Sashe 15
Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Waye?" ta faÉ—a fiska a É—aure dan ta san halin 'yartata da rawan ido.
"Hamma Tijjani, Hamma Tijjanin Iya"
Inna ta zaro ido waje sai kuma ta fara murmushi...
Ba su bar Ringim ba sai da ta tabbatar ta zuga Iya akan ta haÉ—a auren Tijjani da Hajjo. Itama dama ba son Maryam ta ke ba dan haka ta yi saurin na'am da zancen tunda dai yanzu babu Baffah da zai taka ma ta burki. Amma wani hanzari ba gudu ba ta fi son T J ya auri Bafulatanar usul sannan gaskiya tarbiyyan Hajjo bai ma ta ba dan taga yadda Hajjon takeyi cikin kwana biyar da su ka yi a gidan, yarinyar idonta a buÉ—e ya ke.
Inna ta hau fushi tana faÉ—in Iya za ta nuna ma ta cewa 'yarta bare ce tunda Uban Hajjo ba Bafulatani ba ne. Mijinta Warjawa ne. Auren fari ta auri É—an uwanta Bafulatani ba ta son sa haka su ka rabu ko shekara ba su yi ba, ta je ta auri Sama'ila wanda cirani ya kawo shi Ringim a lokacin.
Iya ta shiga ba ta haƙuri tareda cewa indai haka ta fassara maganan ta yi haƙuri ba manufarta kenan ba, za ta yiwa Tijjani magana ya auri Hajjo...
*still mu na kan share hanya ne a labarin domin jaruman mu ba ta ma iso ba tukunna. The sad truth is i'm inlove with Maryam-Nkiru and Tijjani😔*
*Don samun daman karanta cigaban labarin za a biya 300 ta account number kamar haka:*
3099546325
Firstbank
Azizat Hamza
*ko kuma katin MTN na 300 zuwa ga wannan numbar 08137311900*
Za'a tura Shaidar biya zuwa ga wannan numbar still 08137311900 ko kuma ma dai domin ƙarin bayani za a iya tuntuɓar numban, preferably chat ko text.
*Allah ya ba da ikon biya amin*
2/11/21, 10:04 PM - ****: *Chronicles of*
*...... ...... .......ZAYTOONAH*
Rubutawa.....Azizat
Wattpad@Azi_zat
https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref
ð•€â„•ð•Šð•€ð”»ð”¼ ð”¸â„ð”¼ð•Žð”¸ ð•Žâ„ð•€ð•‹ð”¼â„ð•ŠÂ©
*(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*
*Free page*
*5-Maryam*
Bismillahir Rahmanir Rahim
Ba abu ne mai sauƙi ba amma kuma zai yi komi domin ta samu farin ciki. Fasa tafiyar sa ya zo da kace-nace a cikin gida sai dai kuma bai damu ba tunda ya tabbatar buƙata za ta biya. Kwana takwas ya ƙara kafin ya koma chan Obowo, cikin kwanaki takwas ya nemawa Nkiru aiki a wata primary school na gwamnati, ba a dai ɗauketa officially ba saboda ba ta da takardar shaidar karatu amma ance da zaran ta samu takardun ta za a aika ministry a ɗauketa aiki. Kafin nan kuma za ta dinga aiki ne ana ba ta ƙaramin allowance duk ƙarshen wata. Takardunta ba za su samu ba saboda ta baro su a gidan su da ke Owerri, wanda ya rage ma ta mafita ɗaya wato sai dai a sake turo mata takardun daga chan makarantar su, gashi da primary school da high school ɗin duk a England ta yi. Graduation ɗin su ma ko wata biyu bai yi ba su ka dawo Nigeria.
Ranan da T J ya tafi ta sha kuka sosai dan ji ta ke kamar idan ya tafi ba zai dawo da wuri ba. Ba ta san T J ya shiga ranta har haka ba sai ranan da ya tafi, ji ta yi tamkar ya tafi da zuciyar ta ya bar gangan jikin a Ringim.
*"Ba na son ki rinƙa yin dare a waje, ban yadda ki keɓe ke kaɗai da Okafor ba. Banda zuwa church da dare.."*haka yai ta jero ma ta sharuɗɗa safiyar ranan da zai wuce.
Wasa-wasa sai gashi an shafe sati ɗaya da tafiyar sa tun tana kuka har ta dena ta maida hankali ga koyarwan da ta ke yi. Okafor bai dena bibiyarta ba dan ko ta je church haka zai liƙe ma ta, ga pastor ma ya nace akan sai ta bar gidan su T J. Ita yanzu banda kitso ba abinda ke kai ta gidan su Okafor, the more ya ke son kusanci da ita the more ta ke ƙara ja baya da shi.
A gida kuwa ba a sati ɗaya ko biyu Muntari bai zo ba, tun Iya ba ta gane saboda Nkiru ya ke zuwa ba har ta gane ta dinga faɗa tana zage-zage shi kuwa ya kwantar ma ta da hankali akan yana hakan ne saboda yana so Nkiru ta musulunta, idan Nkiru ta musulunta ta dalilinsa ai sunan gidan su zai ƙara daraja ƙila shima a fara kiran sa da Modibbo Muntari. Da wannan ya samu ta sauko amma duk da haka sai da ta ce ya rage shiga harkanta.
A wajen Nkiru kuwa ganin Muntari ta ke a matsayin mutum mai barkwanci shiyasa ba ta taɓa damuwa da zuwansa wajenta ba ko kuma yawan tsaraba da ya ke kawo ma ta idan ya zo.
