Sashe 41
Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
TJ ya durƙusa a ƙasa yana dafe ƙirjinsa saboda zafi da ya ke ji hakan ya sa Maryam ta dakatar da maganganunta.
Ta goge hawayen ta tace"You know what, ba amfanin maganar yanzu saboda ba zai mai da hannun agogo baya ba. But know this Tijjani, i will never forgive your mother and brother"
Tana faÉ—in haka ta fice da sauri, seeing T J a wannan hali ya fara sa wa zuciyarta rauni.
A inda ya ke tsugunne ya fara ƙoƙarin kiran sunan ta amma zuciyar sa ta ma sa ƙunci.
"Mary..." sunan bai gama fita ba ya fara aman jini.
Iya tunda Maryam ta fara bayani jikinta ke ɓari, ganin Tijjani na furzar da jini ya sa ta ƙwalla ƙara ta yi kan sa tana kiran sunan sa "Shehu, Shehu, Tijjani"...
Tana fita daga gidan kai tsaye gidan ta ta wuce, a bakin ƙofa ta haɗu da Auwal zai fita.
Ganinta tana kuka ya sa shi birkicewa "Mommy lafiya? Miya faru?"
"Ka je gidan Muntari ka duba Daddyn ku"
"Mommy..."
"Ka je da sauri Auwal"
Bai ƙara magana ba ya fita da gudu.
Yadda idon T J yai ja jijiyoyinsa su ka firfito ta tsorata amma dole ta rabu da shi saboda ta riga ta sawa ranta daga yau babu ita babu T J. Kayanta ta shiga haÉ—awa da sauri tun kafin Auwal ko sauran yaran su dawo.
Muhimman takardunta ta É—auka sai cards É—inta sannan ta É—auki kaya randomly ta sa a jaka ta fice da sauri. Motarta ta shiga ta bata wuta ba tareda ta san ina takamaimai za ta je ba...
Taimakon gaggawa aka fara yiwa TJ saboda yadda aka kawoshi wurjajan. Allah ne ma ya taimakeshi bai kamu da stroke ba. Ikon Allah ne ya cececi rayuwar sa amma da tuni heart attack É—in ya kashe shi.
Iya na kuka Auwal na yi itama Hanne na hawaye, har sai lokacin da likita ya fito ya ce mu su su godewa Allah he survived, sun stabilizing condition ɗin sa. Amma su cigaba da yi ma sa addu'a, ba a bar su sun shiga wajen sa ba sun dai leƙa shi inda su ka ga yadda aka sa ma sa nasal canula saboda ya dinga taimaka ma sa da numfashin sa.
Wayan Hanne Auwal ya karɓa ya kira numbar Mommy sai dai har ta gama ringing ba a ɗauka ba. Sau biyar yana kira ba a ɗauka dan haka ya rubuta ma ta text ya tura...
***
A ranan da aka kai T J Asibiti a ranan ya isa ƙasar Chad. Wannan karan wanda ya jagorance shi ya nuna ma sa indai buƙatar sa bai biya ba to duk kuɗin da ya karɓa a wajen sa zai maida ma sa da shi. Ya ce Malamin idan ba zai iya aiki ba yana faɗawa mutum shi aikin sa ba cuta ba cutar wa.
A kwana na uku su ka isa gidan Malamin wanda tundaga Ƙofar gida Muntari yai mamakin kyaun gidan. Gidan bai yi kama da irin gidajen bokaye ko malaman tsibbu da ya taɓa zuwa ba.
"Anya ÆŠantani nan ne gidan?"
