← Book details Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 142 OF 161

Sashe 142

Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da ta roƙi Salman akan kar ya gayawa Mommy cewa za ta sai gida kafin ta kashe wayar.

Har dare Galadima bai kirata ba, dama tuntuni ya dena yawan kiranta da ya ke yi. Ita da kan ta ta je ta ɗauko 'yan biyu ta kawo su gidan. Sai da ta gama iƙirarin cewa ba za ta bari abinda ya faru ya dameta ba amma tana hawa gado za ta kwanta ta fashe da kuka. Ta dawo ne da niyyar su cigaba da rayuwa ta jin daɗi tunda ta samu lafiya. Amma kash! Abun ba haka ya ke ba cikin ƙanƙanin lokaci komai ya zo ya kwaɓe tsakaninta da mutumin da ta ɗaukeshi farin cikin ta.

Washegari tun da safe ta fara kiraye-kirayen waya zuwa ƙarfe huɗu na yamma an sama ma ta wani gida da ƙyar. Tunda aka turo ma ta hoton gidan da abubuwan da ya ƙunsa ta ce ya ma ta. Ko ciniki ba a yi ba ta biya kuɗin da aka faɗa lokaci guda. A ranan ta so komawa gidan amma hakan bai yiwu ba sai washegari, har lokacin ba ta ji daga wajen Galadima ba...

A ɓangaren Ghazala kuwa washegarin ranan da su ka raka Zaytoonah ta kira Hajia Abu ta sanar ma ta wai Galadima ya raba mu su gida ita da Zaytoonah amma ta ƙi komawa gidan da ya siya ma ta wai gidan ya ma ta kaɗan. Ta turawa Hajia Abu hoton ainihin gidan da Galadima ya siya.

"Kin san Allah gani ta ke ita millionaire ce ta fi ƙarfin zama a irin wannan gidan. Kin ji maganganun banzan da ta yi ta faɗawa Abu Razz kuwa. Har da cewa ita ba Miskiniya ba ce shine Miskini, wai za ta siya gidan da ya taka nashi dan ta fi ƙarfin zama a ƙaramin gida. Ni dana ga cewa ma abin zai zama faɗa sai na ce zan koma sabon gidan ita ta zauna a wannan amma ta ƙi fir. Wai dama tana managing ne da wanda mu ke ciki. Wallahi kuka ne kawai Abu Razz bai yi ba amma ransa ya ɓaci sosai. Ni tsorona ma kar abin ya sa ma sa hawan jini kin san ya damu da ita sosai"

Tunda ta ke maganar Hajia Abu hankalinta ya tashi. Wacece Zaytoonah da za ta ci mutuncin Galadima haka. Wallahi ba ta isa ba kuwa, ko mi ta ke taƙama da shi sai ta nuna ma ta banbancin Aya da Tsakuwa.

"Kin san tsohon mijinta mai kuÉ—i ne ga uwarta ma ta samu kuÉ—i a sama kwanakin baya..."

"Kar ki damu Ghazalatu. Dama tun da ta haifi mace na ke tunanin ko dai kawai na haÉ—a Galadima da Mubaraka ne. Kwanan nan ta gama degree É—in ta a South Africa"

"Wace Mubaraka?" Ghazala ta faÉ—a a ruÉ—e.

" 'yar gidan Turaki"

Waya ga an kawo kuka gidan mutuwa. Ita da ke son rabuwa da Zaytoonah za a ma ta maganar haɗa Galadima da wata matar. Ba wai ta san Mubaraka ba sosai, amma ta san ita ce ɗiyar Turakin Zazzau ta farko tareda matar sa wata Bafullatanar Cameroon. Mahaifiyar Mubaraka Hajia Ajwa, Ghazala ta ma ta farin sani tas. Mata biyu Turaki ke da shi kafin ya aurota amma duka sai da ta ɗaga su a gidan. Ko shekara ba ta yi a gidan ba ya saki matar sa ta biyu, ita kuma uwargidan sai da su ka shekara uku kafin ya saketa. Kafin ya saketan ma sai da ta sha jinya. Bayan ya saketa kuwa da ta koma gida cikin ƙanƙanin lokaci ta warke sosai.

Hajia Abu za ta haÉ—a auren Galadima da 'yar Hajia Ajwa. Inaaaa ba zai yiwu ba gara ta san abin yi...

***

Zaytoonah na kwance a kan gado Hajia Abu ta kira ta. Kamar ba za ta ɗauka ba sai kuma ta ɗauka ɗin dan ta ji wace tsiyar za ta faɗa ma ta. Tunda ta haihu har yau matar nan ba ta kira ta ma ta barka ba. Ƙannen Galadima da matan yayunsa da ƙannen sa duk yawanci sun kirata sun ma ta barka. Wasu ma da su ka samu zuwa Abuja sai da su ka zo har gida su ka gaisheta amma wannan Sarauniyar Girman kan...

Gidan da aka kai Zaytoonah daban, gidan da aka nunawa Hajia Abu daban shiyasa maganar su ta tafi a bauɗe. Yayinda Hajia Abu ke surfa masifa akan taƙamar Zaytoonah na ƙin zama a gidan da aka siya ma ta. Ita kuma Zaytoonah ta dage a kan ba za ta zauna ba, tafi ƙarfin ta zauna a gidan nan. Idan baida ƙarfin siya ma ta gidan da ya dace da ita ita ta siya.

