← Book details Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 105 OF 161

Sashe 105

Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ina fata wannan kotu za ta duba wannan lamari ta kuma ba da damar cigaba da ƙaran da client ɗina ta shigar tun farko, wanda tsoron kada a hallaka ma ta 'ya'ya ya sa ta janye ƙaran saboda akwai hujjoji ƙwarara da ta ke da shi akan Chief Udodiri"

Justice Ayoola ya ce kotu ta bada damar a dawo da ƙaran ranan 6 ga wata mai zuwa wanda ya kama saura kwana goma sha shida kenan, kafin nan a tisa ƙeyar Chief Udodiri zuwa gidan yari.

Lawyan Udodiri ya tashi yana neman a ba da bail ɗin Udodiri saboda lafiyar sa amma alƙalan ba su amince ba.

Zaytoonah da Mommy fiskar su wasai su ka fito daga kotun. Suna fitowa kuwa 'yan jarida su ka mu su chaa amma ba su tanka mu su ba.

Da ke wannan karan su Chief Asibong sun zo kai tsaye gidan sa da ke nan Abujan su ka nufa.

Sai da aka samu zama aka ci abinci kafin aka sako zancen abinda ya faru. Abin mamaki Chief Asibong ya san komai, su Mommy da Zaytoonah ne kawai aka bar su a duhu dan Justice bai faɗa mu su dukkan abinda ke faruwa ba, sun dai san an ƙwaco yaran kuma yaran na gidan sa. Zaytoonah dai bin instructions ɗin sa ta ke yi a kotun tunda wannan karan babu shi a Alƙalan da su ke sauraron ƙara...

Chief Arinze ne ya samu Chief Asibong akan zai taimaka mu su wajen samun solid evidence akan Udodiri. Yana shakkar zaɓen da za ayi bana, saboda mahaukatan kuɗi Udodiri ya kashe a mazaɓar sa saboda a zaɓe shi, siyasar yanzu kuma na kuɗi ne. Da kuɗi ake siyan ƙuri'on mutane.

Tunda aka fara case ɗin ya ke faɗi tashi wajen ganin ya samu evidence mai ƙarfi akan Udodiri saboda a samu a turashi kurkuku. A hankali ya dinga amfani da kuɗi da siyasa wajen binciko abubuwan da su ka faru shekaru talatin da su ka wuce. Duk abubuwan da 'yan uwan Udodiri su ka ɓoyewa Mommy saboda suna tsoron fushin Udodiri sai ga shi Chief Arinze ya ƙwaƙulo komai.

Lokacin da Chief Asibong ya samu support ɗin Chief Arinze shine ya kira Justice ya sanar da shi komai, bai kira Mommy ba ne saboda ya san a wajen Justice zai samu abinda ya ke so. Bayan Udodiri ya nemi ganawa da Mommy Justice ne ya nemi biyan mai restaurant ɗin kuɗi saboda su samu daman saka camera da za ta ɗau hiran na su. Fortunately kuma ashe Justice ya wayi asalin mai restaurant ɗin kuma ya taɓa yi ma sa taimako a baya. Dan haka ba ɓata lokaci aka haɗa camera ɗin a wajen da Udodiri yai booking kafin ma ya zo.

Da taimakon Chief Arinze aka gano waÉ—anda su ka sace su Junior, bisa shawaran Justice aka bi komai a sannu har aka kawo wannan rana.

Yadda 'yan uwan Mommy ke ta yaba Justice ya sa Zaytoonah yin murmushi, Ko ba komai ta ji daÉ—in hakan...

***

Justice da kan sa ya maido da yaran gida bayan sun yi kwanaki goma shabiyu tareda shi. Ba ƙaramin sabo su ka yi da sabon Daddyn na su ba, kwana huɗu da su ka yi da 'ya'yan sa sun saba sosai da Suhailah. Falaq tana ɗan shiga harkan su amma ba sosai ba sai dai Razia kam ko fiskar su ba ta son gani. Ga wani mugun kishin su da ta ke ji dan gaba ɗaya daga Justice ya dawo to yana maƙale da yaran ne.
Ba abinda ma ya ke É—aga ma ta hankali irin da fa an auri Maman su shikenan za su koma zama tareda su gida É—aya kamar yadda Hajia Ghazala ta jaddada ma ta, tun kafin Zaytoonah ta shigo gidan already ta riga ta tsaneta.

