Sashe 28
Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tundaga marin da Iya ta ma ta ta dena kai abinci gidan, idan an bata abinci sai ta fita da shi sai ta tsaya a ta lungun da Almajirai ke zama suna cin abinci ta juye mu su sai ta ɗan tsaya kaɗan kafin ta wuce gida. Wani lokaci idan ta juye abincin a kwanon almajiran ko kafin ta juye taga nama dumu-dumu sai ta tsaya ta zaƙolo naman da ke ciki ta ci kafin ta juye mu su ta wuce gida.
Ta sawa ranta ba za ta ƙara kai wa su Iya abinci ba.
A ranan na huÉ—u ne da Maryam ta je duba su Sadiq sai Hajjo ke ma ta habaici wai dan ta ga Sadiq ya damu da girkinta ne shine ta ke ja ma sa rai kafin ta aiko. Ta yi maganan ne saboda missing daddaÉ—an girkin Maryam da su ka yi cikin kwanakin.
Maryam ba ta gane zancen ba amma ta dake ta ce "Sadiq duk lokacin da ka ke son cin abinci ka zo gida ka ji" yaron ya gyaÉ—a ma ta kai. Dama yana son zuwa Hajjo ke hanashi, ita a nata tunanin idan ya je ya ci a gidan Maryam ba za ta aiko musu ba. Tunda dai abincin da ta ke aikowa ba abincin da Sadiq kaÉ—ai zai ci ba ne tunda ko tuwo ne leda biyu manya ta ke sawa.
Zuwanta gida ta samu Zaytoonah na yin assignment a falo.
Sai da ta zauna ta ce " Adaeze zo nan"
Zaytoonah ta taso da sauri dan ta san indai Mommy ta kirata da Adaeze ko Princess to za'a lallasheta ne da abun ƙwalama. Ɗazu da rana ta fasawa Mommy plate sai Mommyn ta sa ta kneel down ta ɗaga hannu ta rufe ido na kusan minti shabiyar.
Maryam ta ɗaura Zaytoonah akan cinyarta tana shafa kitson chuku da aka ma ta wanda jelar sa ya sauka har kafaɗanta. Maryam da T J duka suna da gashi sai dai Zaytoonah yanayin gashin T J ta ɗauko baƙi mai tsantsi ba kaman na Maryam ɗin da ya ke brown kuma kinky hair ba.
"Adaeze a wa kike kai wa abinci idan na aike ki gidan Iya?"
Nan da nan idonta ya kawo ruwa.
"Ban ce ki min kuka ba, gaskiya kawai za ki gaya min. Idan ma kin yi ƙarya zan gane kuma dukan ki zan yi"
"Mommy i'm sorry" ta faÉ—i tana fashewa da kuka
"Zubar wa ki ke yi?"
Ta yi saurin girgiza kai
"Ya kike yi da shi?"
Sai da ta sauke ajiyar zuciya kafin ta ce "Almajirai na ke kai wa"
Maryam ta ƙura ma ta ido dan ta gane ko ƙarya ta ke ma ta amma gaskiyar ce dai ta faɗa. Ta sani saboda abinda Iyan ta ma ta ya sa ta ɗau wannan matakin. She wont blame her tunda Iya ce ta creating wannan ƙiyayyar tun farko.
Ta sa hannu ta goge ma ta hawaye ta ce shikenan daga yau za ta dinga aikan Auwal idan baya nan za a nemi ko Almajiri ne ya kai mu su. Zaytoonah ta gyaÉ—a kai...
***
"Maman Bola, Maman Bola" Humairah ta dinga faÉ—i lokacin da su ka fito daga cikin school É—in za su je wajen Manu mai mashin wanda ke kawo su makaranta.