"Kin ci darajar rabo da ya shiga tsakanin ku amma Wallahi da sai na sa ya datse igiyar da ke tsakanin ku a yau-yau É—in nan"

Zaytoonah da itama ta riga ta kawo wuya ta ce " Hajia dan Allah ki sa ya sake ni. Indai kin cika Zainab 'yar Sarki Muhammad Abbas ki saka Daddyn Raziya ya sake ni. Ai na san dama abinda kike so kenan tun farko to nima yanzu na gaji da auren ki ce ma sa ya rabu da ni"

Hajia Abu dai an taɓo ma ta inda ke ma ta ƙai-ƙai ta ce " ki sha kurumin ki. Aurenki da Galadima ya ƙare daga yau"...

Zazzaɓi ne ya rufe Zaytooonah mintuna kaɗan bayan wayar su da Hajia Abu. Ta san Galadima na sonta a da but what if chanjawar da yai zai sa ya amince da buƙatar Hajia Abu what if he divorce her. Ta ya za ta fiskan ci Mommy.

Washegari ko iya tashi ba ta yi ta kula da yaran ta ba. Tabitha mai aikinta ne ta shirya su suka wuce makaranta. Da ƙyar ta iya miƙewa ta bawa Alinah nono. Yarinyar ma kaman zazzaɓin na damunta.
Ba ta tashi ba sai ƙarfe shaɗaya na safe, inda ta yi wanka ta shirya Alinah akan su je su ga Likita.

Lokacin da ta gama shiryawa ta É—au wayanta za ta sa a jaka ta ga missed call É—in Salman da kuma text daga Galadima. Hannu na rawa ta buÉ—e text É—in.

*ki koma gidan ku, zan neme ki daga baya*

Dafe ƙirjinta ta yi tanajin wani abu mai tsini na sukan ƙirjin na ta.
'Shikenan ya sakeni' ta furta a hankali.

Da farko fasa fita Asibitin ta yi amma daga baya da Alinah ta fara kuka saboda zazzaɓin da ya dawo ya sa dole ta wuce Asibiti da ita.

Bayan an duba Alinah. Likitan ya tambayi Zaytoonah ko tana ɗauke da wani cikin ne ta ce ma sa a'a sai dai gwajin da aka yi ya ƙaryata amsar da ta bayar.

"Oh no! Ya Allah why now?"
Ciki bayan Galadima ya rabu da ita. Ciki while Alinah was barely 5 months.
Bayan ta karɓi magunguna ta wuce gida jiki a sanyaye. Ranan yadda ka san an cire ma ta laka haka ta wuni. Ta kasa taɓuka komai. Ƙarshe ta yanke hukuncin komawa Zaria gobe.

Saukar rana ta yi a gidan su. Mommy ba ta nan, ta tafi ABU, tana faman ƙoƙarin shirye-shiryen yin internal defence ɗinta. Tafiya America da ta yi ya delaying zamanta Doctor.

Suna gidan Salman ya same su inda ta sanar da shi Galadima ya saketa. Abin mamaki tana maganar tana hawaye.
Salman ya karɓi wayarta ya karanta text ɗin.

"Ni banga kalmar saki a nan ba. Cewa yai ki je gida zai neme ki"

"Ya sake ni. Hajia Abu ta saka ya sake ni i'm sure of it"

"Lallai Zatoonah a gaishe ki, ni banga inda wannan ya zama saki ba"
Ya ajiye ma ta wayar ya wuce É—akin sa. Zaytoonah ta cigaba da goge hawaye. She was just bluffing lokacin da ta ke yiwa Hajia Abu magana.

Ko da Mommy ta dawo ta ga Zaytoonah a gida da yara ba ta tambayi komai ba sai da yamma bayan yaran sun fita wasa ya saura su biyu a gidan.
Sai da ta gama jin bayanan Zaytoonah kafin ta ce "shikenan nan ai Mrs Millionaire. Sai ki zauna har lokacin da zai neme ki"

"Mommy..."

" taurin kai Zaytoonah, taurin kai Zaytoonah. To Allah ya kyauta"
Daga haka maganar ta tsaya...

***

Malam Shehu na zaune a rumfar sa yana gyangyaÉ—i kamar daga sama ya ji ana cewa "Daddy i want watermelon"
Kalmar Daddy ya sa shi shiga duniyar tunani, wasu shekaru da su ka wuce akwai yarinyar da ta ke kiran sa da suna Daddy.

"Daddy i want ice cream" muryan wata yarinya 'yar ɓukuta ya doki kunnen sa yayinda idon sa ke ganin kyakyawan fiskarta mai ɗauke da cute dimple.

Mutumin da ke tsaye da 'yarsa a bakin rumfar ya É—aga murya ya ce cikin gwarancin Hausa "Malam nawa kwallon Kankana?"

Malam Shehu ya yi firgigit ya duba mutumin wanda ke sanye cikin baƙin suit tareda 'yarsa wacce za ta kai shekara goma tana tsaye gefensa sanye da riga da wando blue na denim jeans.

"Malam Shehu lafiya?" Maƙocinsa wanda shima kayan marmarin ya ke siyarwa ya faɗa ganin yadda ya ke kallon Inyamurin da zai sayi kankanar kamar wani mutum-mutumi.

Yadda Malam Shehu ke juye-juye yana ganin wajen da ya ke kamar makahon da idon sa ya buɗe ya sa Inyamurin ya wuce teburin maƙocin Malam Shehu ya sayi Kankana.

"Lahaula wala ƙuwwata illa billah" Malam Shehu ke maimaitawa lokacin da komai da ya danganci rayuwar sa ke dawo ma sa daki-daki...
2/11/21, 10:04 PM - ****: 71

Bismillahir Rahmanir Rahim

*Father's love*

Ba shi da abinda zai saka wa mutanen da su ka riƙe shi amana a wannan gari sai dai ya bi su da addu'an Alkhairi.
Chapter 142 · 0% Book details