Zaman abinda bai fi minti goma shabiyar ba Justice yai sannan yai sallama da Mommy da yaran. Yaran su ka zo su ka rungume shi suna tambayar sa yaushe zai sake zuwa. Ya ce mu su ko gobe ma zai zo idan suna so. Sai su ka fara tsalle suna haÉ—a baki wajen faÉ—in "muna so, muna so"

Saboda kar su cigaba da takurawa Muhsina wanda mijin ta ya ke shirin dawowa nan da kwana biyu ya sa dukkan su suka tattaro su ka dawo gidan Chief Asibong.

Lokacin da Justice ya fita ne Mommy ta yi saurin shiga É—akin Zaytoonah, sanda ya zo tana wanka amma har yanzu ba ta fito ba.
Tuni ta yi wanka ta shirya amma ta ƙi fitowa.

"Ba za ki je ki yiwa Justice godiya ba"

"Mommy na ma sa a waya"

"Ba na son shirme, ki je kafin ya tafi"

Ta miƙe tana mutsu-mutsu da baki...

Ranan da aka dawo kotu cikin watan Azumi ya faÉ—a.

Kotu ya cika maƙil. Tawagar Chief Arinze da ta Chief Asibong duk suna wajen. Kowa ya zuba ido ya ga yadda za a ƙare shari'ar.

Ikenna wanda ya ke ƙani ne ga Udodiri uwa ɗaya uba ɗaya shi aka fara gabatarwa inda ya ba da shaidar cewa bayan mutuwar Patrick da matar sa duk wani dukiyar su da su ka bari Udodiri ya chanja zuwa sunan sa. Saboda ya cire kan sa daga rikici ya sa shi cewa lokacin da Patrick ya mutu yana ƙarami dan shekarun sa shashida a lokacin. Sai dai daga baya Anty Uloma ta gaya ma sa cewa Udodiri ne ya kashe Patrick saboda ya gaji dukiyar sa.

A hankali Zaytoonah ta ke takawa har ta kai wajen stand É—in, tuni ta farayin laushi, Azumin ya fara shigarta.

"Mr Ikenna ko za ka gaya mana miyasa ba ka bayyana abinda Uloma ta gaya ma ka ba sai yanzu?"

Ikenna ya ce " ina tsoron Yaya na ne saboda dukkan mu ya ja mana kunne akan duk wanda ya tona ma sa asiri zai kashe shi ya kuma kashe ma sa Iyalai. Kuma sanin halin zai iya ya sa na yi shiru"

Bayan Zaytoonah ta gama yi ma sa tambayoyi sannan Lawyan Udodiri shima ya taso yai na shi wanda duk tambayoyin sa ƙoƙari ne na ruɗar da Ikenna kuma hakan bai faru ba.

Bayan an gama da Ikenna sannan Zaytoonah ta gabatar da Ebube da kuma tawagar sa inda su ka amsa laifin su na yiwa Uloma sata da kuma kasheta da su ka yi wanda umurni ne daga wajen Chief Udodiri. Udodiri shiru yai kawai yana sawa a ran sa cewa duk yadda aka yi akwai hannun Chief Arinze wajen tonuwar asirin sa. Ya rantse idan har aka sake shi ba abinda zai hanashi kashe Chief Arinze.

Bayan shaidu da aka gabatar beyond doubt sannan Alƙalan su ka ɗauki hutun minti goma inda su ka keɓe kan su suka tattauna gameda sahihancin dukkan bayanan da aka bayar da kuma irin hukuncin da za a yankewa Chief Udodiri.

Tana zaune da Mommy tana ɗan mammatsa ƙafar ta da su ka riƙe sai ga kiran Justice ya shigo. Kaman ba za ta ɗauka ba amma ganin Mommy ta zura ma ta ido ya sa ta ɗau kiran tareda rage volume ɗin saboda kar Mommy ta ji maganar Justice.