Maman Bola suna ne da wata 'yar ajin su Zaytoonan ta sa ma ta saboda kullum itace da takarcen ciye-ciye idan ta zo school. Tsab-Tsab za a shiryata zuwa makaranta amma kafin a tashi ta ɓata jikinta. Idan ba ka ga uniform ɗin ta ya yi dumu-dumu da kayan ƙwalama ko maiƙon abinci ba zaka ga ya ɓace da ƙasa. Tana zaune a aji tun ma kafin a fita break za ka ga ta fara buɗe food flask ɗinta tana cin soyayyen dankali ko ƙwai, idan ta ɗebi loma ɗaya biyu ta ga za a ganta sai ta yi saurin rufewa ta goge hannunta na maiƙo ajikin uniform ɗin. Zaytoonah kenan.
Humairah ba ta san da sunan ba sai da yau suna fitowa Habiba 'yar class ɗin su Zaytoonan ta kira ta dashi. Shine kuma Humairan ta samu sai tsokanarta ta ke yi. Zaytoonah ba ta kulata ba dan Mommy ta hanata dukan Humairah kullum ta kawo ƙaran ta sai ta riƙa cewa ita ce Babba ta yi haƙuri. Ita kuma Maryam ba ta son ƙara ingiza wutar gaban da Iya ta kunna ne tsakanin yaran.
Daidai wajen ɗalibai dayawa da ke jiran a zo a ɗaukesu Zaytoonah ta yi wuf ta cire hulan Humairah. Ƙitson chuku aka ba su a satin kuma shi ke kan Humairan amma da ke ba ta da gashi sai chukun ya ƙi haɗuwa balle ma har a haɗe shi a dunƙule kamar yadda na Zaytoonah yai.
Zaytoonah ta fara " ku ga Humairah me ƙwaƙwuyayyen gashi, ƙwaƙus, ƙwaƙus ƙus, ƙus, ƙus"
Haka ake tsokalar yaran da ba su da gashi a class na su kuma abun na sosa mu su rai har ka ga suna kuka, wani lokaci sai Aunty ta tsawatar ake denawa.
Itama Humairan kuka ta fara musamman da ta hango wasu É—aliban sa'anninta na dariya.
Har Manu ya saukesu Humairah ba ta dena kuka ba. Ta shiga gida da gudu tana kuka, straight É—akin Iya ta wuce tunda ba ta ganta a falo ba...
Mommy ba ta dawo daga office da wuri ba yau dan haka gidan maƙotan su Maman Fawaz su ka wuce dan su jirata, da ke Auwal sai ƙarfe biyu zai dawo saboda a JSS 2 ya ke. Idan kuma ya rigata dawowa zai karɓi key a wajen Maman Fawaz ya buɗe mu su gidan.
Su na zaune a falo suna wasa da yaran Maman Fawaz ɗin sai ga Iya ta yi sallama hannunta riƙe da Humairah.
"Iya ga ta nan, dama nan su ke zama idan Mommyn su ba ta nan" Humairah ta faÉ—a tana nuna Zaytoonah.
"Zo nan dan Uwar ki"
"A'a Iya ke ce a gidan na mu" Maman Fawaz ta faÉ—a da fitowanta kenan daga kitchen.
Ba ta kula Maman Fawaz ba ta je ta finciko Zaytoonah.
"Dan Allah ki yi haƙuri kin san sha'anin yara..."
"Ba ruwan ki jikata ce" Iya ta katseta
Zaytoonah na kuka haka Iya ta ja ta su ka bar gidan. Direct gidan Hajjo su ka wuce wanda tun a hanya Iyan ke ta surfa masifa.
Suna zuwa kuwa ta ɗauko almakashi ta danneta ta fara aske ma ta gashi tana faɗin gaba ta ƙara yiwa Humairah Shalele dariya ƙwandala za ta ma ta.
Humairah na dariya ganin yadda dogon gashin Zaytoonah ke zubewa a ƙasa.
"Iya kin san dai Maryam ba za ta yi shiru ba ko?"
Hajjo ta faÉ—a bayan ta fito daga kitchen jin kukan Zaytoonah.
