajen da ya ke zaune bayan ta share hawayen da ya sauko ma ta. Lokacin da ya rungumeta ta ƙara tabbatarwa cewa Uncle Muntatrin dai ƙashi da rai ne.

"Allah ya bayyana mana Shehu, ya kawo mana shi gida lafiya kamar yadda ya fidda ka Muntari" Iya ke wannan maganar tana ƙara sabon kuka.

Sosai maganar ta daki Muntari tunowa da yai cewa shine silar rugujewar farin cikin waÉ—annan yaran. ÆŠaya bayan É—aya ya fara kallon yaran É—an uwan na sa, ga su nan mata biyu maza biyu Masha Allah.

Ta ina zai fara ba da wannan mummunan labari, ta ina zai fara bayyana mu su cewa kishi, ƙiyayya da son zuciya ya sa shi jefa Mahaifin su duniya.

Dole ne ya faÉ—a mu su gaskiya amma ba yanzu ba, ba yanzu da su ke marmarin ganin sa ba. Idan har ya faÉ—i komai ba makawa tsanar sa za su ji. Har Mahaifiyar sa da kukan daÉ—in ganin sa sai ta tsine ma sa.
Ya sauke nannauyan ajiyar zuciya tareda maida kallon sa ga Salman wanda ba inda ya baro Yayan na sa. May be because he's feeling guilty sai ya ke gani kamar Tijjani ke zaune a wajen.

Ƙuruciyar su ya tuno irin kyakykyawan zuciya ta Tijjani, kyakykyawar zuciyar da a yau shi kaɗai ya ke kwaɗayi. Ina ma yana da ita, da duk wannan abubuwa ba su faru ba. Sai dai ƙaddara ta riga fata...

Auwal da Iya su suka bayyanawa Muntari abinda Alhaji Rabi'u yai da dukiyar sa. Bai kawo komai ba sai sakayya, sakayyar abinda yai ne ke bibiyar sa shiyasa dukiyar ta sa ma ta faɗa hannun banza. Amma fa ba zai bari ya shige haka ba, taɓa mutuncin mahaifiyar sa da iyalin sa ya fi ma sa komai ciwo fiye da dukiyar da ya kwashe.

Ranan bai iya baccin kirki ba saboda tunanin ta inda zai fara tunkaran lamarin.

Kwana uku yai yana juya lamarin kafin ya tsaida matsaya guda.
Da yamma ya wuce gidan Mommy dan ya sanar da ita ƙudurin sa.

Bayan sun gaisa ya tambayeta yaushe Hanne ta ce za ta turo ma sa 'yar sa.

"Gobe Jummu'ah za su zo weekend zan sa Salman ya je ya É—auko ta. Baby ta zama 'yan ma ta sai ka fara tanadin kuÉ—in É—aki"

Murmushi mai ciwo yai kafin ya ce "Baby ai karatu za ta yi kamar mai sunan ta"

"Na ji Salman ya ce kin fara degree na uku, ba kya gajiya da karatu ne"

"Ka san neman ilimi ga Malami baya ƙarewa"

"Hakane. Da Hamma na nan da yanzu ya zama Profess..." maganar ta tsaya tunowa da yai cewa shine silar katse komai.

Shiru ne ya biyo bayan haka kowa da irin abinda ya ke yawo a zuciyar sa.

Chan Muntari ya daure ya fito da abinda ya kawo shi wajen ta. Bayan ya gama bayanin sa Mommy shiru ta yi na kusan minti biyu tana kallon ƙarfin hali irin na Muntari, kafin ta ce.

"Adaeze ba za ta zama Lawyer ɗin ka ba Muntari. Kwanciyar hankalin ta shine burina a koda yaushe, ko da mijin ta zai ba ta izinin ta jagorance ka ni ba zan taɓa amincewa ba. Idan ƙara za ka shigar zan haɗaka da ƙwararren Lawyer amma Zaytoonah ba za ta karɓi wannan case ɗin ba"

"Humairah ta gaya min ita ta jagoranci case É—in ki da Kawun ki har aka samu nasara"

"Muntari! Zaytoonah ba za ta karɓi case ɗin ka ba" Mommy ta faɗa da karfi, wanda ya sa Muntari tsorata.

***

Zaune ta ke a madaidaicin office É—in ta da ke cikin katafaren shagon ta. Bayanan Galadima gameda matsalar Zaytoonah su ke ma ta yawo a kwanya. Wannan dama ce a gareta hakan ya sa ta janyo wayarta ta shiga bincike akan ma su matsalar Zaytoonah.

"Ben" ta maimaita tunowa da ta yi shine sunan da Zaytoonah ke maimaitawa ranan da ciwon ta ya tashi. Ben shine dodon Zaytoonah ita kuma shine maganin matsalarta. Wani munafukin Murmushi ta yi lokacin da kwakwalwarta ya hango ma ta Mahaukaciya Zaytoonah...

Wata guda da Muntari yai a gida har ya ɗan fara kyan gani. Zuwa lokacin kuma ya tunkari Alhaji Rabi'u da maganar maido ma sa dukiyar sa ko kuma ya shigar da shi ƙara amma Alhaji Rabi'u yai biris, ce ma sa yai ya je duk inda zai je babu mai sauraron sa.

Barrister Auwal Usman Abubakar shi zai jagorance shi. Ba wai dan ya so ba sai dan Iya da Baffansa sun sa baki. Mommy dai ce ma sa ta yi yayi taimako dan Allah ba dan an tursasa shi ba. Kamar zai fasa sai kuma ya chanja ra'ayi ya amince akan zai karɓi case ɗin.

