Sashe 136
Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Duk da Mommy ta ma ta bayanin dalilin da ya sa ba ta bawa Zaytoonahnwaya idan Galadima ya kira, saboda yana cikin process na treatment É—in ta ne.
Amma ko sau É—aya ai ya kamata ya zo ya duba ni, ko sau É—aya. Abinda ta ke tunowa kenan lokacin da video call É—in ya connecting.
"Masha Allah! Princess ke ce haka" Zaytoonah ta haÉ—e fiska kamar wata Boss.
"Na san ina da laifi amma yanzu dai a min murmushi na gani ko hankalina zai kwanta"
Zaytoonah ta sake haÉ—e fiska tareda kau da kai gefe.
" 'Yan mata ba za ki kalli Tsohon na ki ba"
Sai da ta ja ma sa aji kafin ta juyo ta ƙura ma sa ido.
"Kin yi kyau" ya faÉ—a tareda hura ma ta kiss.
"Dole na zo na ganki 'yan mata na, haƙuri na ya ƙare. Ina 'ya ta?"
"Wai 'yar ka. Lokacin da na ke wahala da ita ai ba ka nemi ka san lafiyata ba"
"Adaeze ban sani ba, ba ki sanar da ni ba. Ina buƙatar samun lafiyar ki shiyasa na bi umurnin da Hajia ta faɗa. Da na sani da ba zan iya haƙura iya waɗannan lokacin ba"
"So ba ma dan ni za ka zo ba sai dan Babyn ka. Shikenan na san matsayina"
"Ya Allah! Barrister kar ki É—aure ni da maganar da ban faÉ—a ba"
" idan na yi hakan mi Justice Yunus zai yi a kai?" Ta faÉ—a tana wani juya ido.
" hukuncin ƙarisa rayuwar ki a gidan Yunus ɗan Muhammad Abbas, tareda aikin..."
Ihun da ya ji ya sa shi faÉ—in "Subhanallahi! Princess ina zuwa"
Da sauri ya ajiye wayar ya fita.
Ghazala ce ta ranƙwashi Raziya shine ta challa wannan ƙaran sanin cewa Daddy na gida.
"A ni ki ke wa rashin kunya Raziya. Ni ki ke cewa munafuka"
Kamota ta yi da ƙarfi ta fara kai ma ta duka da hannu ita kuma sai ihu ta ke tana kiran Daddy.
Da gudu Galadima ya sauko dan ya tsorata da ihun da ya ke ji.
"Mi ye haka?"
Ghazala ta sake Raziya ta kalli Galadima tana huci. Maganar haihuwar Zaytoonah ya dagula ma ta lissafi ga wannan banzan yarinyar ta tunzura ta.
"Ghazala ba magana na ke ba"
"Rainin yarinyar nan yayi yawa, har ta kalli tsabar ido na ta ce min munafuka. Wani irin tarbiyya ne wannan"
Kallon ta ya ke cike da mamaki, bai taɓa tunanin Ghazalar da ya sani kusan shekara ɗaya da rabi da ya wuce ba ne. Matar da ke haba-haba da yaran sa tana lailaya su kamar ƙwai shine wai yau ta ke dukan ma sa 'ya.
"Ki sameni a É—aki" ya faÉ—a tareda barin gurin. Bayan wucewar Galadima, Ghazala ta zunguri Raziya ta ce " ke kuma ni da ke a gidan nan"
Da ta samu Galadima a É—aki tambayarta yai dalilin dukan Raziya da ta ke yi.
"Ni ban gane ba. Ba ni da ikon hukunta 'yarka kenan idan ta haihu ko me?. Dole mana ka min gori tunda ban haifa ma ka komai ba ai ita waccar mai ciwon haukar da ta haihu tun safe ka ke ta wani fara'a kamar wanda akai wa kyautar Aljannah"
Duk bayanin da ta yi bai tanka ba sai kawai ya sake tambayar sa "mi Raziya ta mi ki?"
Rasa abin faÉ—a ta yi dan idan aka fara tone-tone ba za ta ji da daÉ—i ba tunda dai akan maganar Zaytoonan ne Raziya ta kirata da munafuka.
"Yau na san matsayina a gidan nan, wato kallon matar uba ka ke so su min ba kallon uwa ba. Shikenan duk abinda Raziya za ta yi a gidan nan ba zan sake saka baki ba" daga haka ta fice daga É—akin a fusace.
Ya ji zafin abinda ta yi amma farin ciki da ya ke ciki ya kawar da ɓacin ran abinda ta ma sa dan haka ya maida hankalin sa kan wayar sa dan ya kira Zaytoonah ya ga Babyn sa.
Itama Zaytoonan taburman fishi ta hau dan sau uku yana kiran wayar amma ba a É—auka ba...
***
Yadda ake shirye-shiryen suna ka ce Baby Alinah ce haihuwar farko da akaiwa Galadima. Kwana kafin suna ya tattara iyalin sa suka koma Zaria dan a nan za ayi sunan. Duk da mai jego da baby ba sa nan amma hakan bai hana yin hidiman suna sosai ba. Ghazala dai sai ido ta zubawa Galadima dan tun ranan da aka yi case É—in dukan Raziya da ta yi bai sake sake ma ta fuska ba.
Suma 'yan uwan Galadima da su ka yi ta shige da fice ranan suna ba ƙaramin ƙona ran Ghazala yai ba, ita kam da namiji aka haifa da ta shiga uku a hannun su.
Wannan suna ya sa ta sake kwaÉ—aita haihuwan nan, ko da artificial insemination ne za ta yi sai dai matsalarta É—aya ba lallai Galadima ya yarda da irin wannan abu ba sai dai...
