← Book details Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 112 OF 161

Sashe 112

Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da ta idar da sallah da ƙyar ta iya ƙarisa azkar ɗin ta na safiya, ko tilawa ba ta yi ba kamar yadda ta saba ta koma kan gado ta kwanta.

Ƙarfe bakwai da minti Arba'in wayarta ya fara ringing. Kamar ba za ta ɗauka ba amma ganin an kuma kira a karo na biyu ya sa ta ɗauka. Salman ne ke kira ta swiping kiran tareda faɗin "wato ɗan baccin safen ma ba za ka bar ni na yi ba"

"Sorry Sis kiran ne its urgent shiyasa"

"Lafiya dai ko?"

"Na kira Galadima numbar sa a kashe shiyasa na kira ki"

Tashi zaune ta yi tana faÉ—in "Salman mi ya ke faruwa? Mommy fa?"

"Zaytoonah sai dai haƙuri amma mun yi babban rashi yau da Asuba"

Jin maganar mutuwa ya sa bugun ƙirjin ta ya ƙaru ta ce " wa ya rasu?"

"Hajiya Saudah, Kakar marigayi"

"Innalillahi wa Inna Ilaihi Raji'oun. Ba ta samu lafiya ba. Ina ce ko wata bai yi ba da dawowar ta Asibiti a Egypt"

"Mutuwa ai ko da jinya ko ba jinya za a yi ta Adaeze"

"Hakane" ta faÉ—a tareda goge hawayen da ya silalo ma ta tunowa da ta yi da Zuhayr wanda a ko da yaushe ta ke jin mutuwar sa É—anya a tattare da ita.

"Ki faɗawa Galadima za a yi Jana'iza ƙarfe tara na safe"

Ko amsawa ba ta yi ba ta kashe wayar saboda yadda jikin ta yai sanyi. Tana tuno haɗuwar su na ƙarshe da ita kusan kwana shida da su ka wuce da ta zo yiwa Mommy Barka har da ba da haƙuri akan ba za ta samu zuwa biki Ringim ba saboda ciwon ƙafa da ta ke fama da shi yanzu ba ta iya juran zaman mota balle tafiya nan da chan yana ba ta wahala.
Ta tuno gudunmawar biki da aka yi daga gidan su Zuhayr aka kawo mu su wanda ta san Hajiyar ce ta jagoranci abin. Wasu kyaututtukan ma ba ta buÉ—e su ba ma saboda ba lokaci.

Kowa daka gani a duniya lokacin sa zai ci. Ga shi dai Hajiya Nenne ita ce Babba kuma ta fi Hajiya Saudah tsufa amma kuma Hajiya Saudar ta riga ta barin duniya.

Ta buɗe gallery ɗin wayarta ta shiga folder da ta saving da suna FOREVER YOU ta dinga scrolling hotunan Zuhayr da ke cikin folder ɗin har ta kai kan hoton da ta ke son gani. Hoto ne da Zuhayr yai da Hajiya Saudah lokacin da su ka zo Nigeria a bikin Muhsina. Ranan wata Jummu'ah ne da yai shigar manya kaya ya zo gaishe da Hajiyar ta ke ce ma sa kayan sun ma sa kyau ya dinga saka irin su. Selfie su ka yi kafin daga baya Zaytoonah ta karɓi wayan Zuhayr ɗin ta mu su hoto su biyu.

Buɗe ƙofar da aka yi ne ya dawo da ita daga dogon tunanin da ta tafi.

"Subhanallahi" ya faɗa yana ƙarasowa wajen ta da sauri saboda hawayen da ya gani a idon ta.

"Zaytoon mi ya faru?" yai tambayar yana dafa kafaÉ—ar ta. Ta yi saurin exiting gallery É—in ta dan kar ya ga hoton. Yana É—aya daga cikin abinda Mommy ta ma ta nasiha akai.

*"Duk da Zuhayr ba ya raye hakan ba zai hana Mijin ki yai kishin sa ba, musamman idan har za ki dinga nuna ma sa kin damu da tsohon mijin ki fiye da shi. Zaman ku da Zuhayr ya ƙare Adaeze. Galadima shi ne mijin ki yanzu, ki riƙe shi hannu bibbiyu"*

Ta yi saurin goge hawayen ta ta ce " Hajiya Saudah Kakar su Hashir ne ta rasu yau da safe"

"Allah ya jiƙan ta da Rahama"

Ta amsa ma sa da Amin kafin ta gaya ma sa saƙon Salman.

"Bari mu karya sai mu wuce gidan"

Ta É—ago ta kalli idon sa kafin ta sauke tana tunanin mi ya ke nufi da kalmar "mu", dan ba ta kawo zai bar ta ta je gidan rasuwan ba.

Bayan fitan sa daga É—akin ta shiga banÉ—aki ta yi wanka sannan ta fito ta shirya. Kiran Mommy ta yi dan ta ma ta ta'aziyya amma ba a É—auki wayan ba. Ta kira Muhsina wanda itama bai jima ba da ta ji batun rasuwan, daga jin muryan ta ka san itama ta yi kuka.

Bayan ta gama wayan ne ta ga text ɗin Justice akan ta sauko ƙasa su karya lokaci ya tafi. Ɗazu da tana wanka ya shigo ɗakin ya ga ba ta nan.

Har ta É—auko mayafi ta saka akan kayan da ta sa sai ta maida shi ta nemo hijab wanda ya shiga da kayan jikin ta ta saka ta fita.
Lokacin da ta iso wajen dining É—in yana kan waya dan haka ta ja kujera ta zauna.
Bayan ya ajiye wayar ne ta gaishe shi ya amsa yana ƙara yi ma ta ta'aziyya.