"To ko Ubanta yana nan ya isa yai magana balle uwarta Inyamura"
Hajjo ta taɓe baki ta koma kitchen ɗin. Jikarta ce dan haka ba ruwanta da abinda ta ke yi.
Bayan ta aske gashin wanda ya saura kaman irin low-cut ɗin nan sannan ta riƙe kunnen ta ta ce " duk ranan da kika sake tsokanarta sai na ɓaɓɓallaki"
Har gara Salman sau dubu a wajen Iya akan Zaytoonah wacce kamanninta da Maryam ya ƙara sa ma ta baƙin jini a wajen Iyan. Banbancinta da Maryam kawai farin fata ne wacce ita Zaytoonan ta ɗauko baƙin fatan T J.
Da gudu Zaytoonah ta fice a falon wanda tsabar bata ganin gabanta sai da ta bugu da ƙofa. Ko zafin bugun bai dameta ba ta fice daga gidan tana kuka.
A hanya ta haÉ—u da Auwal da ke shirin shiga gidan Maman Fawaz.
"Zaytoonah wa ya dake ki? Ina ki ka je? Iya ce ta dake ki ko Umma Hajjo?"
Duk tambayoyinsa ba wanda ta amsa ma sa sai kuka kawai...
A bakin ƙofa ta tsaya tana kuka tana jiran Mommynta, Auwal yayi-yayi ta shiga gida ta ƙi dan haka shima ya tsaya bakin ƙofan yana cigaba da lallashinta, shi bai ma lura da kanta ba saboda akwai hula a kanta.
Salman ma ganin yadda Zaytoonah ke ta kuka ya sa shi fara kukan, su na yawan faÉ—a da Addar ta sa amma yana son ta sosai.
A haka Maryam ta dawo daga office kusan 2:30pm ta same su.
Tana saukowa daga mashin Zaytoonah ta je ta faÉ—a jikinta tana kuka tana Mommy.
"What happened?. Auwal miya sameta?"
"Nima ban sani ba amma ina tunanin Iya ce ta dake ta"
Ta É—an sunkuya dai dai tsayin Zaytoonan ta ce " Adaeze waya dake ki?"
Zaytoonah ta sa hannu ta cire hulan kan ta tana cigaba da kuka.
"Iya did this to you?"
Ta gyaÉ—a ma ta kai.
Rarrashinta ta fara yi amma inaa ta ƙi yin shiru hakan ya sa ta ɗauketa duk da girmanta a hakan ta shiga da ita cikin gida.
Yau duk kayan ƙwalamar an ma ta tayin su ta ƙi ci sai kuka. Daga baya ne ma Maryam ta lura da fashewar da gefen goshinta yai. Ta goge jinin da ya bushe ta shafa ma ta magani.
A jikinta ta kwanta tana shafa bayanta har ta yi bacci, sannan ta kwantar da ita a gado.
Ranta idan yai dubu to ya ɓaci, ba za ta bari a cigaba da cin zalin 'yar ta ba dan haka ta wuce gidan Hajjo cike da ɓacin rai.
Spaghetti ce akayi dafa dukan ta wanda yai yi wani irin dahuwa sosai ya caɓe. Amma a haka su ka zauna suna ci, Humairah dai wasa ta ke yi da shi dan abincin bai ma ta ba. 'Yar indomie noodles ɗin nan Ummanta ba ta dafa ma ta yai kyau kaman na sauran 'yan ajin su.
Sallama da ta zama dole Maryam ta yi lokacin da ta shiga falon.
Duk su ka tsura ma ta ido, Sadiq ne kaÉ—ai baya wajen dan yayi bacci a É—aki.
"Wallahi Wallahi duk ranan da wani a gidan nan ya sake taɓa min lafiyar 'ya ta sai hukuma ta rabamu, ko da kuwa uwar da ta haifi uban ta ne. Cin zalin ya isa haka, ya isa haka, i repeat ya isa haka. Idan ba a son 'ya ta a bar min ita ina son kayana. Idan kunne ya ji jiki ya tsira" daga haka ta fice a gidan.