"Haka matar tawa take da raki, yau Azumi 11 fa." Ya faÉ—a bayan ya amsa sallamar ta.
Ba ta san ya aka yi ta tsinci kan ta da yin murmushi ba" wai matar sa. Bayan sai bayan sallah za a É—aura aurn.
"Ina Alfahari da ke Zaytoon, kin yi ƙoƙari sosai"

"Na gode" ta faÉ—a tana satan kallon Mommy wanda ita kan ma hankalin ta baya kan wayar ta su.

Bayan an dawo daga hutun ne chair Justice É—in ya fara bayani kamar haka.

"Bayan kotu ta tabbatar da dukkan shaidu da aka kawo, kotu za ta yankewa Augustus Udodiri Uzodinma bisa laifin kashe rayuka uku tareda cinye dukiya, gamida take 'yancin ɗan Adam da yai ta hanyar azabtar da Maryam Nkiru Uzodinma. Daga ƙarshe kuma an kama shi da laifin kidnapping ɗin ƙananan yara guda uku. Bisa girman wannan laifuffuka Kotu ta yanke ma sa hukuncin kisa ta hanyar rataya.

"Sannan wannan kotu ta yanke wa Chidi da yaran sa hukuncin shekaru biyu a gidan yari. Yayinda Ebube da yaran sa za su ƙarisa rayuwar su a gidan yari.

"Kotu ta kwace lasisin Barr. Toby Rowling har na tsawon shekara bakwai idan aka kama shi yana practising Law kafin nan za a yanke ma sa hukunci mai tsanani.

"Kotu ta damƙawa Maryam Nkiru Uzodinma Kamfanin mahaifinta da Udodiri ya ƙwace tareda gidan sa da ya gina kafin ya mutu dama duk wani dukiya da ya bari kafin mutuwar sa. Sannan Iyalen Udodiri za su biya diyya ga 'ya'yan marigayiya Uloma Uzodinma"

Daga haka Justice Ayoola ya buga gudumar su ta alƙalai.

Hawaye ne ya ziraro a idanun Mommy, Zaytoonah ta yi saurin ƙarasowa wajen ta ta rungumeta itama na zubda hawayen farinciki.

Hayaniya ya ɗan kacame a kotun saboda yadda matar Udodiri da yaran sa guda biyu da jikan sa ɗaya su ka saka ihu suna kuka yayinda Babban ɗan sa namiji ke ta faman ririƙe mahaifiyar ta su yana baya haƙuri....
2/11/21, 10:04 PM - ****: 54

Bismillahir Rahmanir Rahim

*The second wife*

"Dan Allah ki yi haƙuri" Raziya ta faɗa fiska shame-shame da hawaye da majina.

"Ban ji ba, ki ka ce me?" Zaytoonah ta faɗa tana riƙe kunne

" ki yi haƙuri ba zan ƙara ba"

"Good. Da bakin ki kika ce ba za ki ƙara ba sai dai idan ki ka ƙara ɗin mi zan miki?"

"Anything" ta faɗa tana sheshsheƙar kuka.

"Shikenan tashi ki je"

Ta miƙe da ƙyar ta bar ɗakin. Bayan ta fita Zaytoonah ta ce "ashe rashin kunyar na ƙarya ne. Gaba ki sake neman tsokana, ni da ke a gidan nan".

Tana kitchen ta ji shigowar Hajiya Ghazala tana wani É—aga murya wai ina Raziya.
Zaytoonah ta ja tsaki ta cigaba da abinda ta ke.

"Ta dake ki?" Hajia Ghazala ta tambayi Raziya da ke kwance. Raziya ta girgiza ma ta kai.

"Aiki kawai ta sa ki?"

Ba ta iya magana ba sai gyaÉ—a kai da ta yi.

"To bari ki ji indai kina so ta bar gidan nan. Idan Daddyn ku ya kira ki ce ma sa ta dake ki kin ji"
Chapter 105 · 0% Book details