Haka aka sha hidimar suna aka watse yarinya dai ta samu sunan da mahaifiyarta ta zaɓa ma ta wato ALINAH...
***
Yau sati biyu kenan Shehu na zuwa gidan Malam Zulkiflu mai ƙusumbi. Duk da zuciyar sa baya son zuwa wajen wannan Bawan Allah amma duk sanda Malam ɗin ya aiko ɗaya daga cikin Almajiransa su kira shi sai ya tsinci kan sa da kasa yi ma sa mu su.
Yau ma ɗin zaune ya ke gaban Malam wanda ke rubutu a wani ƙaramin Allo.
Tambayar da Malam ɗin ya sako ma sa ne ya sa shi yin nazari amma tun ɗazu da ya ke ta ƙoƙarin gano amsar tambayar Malam ɗin bai gano komai ba. Tambayar Malam tambaya ce da a baya ba ya son ji amma yanzu kuma da Malam ɗin yai tambayar sai ya tsinci ka san da son sanin amsar.
Chan ya nisa ya ce " ni dai Malam ba zan iya cewa takamaimai ga daga inda na fito ba ko kuma na ce ga asali na ba, amma kuma gaskiya na jima ina yawo garuruwa ina kasuwanci dan har yankin Niger na shiga, daga nan ne ma na juyo zuwa Sokoto kafin kuma na dawo nan"
Malam ya ɗago ido ya kalli Shehu ya ce "da izinin Allah za ka tuno komai. Kamar yadda na faɗa ka riƙe addu'ar da na faɗa ma ka"
Shehu ya gyaɗa kai. Bayan Malam ya gama rubutu a jikin Allon ya kawo ruwan ZamZam da ya tanada saboda ayyukan sa irin wannan ya wanke Allon da shi sannan ya bawa kwanon da ke ɗauke da ruwan ya ce ya sha. Ba musu kuwa ya karɓa ya shanye tas...
***
Yau ne za a yiwa Zaytoonah gwaji na ƙarshe. Ya kamata a yi shi tun kafin ta haihu amma saboda ta yi nauyi lokacin shiyasa aka ɗaga zuwa bayan ta haihu.
Addu'o'in da ake ma ta da wanda ta ke yi duk ya taimaka wajen yaƙice ɗimuwa da ta ke yi duk lokacin da ta ke cikin duhu, ko ta ga hoton Ben. Ta kuma dena kama sunan Zuhayr a duk lokacin ma da ta firgita, ƙwaƙwalwarta ya fahimci Zuhayr ya tafi kenan ba zai kuma dawowa ba.
"Kamar yadda na faɗa miki indai ki ka ci wannan test ɗin to zan rubuta miki cewa kin warke gaba ɗaya. Its a difficult test amma inada yaƙinin za ki ci"
Likitan ta ya faÉ—a.
Ya riga ya ma ta bayanin test É—in kuma ta fahimta.
Baby Alinah na goye bayan Mommy lokacin da Dr ya rufe fiskarta da wani ƙyalle. Mommy ce ta riƙe hannunta ta shigar da ita ɗakin da za a ma ta gwajin. Bayan an kulle ƙofar ne Dr da ke waje ya ce ta cire ƙyallen da aka rufe ma ta ido. Tana cirewa kuwa ta gan ta cikin ɗaki mai duhu.
Mommy da Likita suna tsaye jikin na'uran computer suna ganin duk abinda ke faruwa a cikin É—akin.
ÆŠakine mai duhu an riga an kwatanta ma ta inda switch É—in kunna wutan É—akin ya ke dan haka abinda za ta yi shine ta je wajen ta kunna wutan.
Zaytoonah na tsaye cikin duhu ta ja dogon numfashi kafin ta karanta addu'a a ranta ta fara takawa a hankali. Ba ta fi taku biyar ba ta ji an kira sunan ta.
"Zaytoonah" da murya irin ta Ben. Ta É—an ji wani dim a ranta amma ta dake ta cigaba da tafiya.
"You snatched away Zuhayr from me i'll kill you today, no body will save you" muryan Ben ya ratsa kunnen ta. Da da ne ihu za ta saka amma yanzu confidently ta ce "i know you are not Ben. Ben is dead, he's gone forever"
Kyalƙyalewa akai da dariya sannan aka ce "you're joking Zaytoonah. I survived the gun shot, i'm alive" ya na gama faɗi sai kawai ta ga alamar ana takowa wajen ta.
Danne tsoron da ke zuciyarta ta yi tana tuno cewa Mommy da Likita da 'yarta suna nan waje suna jiranta ba abinda zai sameta a wannan É—aki.
"I'm going to kill you Zaytoonah"
Yana gama maganar ta ji an taɓa kafaɗarta ta baya.
Ihu ta ke son yi amma ta rintse ido ta maimaita abinda Galadima ya sanar da ita jiya "Tawakkaltu Alallah" a fili.
"Nobody is going to save you from me Zaytoonah" aka faÉ—a saitin kunnen ta.
"You are not real. The reality is, Ben died years ago, he's never coming back" daga haka kawai ta ƙarisa da sauri ta je karshen ɗakin ta laluba hannunta a bango har ta samu switch ɗin wuta ta kunna. Tana kunnawa haske ya karaɗe ɗakin sai ga robot guda biyu ma su kaman Ben a ɗakin. Daga waje aka saka tafi.
Fitowa ta yi daga É—akin tana murmushi yayinda Mommy ta rungumeta cike da farin ciki.
Duk maganan da ta ke a ciki wani nurse ne da ke gefen Likita ke magana da shigen muryan Ben yayinda ya ke directing movement É—in robots É—in.
Lokacin da Zaytoonah ta janye jikinta sai kawai ta ga hawaye a idon Mommy.
"Mommy kuka kuma?"