← Book details Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 161

Sashe 42

Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bismillahir Rahmanir Rahim

Lokacin da ta fito daga Arrivals hango wata ma ta tayi tsaye ta É—aga wani takarda wanda aka rubuta *Welcome Mrs Zainab Tijjani Abubakar*
Har za ta ƙarisa wajen matar sai kuma ta fasa dan sunan ta ba Zainab ba ne, duk da zuciyarta ya ba ta ita matar ta zo ɗauka, tunda an gaya ma ta da ta sauka akwai wanda zai zo ya ɗauketa zuwa gida. Ta tsaya gefe tana tura baki.

Chan Matar ta hango Zaytoonah tunda dama ta ga hoton ta dan haka ta fara É—aga ma ta hannu tana kiran ta Zainab Zainab. Zaytoonah ta ji sarai amma ta share tunda sunan ta ba Zainab ba ne, ta ma kauda kai daga kallon wajen da Matar ta ke.

"Ba ke ce Zainab Tijjani ba?" Matar ta tambaya bayan ta ƙariso gaban ta.

Zaytoonah ta ce "ke ma kin faÉ—a ai"

"Sorry ba ke ce wannan ba" ta yi maganar tana nuna ma ta screen É—in wayarta.

Ta kalli hoton ta ce "kamar ba"

Matar ta yi murmushi ta ce "afuwan Amaryar mu, Hajiya ce ta ce min sunan ki Zainab"

"Zaytoonah Tijjani Abubakar" ta faÉ—a with pride

Matar ta miƙa ma ta hannu ta ce "Muhsina Aliyu Ilyas, cousin ɗin mijin ki"

Musabaha su ka yi su na murmushi. Duk da Matar ta girmeta amman alamu sun nuna ba ta da girman kai dan a ƙalla za ta kai shekara ishirin da biyu zuwa da uku...

Muhsina ke driving É—in su tana yi tana yiwa Zaytoonah labarin gidan su da kuma Zuhayr. Zaytoonah kam na ta kunne, dan Muhsina akwai labari ba ta ma bari ka sa baki, daga ta kamo nan sai ta sake ta kama wani labarin daban.
A wani ƙaton gida su ka tsaya inda Muhsina ta ce ma ta sun iso gida.
Tare su ka shiga cikin gidan Muhsina na riƙe da hannun ta.
Sama su ka haura inda Muhsina ta shigar da ita É—akin ta.

"Hajiya ta ce a sa ki a first room to amma na ga tunda kwana biyu za ki yi gara ki zauna da ni ayi family bonding. Ko ba haka ba?"

Zaytoonah ta yi murmushi.

"Yanzu zan bar ki ki shiga bathroom ki yi wanka ki shirya sai ki sauko ki ci abinci. Then we'll talk"

Lokacin da ta fito daga wanka an shigo ma ta da akwatin ta dan haka ciki ta ɗau kaya ta saka. Lokacin da ta ke rufe akwatin Muhsina ta shigo ta ja ta su ka sauko ƙasa. Kai tsaye wajen dining su ka je wanda an jera abinci kala-kala a kai. Kowa da kan sa yai serving abincin su ka zauna su na ci.

"Hajiya za ta iya dawowa nan da 1 hour haka, Firdaus ƙila sai dare ki gan ta, Abba ya je Japan"
Sai da ta kurɓi juice kafin ta cigaba "Saifullah yana Stanford babban Yayan mu Ishaƙ kuma yana Abuja shi da iyalin sa"

Zaytoonah ta ce "OK"

Haka dai su ka gama cin abincin ana hira kaman sun san juna da jimawa.
Da yamma ta fito ta gaida Hajiya Maimunah wanda yanayin yadda ta amsa ma ta ya sa ta gane matar ba ta son ta.
Da dare su ka haÉ—u su huÉ—u a dinning za su ci abinci.
Firdausi sai kallon Zaytoonah ta ke tana dariya ƙasa-ƙasa. Tun da ta dawo ta leƙa ɗakin Muhsina ta ga Zaytoonah ta koma ɗaki tana dariya. Ashe ma tafi yadda su ka gan ta a hoto ƙiba.