Da ke ba ta da appetite ba ta wani iya cin abincin kirki ba.
Bayan sun fito daga gidan ne ya ke jaddada ma ta kamar yadda ya riga ya tsara za su koma Abuja a yau to shi kaÉ—ai zai tafi. Ya ba ta dama ta zauna a nan har zuwa sati, idan ya zo weekend sai su tafi tare.
Ya haÉ—a da cewa ya ba ta dama ta je gidan rasuwa har na kwana uku amma bai yarda ta yi dare ko ta kwana a wajen ba.
Ita dai jin sa kawai ta ke yi amma tunanin ta ya tafi wani wajen.

Lokacin da Dreba ya sauke su a compound ɗin gidan tuni an cika saboda ƙarfe tara saura minti goma ana jira a fito da gawar ne kawai ai ma ta sallah.
Zaytoonah ta fito daga motar kan ta a ƙasa har ta wuce ta ƙofar baya ta shige gidan yayin da Justice ya wuce wajen dandazon jama'ar da aka taru.

Kai tsaye falon marigayiyar ta shiga inda a nan ta samu Hajiya Nenne da ma ƙannen Hajiya Saudar. Mommy ma ashe ta zo tana wajen.

Hajiya Nenne na riƙe da Tasbaha tana ja lokaci zuwa lokaci tana sauke ajiyar zuciya. Zaytoonah ta je gaban ta ta zauna tana riƙe hannun ta yayinda sabbin hawaye su ka fara silalo ma ta.

"Lah Zaytoonah ki bar kuka fa. Ai Saudatu ta yi rabo , ta tsira, yanzu kan sai dai mu. Matar nan shekaru hamsin da tara muna zaune zaman lafiya da ita, zama na amana. Duk haihuwan 'ya'yana ita ke zuwa mu su jego ba ta taɓa ha'intar su ba. Da nata da nawa 'ya'yan duk ɗaya su ke a wajen ta. Ga fara'a, ga sadaka ga kyauta ga ibada, Kai Allah ka jiƙan Saudah" ta ƙarisa maganar tana fyace majina da jiƙaƙƙen handkerchief da ke hannun ta. Gaba ɗaya mutanen wajen sai jikin su yai sanyi...

Bayan an kai Hajiya Saudah gidan ta na gaskiya Zaytoonah ta zauna tareda su Hajiya Nenne ana karɓan gaisuwa. Da su ka samu daman magana da Mommy ne ta ke ce ma ta da ƙarfe shabiyun rana yayi ta je gida dan ta kula da mijin ta. Zaytoonah ta ce ai shi ya ce ta zauna a nan har yamma.

Zaytoonah ba ta bar gidan rasuwa ba har sai ƙarfe huɗu da rabi na yamma. Da ke tare su ka fito da Mommy sai da ta fara biyawa gidan su kafin Salman ya maido ta gida a motar Mommyn. Yaran ta ma ba sa nan dan tunda su ka je gidan rasuwan tareda Salman su ka maƙalewa Alhaji Tsoho su ka cewa Salman ba za su dawo ba.

A falo ta tadda Justice wanda ke ƙoƙarin komawa Abuja, ya fito da jakar laptop ɗin sa ne Sabi'u ya karɓa ya fita ma sa da shi.

"Har za ka wuce?" Ta faÉ—a a sanyaye.

"Ko za ki shirya mu tafi tare ne" yai maganar yana murmushi

Ta yi saurin girgiza kai.

"Zan wuce" yai maganar tareda ƙarisowa gaban ta.
Sai da ya dafa kafaÉ—an ta duka biyu kafin ya manna ma ta kiss a goshi ya ce "ki kula min da kan ki"
Kasa É—ago ido ta yi ta kalle shi. A hankali kuma ta furta "Allah ya tsare hanya"
Ya amsa da Amin.
Ta raka shi har bakin mota ya shiga sannan Dreba ya wuce da shi...

***

Ba ta san mi za ta dafawa Justice ba dan ba sanin abubuwan da ya ke so ta yi ba. Tun da safe ya kirata ya sanar ma ta yau zai taho, bayan sallar Jummu'ah da su ka taso ma sai da ya kira ta ya ce sun kamo hanya. Tun lokacin ta ke ta saƙawa da warwara kan mi za ta dafa ma sa. Atleast dai ko ba komai ya kamata ta ma sa tarba mai kyau.
Tun da ta zo ma su aiki ke girki, da ke ba wai ma ta samu nitsuwa ba ne ko gwada girkin ba ta yi ba.

"Sannu da aiki Baba"

"Hajiya barka da yammaci. Ya jikin?"

"Da sauƙi"

"Miyar zogale za a yi ne?" Zaytoonah ta tambaya ganin matar na gyaran zogale.

Murmushi ta yi ta ce "ai Yallaɓai yana son kwaɗon zogale sosai, na ce barin yi ya fara da shi kafin ya ci abinci"

Zaytoonah ta zauna ta tayata gyara zogalen tana kallon yadda ta ke sarrafa shi. Ba abu ne da ta taɓa yi ba dan haka ba za ta gwada yin karambani ba kar a zo a samu matsala. Duk yadda dai ta ke yi tana gani tana ɗaukan darasi.

Lokacin da ta ce tuwon shinkafa miyar egusi za a yi nan Zaytoonah ta amshi girkin dan wannan kam idan ba ta yi ba sai Allah ya tambayeta.
Bayan sun gama haÉ—a komai su ka kai abincin dinning su ka jera...

Ƙarfe shida saura Justice ya shigo gidan kai tsaye sashen sa ya shige bayan ya leƙa ɗakin Zaytoonah ya ga wayam.
Chapter 112 · 0% Book details