ÆŠantani yai dariya ya ce "hanyar cin abinci na fa kenan Alhaji Muntari. Mutane sun fi goma na kawo wannan guri"
Ɗantani dillalin Bokaye ne da Malaman Tsibbu, a yadda ya ke ya san address ɗin Bokaye a ciki da wajen Nigeria sun fi talatin. Aikin sa shine kai mutane ko haɗa mutane da Bokaye musamman ma manyan ma su kuɗi, 'yan siyasa ko 'yan kasuwa ko ma manyan mata ma su son hana kishiya zaman lafiya. Kafin ku je za ka biya shi idan buƙatar ka ta biya za ka balancing kuɗin ka. Bai faye bin mutane har wajen ba, yawanci kwatance ya ke yi ko yanzu da waya ta fara yawaita a hannun mutane sai ya ba da lambar wayar Boka.
Alhaji Muntari ya ce indai ba ƙafarsa ƙafar Ɗantani ba ba zai je ba tunda anjima ana cin kuɗin sa a banza buƙatar sa ba ta biya. Shi kuwa Ɗantani kuɗin da Muntarin yai alƙawarin ba shi ne ya sa dole ya biyo shi su ka je ƙasar Chad ɗin.
Shi kan sa ya san wajen wannan ne gangaran wanda indai buƙatar Muntari ba ta biya ba to ya haƙura kawai ba inda za a iya yi ma sa aikin.
Sai da su ka fi awa ɗaya suna jira kafin aka mu su iso zuwa ciki wajen Malam ɗin. Ɗakine mai faɗi wanda babu floor sai yashi da aka zuba a ƙasa. A tsakiyar ɗakin Mutumin ke zaune a kan fatan Damisa. Idan ka duba bangon ɗakin an cikeshi da rubutun Larabci wanda yawanci ayoyin ƙur'ani ne da aka jirkice su. Mutumin dai gashi nan baƙi ne wuluk kuma yana sanye da baƙin kaya babban riga da baƙin rawani, yana riƙe da baƙin carbi irin mai dubu ba ɗayan nan yana ja.
Hannu yai wa ÆŠantani akan ya tafi dan haka Muntari ne kawai ya zauna a gaban sa yana zazzare ido saboda yadda kan sa ke sarawa tunda su ka shiga É—akin.
A yashin da ke gaban sa Malamin yai wasu rubutu yanayi yana girgiza kai.
Ya ɗago ya kalli Muntari wanda tunda ya zauna ya kasa magana. Ji yai kamar an riƙe bakin ga wani irin sanyi-sanyi zafi-zafi da ya ke ratsa shi tun shigowar sa.
"Mutu ka raba" Malamin ya furta yana kallon Muntari.
Ganin jajayen idon Malamin ya sake birkitashi, baki na rawa ya ce "ban gane ba?"
"Ka zo domin kana son auren matar Yayan ka, auren su kuma mutu ka raba ne"
Muntari zai yi magana Malamin ya dakatar da shi ya ce "duk inda za ka je, duk inda za ka shiga aka gaya ma ka saɓanin wannan to ƙarya ce aka ma ka za a ci kuɗin ka ne ka rubuta ka ajiye. Gaskiyar ɗaya ce Madamar Yayan ka na raye, Maryam ba ta da wani miji sai shi"
Muntari ya zaro ido waje na farko saboda mamakin kalaman Malamin na biyu kuma yadda aka yi ya san sunan Maryam ba tareda ya faÉ—a ma sa ba. Abinda ma ya kawoshi bai faÉ—a ba aka sanar da shi. Lallai kam Malamin mai gaskiya ne.
"To yanzu shikenan ba yadda za ayi ka raba auren?"
Malamin ya kwashe da dariya marar daɗin ji sannan ya ce "idan kashe shi za ka yi inaga ba sai na ma ka komai ba domin akwai hanyoyin kashe mutum cikin sauƙi wanda na san ka sani. Amma Yayan ka na raye ka ce za ka aureta wannan idan ya faru ka zo zan yi ma ka sujjjada saboda na yi ma ka ƙarya"
Zuciyar Muntari ta cunkushe duk da tsanar da ya ke wa Tijjani baya tunanin zai iya kashe shi. Wani tunani ne.ya faÉ—o ma sa yai saurin cewa.