Zaytoonah na lura da ita amma ta yi shiru kar ace daga zuwa ta fara faÉ—a.

"Ikon Allah! Ko ina Zuhayr zai kai wannan buhun oho?"

"Inda Abba ya kai Hajiya" ta faÉ—a tana kallon Firdausin.

"I beg your pardon?" Hajiya Maimunah ta faÉ—a.

"Neman inda za a kaini ta ke yi shine na ce wajen da Abba ya kai ki nan Zuhayr zai kai ni. Idan tana son ƙarin bayani ki fayyace ma ta dalla-dalla dan na san kin gane mi na ke nufi"

"Hajiya ki ji min wannan fat girl É—in fa..."

Fork É—in da ke hannun Zaytoonah ta datsa akan plate É—in da Firdausi ke cin abinci ta ce "kar ki sake kirana Fat girl, Zaytoonah aka yanka min"

Ba Firdausin ba har Hajiyar sai da ta tsorata.
Firdausi ta tashi ta bar wajen bayan ta ja dogon tsaki.

Hajiya kuwa ta yi ƙarfin halin cewa " Zainab ki ke ko waye. Ki kiyaye reni a gidan nan dan Muhsina da Firdausi ba sa'annin ki ba ne"

Zaytoonah ta ce "ki ma ta faÉ—a ta iya bakin ta".

Da za su kwanta Muhsina ta ce wa Zaytoonah ta yi haƙuri abinda Firdausi ta ce ma ta a wajen cin abinci. Wai kishi ta ke yi tunda ta jima tana son Zuhayr amma ba ta samu kan sa ba. Zaytoonah ta ce chan ta matse ma ta.

Kwana biyun da ta yi bayan nan Muhsina kaÉ—ai ke shiga harkarta. Firdausi kam dama tun rana magana ba ta kuma haÉ—a su ba. Ita kuwa Hajiya tsakanin su gaisuwa.
Da wayar Muhsina ta kira Mommy ta sanar da ita ta isa gidan Uncle ɗin Zuhayr saura ta wuce Las Vegas gidan Zuhayr ranan Monday. Mommy ta kuma yi ma ta nasiha sosai akan zaman haƙuri da kuma yawan addu'a, sun gaisa da ƙannen ta kafin ta kashe wayar.

Muhsina ce ta kai ta airport inda ta shiga jirgin da zai kai ta Carson city babban birnin jahar Nevada. Muhsina ta ce Zuhayr zai zo ya ɗauketa a airport ko kuma idan bai samu dama ba zai iya tura Driver, akan haka su ka rabu da Muhsina wanda ta ji daɗin zama da ita sosai. Very simple lady, ba ta da girman kai ko kaɗan. Amma ƙanwarta Firdausi kam sai hamdala.

Wani bature ne da ya kira sunan sa da Benedict ya zo ya tareta a airport. Tana tunanin mota za su hau sai ta ga ya jagoranceta zuwa inda su ka shiga private Helicopter da aka rubuta Z M I a jiki wanda ya tashi da su zuwa garin Las Vegas.

A gaban wani ƙaton mansion su ka sauka. Ita kan har su ka iso jikinta rawa ya ke yi, tsoronta kar fa kasheta za aje ayi. Dan tunanin da ta yi shine Zuhayr Mafia Boss ne. Ga uwa uba wannan Ben ɗin fiskarsa a murtuke duk tambayoyin da ta ma sa kafin su shiga helicopter ɗin cewa yai za ta san komai idan su ka isa gida.

Addu'a ta ke a ranta har su ka shiga gidan inda su ka ci karo da wani katafaren falo. Ta ja ta tsaya ganin Ben na haurawa sama. Sai da yai nisa a hawa stairs ɗin ya juyo ya ga har lokacin tana ƙasa. Ya ma ta alamar ta hauro amma ta maƙe kafaɗa. Dan haka dole ya sauko ya dawo wajenta.
"ÆŠakin ki zan nuna miki" ya faÉ—a da American accent É—in shi.