Shi kam Muntari sai da ya je wajen malamai É—ai-É—ai har uku aka tabbatar ma sa zai iya auren Nkiru dan haka ya zage damtse yana ta buga-buga, burin shi nan da shekara É—aya zai siyi gida a Kano ya auri Nkiru su dawo Kano tare, ko ta musulunta ko ba ta musulunta ba ba ruwansa ba ne wannan, shi dai ya ga Nkiru kuma yana son ta ko a yaya ta ke.
A hankali Nkiru ta fara sabawa da rashin T J ta kuma zage tana koyon Hausa da Fulatanci. So ta ke ta impressing T J idan ya dawo, malamai 'yan uwanta musamman Mr Kabir da Malam Abdullahi su su ke taimaka ma ta take koyo dan har littafi ta ke da shi na darasi.
A gida kuwa tun ana magana akan zaman Nkiru a gidan har aka zo aka saba aka ma dena maganar, har idan ba a ji É—uriyar ta ba za a fara faÉ—in 'BoÉ—É—iyon Hamma na nan kuwa?'
Idan tana maimaita kalmomin da ta koya na fulatanci kuwa Goggo da Yadikko su na shan dariya, wani lokaci su gyara ma ta ta fahimta ko da ba Pendo ko Yakubu wani shima da ya ke ɗan jin turanci a gidan da zai ƙara ma ta bayani da turanci.
A zamanta kuwa ta lura akwai wata mata wacce kamannin Muntari ta ke da shi shiyasa ta É—auka mahaifiyar sa ce, matar ba ta son ta ko kaÉ—an da ta ganta za ta fara tsuke fiska tana yare. Idan ta gaidata da Fulatanci ko Hausa kuwa sai ta kama masifa hakan ya sa ta dena gaisheta. Kwatsam ranan su na hira da Pendo ta ke cewa Maman T J wato Goggo kenan ta fi Maman Muntari kirki. Pendo ta kwashe da dariya ta ce ai T J da Muntari mamansu É—aya ne kawai dai T J ya girma a hannun Goggo ne. Abun ya ba wa Nkiru mamaki...
***
Lokacin da T J ya tafi wata uku da sati uku ya rage T J ya gama bautar ƙasar sa amma haka ya dinga ganin kwanakin nan kamar ba sa tafiya. Ba ranan Allah da za ta fito da ba zai wuni da Nkiru a ransa ba. Tun da ya ba wa Eze labari kuwa Eze ya samu abun tsokanar shi yana cewa ya faɗa soyayya. Shi dai bai gaskata hakan ba ya dai san yana jin tausayinta.
A wani weekend me ya sa Eze ya rakashi ƙauyen su Nkiru inda su ka bibiyi labarin Uncle Udodiri. Da ke Eze ma igbo ne ba su sha wahalar samun information ba. Augustus Udodiri ya koma Owerri da zama bayan ya yiwa Yayan sa da matar sa burial na gani na faɗa a ƙauyen. Har shanu biyu aka kashe a wajen burial ɗin abinda ba a taɓa yi ba a ƙauyen na su. Da su ka tambayi maganar 'yar Patrick da Caroline cewa aka yi ta gudu saboda kunyan kashe iyayenta da ta yi. Wasu kuwa sun ce ma ta mutu ne.
Haka dai su ka bar ƙauyen cike da jimamin wannan Al'amari, sun so haɗuwa da Elizabeth amma kuma ance ta tafi wani church program a Enugu...
Tunda su ka ci wata biyu T J ya fara lissafin kwanaki. Kwanakin na matsowa yana ƙara fargaban abinda zai tarar idan ya je gida. Tsoron sa kar Nkiru ta koma mu'amala da Okafor duk da ya hanata, kai koma ba Okafor ba wani ɗan uwanta christain ɗin. Idan ya tuna haka duk sai ya ji ran sa ya jagule. A haka dai kwanakin su ka cigaba da tafiya.
***
Yau ma kamar kullum kitso ta zo gidan su Okafor, su na da shago nan dukkan su ke zama har da Mama Okafor sai dai ranan sunday ba sa zuwa. Ita kuwa Mama Okafor dama tana dawowa da wuri irin 4-5pm ɗin nan. Ko da ta je gidan babu kowa sai Okafor, shima fita zai yi lokacin da ta zo. Sai ya ma ta ƙarya akan ta shiga ciki Maman sa ta je maƙota ne za ta dawo yanzu, ba ta kawo komai a ranta ba ta shige ciki, shi kuwa yana shiga ya kulle ƙofa da key. Bayan ta zauna ne ya fara tambayarta akan dalilin da ya sa ta ke gudunsa ta ce ma sa ba komai. Ya ce ƙarya ne ya lura ko gida ya je ya aika a kirata sai ta sa a ce ma sa ba ta nan.
"Kina tunanin T J yana son ki ne? Ko kuma kina tunanin su za su fi mu son ki?. Barin gaya miki abu ɗaya ki ji, T J da ki ke gani ba zai taɓa son ki ba..."
"Zan je gida, idan Mama ta dawo ka gaisheta" ta faɗa tana miƙewa tsaye saboda yadda maganar sa ta fara karya ma ta zuciya.
Shima miƙewa tsaye ya yi ya matso kusa da ita ya dafa kafaɗarta ya ce "Nkiruka ki tsaya tukunna. Give me a chance, ina son ki, zan kula da ke sosai, idan ki ka amince da ni za ki ji daɗi. Ba zan taɓa goranta miki ba infact duk lokacin da mu ka tashi zuwa ƙauyen mu a Enugu zan raka ki mu je na ku ƙauyen"