"Idan baya nan aka neme shi aka rasa ka ga dole ta haƙura da auren ta auri wani. Na san zuwa shekara ɗaya biyu za ta gaji da jira ta nemi yin wani auren ni kuma sai na aureta a lokacin ka ga dai ba a kashe shi ba kuma bai saketa ba a kotu aka raba auren ni kuma sai na aureta"
Malamin ya zuba ma sa ido yana kallon tsantsan hassada da ke tattare da Muntari, son da ya ke yiwa Maryam bai kai ya kasa haƙura da ita iya shekarun nan ba. Yana da yaƙinin da Maryam wani ta aura ba Yayan sa ba da tuni ya haƙura da ita amma Hassada ya ke da ɗanuwan sa. Hassada ce ta cika ma sa zuciya shiyasa ya kasa haƙura da Maryam saboda hassadar Yayan sa ya samu macen da ya ke so.
Shima ɗin Hassada ce ta kawo shi abinda ya ke yi yau. Mahaifin sa babban Malamin zaure ne a ƙasar Senegal, yana da tarin Ilimi ga ɗalibai da su ke zuwa ɗaukan karatu a wajen sa ba adadi. Ana zuwa daga ƙasashe daban-daban ɗaukan Ilimi wajen sa. Mahaifin shi shi ɗaya ya haifa namiji dan sai da ya haifi 'ya'ya mata goma sha uku kafin aka haifeshi. Sunan sa Yusha'u kuma sun taso da ɗan ƙanin Baban sa Lukman, kan su kusan ɗaya.
Lukman maraya ne iyayen sa duka biyu sun rasu. Tun suna yara ya ke hassada da Lukman saboda hazaƙarsa da ƙoƙarinsa. Shi da ya ke ɗan malam da wuya ya ke riƙe karatu amma Lukman Allah ya ma sa kaifin basira. Dayawa mutane kan ɗauka Lukman ne ɗan Malam na asali ba Yusha'u ba.
A shekarun sa ishirin da biyu ya rabu da gida ya rabu da iyayen sa saboda hassadar da ya ke wa Lukman. Malam ya tsufa yana yawan jinya hakan ya sa ya fara tura Lukman jan mutane sallah tareda bawa mutane karatu da kuma fatawa. Lukman yayi karatun da shi kan sa Malam ya san ya samu Magaji idan baya nan. Shi Yusha'u ko ƙur'ani bai sauke ba balle ya iya fassara balle balle balle.
Wajen wani malamin da ya je ne aka ba shi laƙanin karatu da ta farin jini saboda yana son kere Lukman ashe laƙanin Aljanu da Shaiɗanu ne. Ya je yai ta kiran sunayen Aljanu har ya kusa zaucewa kafin daga baya su ka saita shi a harkan tsubbu. Shekaru Arba'in kenan yana wannan harka shi kuwa Lukman yai shekaru talatin da takwas yana ibada yana koyar da mutane har Allah ya ɗau ran sa. Duk hassadar sa gareshi sai da abinda Allah ya rubuta ma sa ya tabbata. Har yau idan aka kira sunan ɗan uwan sa Lukman sai dai ka ji ana Allah ya ma sa rahama saboda kyakyawar rayuwa da yai.
"Indai Hassada ce za ta kai ka ga halaka" abinda Malam Yusha'u ya faÉ—a kenan a zuciyar sa...
*Dam Dam Dam....free pages are ending soon domin an kusa fara shiga ainihin labarin*
*Don samun daman karanta cigaban labarin za a biya 300 ta account number kamar haka:*
3099546325
Firstbank
Azizat Hamza
*ko kuma katin MTN na 300 zuwa ga wannan numbar 08137311900*
Za'a tura Shaidar biya zuwa ga wannan numbar still 08137311900 ko kuma ma dai domin ƙarin bayani za a iya tuntuɓar numban, preferably chat ko text.
*Allah ya ba da ikon biya amin*
2/11/21, 10:04 PM - ****: 21