"Ni dai ka kiramin Zuhayr"

Ya É—an kalleta briefly kafin ya ce " baya nan sai gobe zai dawo, ki biyoni"

Ta yi jihadi ta bi bayan sa. Wani ɗaki ya buɗe ma ta ya ce ɗakinta kenan kuma wai bayan ɗakin bai yadda ta shiga wani ɗaki a saman ba amma za ta iya shiga ko'ina a ƙasa. Ya haɗa da cewa akwai cook ɗin su a gidan za ta iya kiran sa ta ba shi order na abinda za ta ci ko kuma ta sauko ta je ta gaya ma sa da kan ta. Ta gyaɗa ma sa kai sannan ta yi Bismillah ta shiga ɗakin. Ɗakine ƙato dan za ta iya cewa ya girmi falon gidan su. Ba wani tarkace a ciki da ya wuce makeken gado, closet, da dressing mirror sai kuma wata ƙofa da ta gani da ta ke tunanin banɗaki ne.

"Allah gani gareka, anya zan iya zama a nan? karfa Zuhayr ya sa a kasheni ya kira gida ya ce na mutu" ta yi saurin kawar da zancen ta hanyar buɗe banɗaki ta shiga, bayan ta gama ƙarewa banɗakin kallo kafin ta tsaya ta yi wanka.

Muhsina ta gaya ma ta lokutan sallah dan haka ta san ta missing sallolin Magariba, Isha, Asuba da kuma Azahar, dan haka tana sa kaya sallah ta yi duk da ba ta da tabbacin inda Alkibla É—in garin ya ke, ta dai bi instint É—in ta ne sai ta shimfiÉ—a sallayar da ta zo da shi daga gida ta hau rama sallolin da ake binta.

Bayan ta gama ta sauko ƙasa dan yunwa ta ke ji rabon ta da abinci mai kyau tun kafin ta bar gidan su Muhsina. A airport ɗin Carson City ta sayi soft drink da donut guda uku ta ci shikenan kuma.
Bayan ta sauko ta fara bin falon da kallo, tsarin falon ya mata kyau sosai. Wani ƙaton hoto ta tsaya kallo wanda ta ga wani yaro akan doki, yaron ba zai wuce shekara goma ba, gefensa wata baturiya tana dariya ɗaya gefen kuma da ka gani ka san ba bature ba ne saboda baƙin fata ne, sai dai ba baƙi sosai ba. Ɗaya hoton kuma waɗancan mata da mijin ne tsaye macen tana ɗauke da jaririn yaro a hannunta. A hoto na gaba ne ta ƙurawa ido, Zuhayr ne dan ta gane shi da hoton sa da aka nuna ma ta, sai dai a wannan hoton bai kai wancan hoton da ta gani girma ba dan ba zai wuce 21yrs ba haka. Shima hoton akan doki ya ɗauka.

Alamun mutum ta ji a bayanta dan haka ta yi saurin juyowa. Su ka yi ido huÉ—u da Ben wanda idon sa ya rikiÉ—a ya koma ja.

"Mi ki ke buƙata?" Ya tambaya da kakkausan murya.

"Ka ce zan iya shiga ko'ina a ƙasa shine na zo zan duba Cook ɗin dan yunwa na ke ji"

Da hannun yai ma ta nuni zuwa hanyar kitchen.
Tana barin wajen Ben ya É—auke hoton Zuhayr da ta ke gani ya haura sama da shi.

Ƙaton kitchen ne wanda za ka ɗauka kitchen ɗin wani babban restaurant ɗin ne. Chef ɗin da ta gani wani tsoho ne yana girki a kitchen ɗin, dan aƙalla zai yi shekara sittin haka.
Chapter 42 · 0% Book details