Alhaji Rabi'u bai tsammanci da gaske Muntari ya ke ba sai da Lawyan sa ya kawo ma sa letter daga kotu. Murmushin mugunta yai ya cillar da Letter.
Ranan shaɗaya ga wata za a fara sauraron ƙara amma kafin ranan zai rufe maganar....

Tashin hankali goma da ishirin Zaytoonah ta shiga lokacin da mummunan labari ya riske ta. Ɓarayi ne su ka shiga gidan su Iya su ka halbi Auwal da Uncle Muntari.

Justice baya gari, a waya ta sanar da shi abinda ya faru tareda neman izinin tafiya Zaria. Bai hanata zuwa ba sai dai ya ce bai yarda ta tuƙa kan ta ba sai dai Dreba ya kaita.

Lokacin da su ka isa Zaria ana kiran sallar Maghrib. Kai tsaye Asibiti aka wuce da ita dan dukka 'yan gidan na su a wajen su ke.

Ta samu ganin Auwal dan shi halbi ɗaya aka ma sa a kafaɗa, amma Uncle Muntari halbi uku aka ma sa ɗaya a gefen ƙirji biyu a ciki. Har zuwa lokacin da Zaytoonah ta iso ma ba a gama ma sa aiki ba.

Haka dukkan su suka zauna jugum suna sauraron fitowar Likitoci. Ba su fito ba kuwa sai ƙarfe shaɗaya saura na dare.
Sun tabbatar mu su da cewa Muntari na cikin haɗari. Harsashi ɗaya ya shiga Kidney ɗin sa automatically kidney ɗin ya mutu sun cire shi, ɗayan kuma da ya saura ba shi da lafiya dan shan giya da yai a baya ya riga ya ɓata Kidney ɗin.
A taƙaice Muntari na buƙatar kidney transplant ASAP.

"Innalillahi wa Inna Ilaihi Raji'oun" Mommy ta furta tareda dafe ƙirji.

Lokacin da ta fito daga Office É—in Likita Iya ce ta fara taran ta " ya rasu ko?"

Mommy ta yi saurin girgiza kai.

"Za mu iya ganin sa"

"Likita ya ce sai gobe"

"Allah ka tashi kafaÉ—an bawan ka Muntari" Iya ta faÉ—a tana rafka tagumi.

Kwana uku Muntari na kwance sai a rana ta huɗu ya farfaɗo. Kidney ɗin sa guda ɗaya da me aiki idan ba a samu wani ba zuwa gaba kaɗan itama mutuwa za ta yi. Maganar nan da wata biyu zuwa uku aka ƙiyasta ma sa.

Mommy ta saka a fara binciken donor ko za a samu a siya ma sa amma ba labari har yanzu. Cikin 'yan uwa duk wanda aka tunkara da maganar kidney sai ka ji yana faÉ—in Jarrabawa ce ta same shi a barshi ya fuskanci jarrabawar Ubangiji.

Duk da Auwal na halin samun kulawa shi ma sai da ya ce a duba na sa idan yai dai-dai sai a cire na sa ɗaya a bawa Muntari ɗaya. Sai dai Likitoci sun ƙi aminta da hakan dan atleast idan ba tsautsayi ba yana buƙatar wata shida kafin a fara maganar ma za a ma sa aiki irin cire kidney. Ba tareda Mommy ta sani ba Salman ya je aka gwada na sa sai dai aka ci sa'a bai zo dai-dai da na Muntari ba.

Maganar ƙara tuni anyi watsi da shi, dan yanzu ko taɗin ma ba a yi. Alhaji Rabi'u ko leƙo Asibitin bai yi ba balle ya zo ya duba halin da Muntari ke ciki...

Kwana biyu Zaytoonah ta yi a Zaria ta koma Abuja saboda zazzaɓi da 'yan biyu ke yi. Sai da ta yi kwana takwas kafin da su ka zo weekend ta sake leƙa su. Auwal dai jikin da sauƙi sosai dan ana maganar za a sallameshi nan kusa.

Mommy ce ta shigo É—akin da aka kwantar da Muntari. Iya ce kaÉ—ai a É—akin na sa tana zaune akan sallaya tana addu'a.

"Iya idan kin ba da dama zan sa a fita da Muntari ƙasar waje idan har ba a samu Kidney ba nan da sati ɗaya"

"To to ai ba matsala. Indai zai samu lafiya a chan Bismillah"

Hawaye ne su ka taru a idon Muntari.

"Maryam" ya kira sunan Mommy yayinda hawaye ya fara zubo ma sa. Bayan duk laifuffukan da ya aikata bai chanchanci alkhairi daga Maryam ba.

Ƙila ma ba zai yi nisan kwana ba gara kawai ya fito ya bayyana tarin laifuffukan sa ya kuma nemi yafiyar wanda ya zalin ta.

"Dan Allah ki tara min yaran Hamma"

Daga ita har Iyan ido su ka zuba ma sa

"Ina son neman gafaran su ko zan samu Allah ya gafarta min"

"Muntari wani irin magana ne wannan"

"Dan Allah Maryam ki kira su"...

Text ta tura mi shi saboda ya ce wajen Mai Martaba zai je.

Reply ɗin sa da ta gani ne ya sa ta dariya. Sosai Galadima ke ba ta mamaki idan yai wani abin kamar ƙaramin yaro.

*Dan Allah ki dawo da wuri, yau gaskiya ina buƙatar tanadi. A gaishe da mai jiki*
Chapter 123 · 0% Book details