← Book details Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 99 OF 141

Sashe 99

Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Malan dake runfarsa yana ta siye da siyarwa tunda yan matan nan suka biyo zasu wuce gida ya loda musu kayan miya yace a je a rangada dan wake a more ya ci gaba da saide saidensa da nufin kusan magariba ya isa gida ne ya samu baki, bakin kuwa ba kowa bane sai Anas da mahaifiyarsa, inda mahaifiyar ta Anas ta roke shi cewar ya kawo ta wajen Malan Akoy maganar da take so su yi, bayan ya zo mata da abinda ya faru yau, zuciyarta ta yi kulewar da baki bai isa ya warware ba, ta ce da shi ya shirya su je ta kara bada hakurin itama, sannan tace da shi su fara biyowa ta wajen Malan zata yi magana da shi mai mahimmanci, inda ya ji dadi a ransa domin shi ya sanar mata kawai a yi maganar aurensa da Nur a gama , shiKenan ya ci gaba da aikinsa a nutse ne, bai san abinda zata fada ba, ya dai san cewar maganar auren ne zata kawota har wajen Malan ....dan haka ya ji sanyi a ransa, dama ya sanar mata maganar ne dan shi ba abinda yake boyewa mahaifiyarsa, komai sau ya sanar mata bale abinda ya shafi aikinsa, baya wasa da shi ɗan kulun cikin nema masa taimakon ya kara girkuwa a zuciyar ogansa take , yanzun ma ya fada mata ne dan a masa wanda zai wuce Aliyu a zuciyar ogan nasa, shine tace zata je ta sake ba Anna hakuri da kanta Ama kafin nan sai sun je ta ga Malan, wato mahaifin su HALLAH!.

Kwarai Malan yayi mamakin ganinsu a wajen sana'arsa, da mutuntawa ya ce" A'a, sanunku da zuwa, Ama Anas ai da sai ku karasa gidan a yiwa maman naka shinfida idan ya so sai a kirawoni, Ama a nan ka ga ai ba za'a tarbi bako a nan ba, ku mu je cen din sai in karaso ni ma" ya karashe yana ta yagar baki irin fara'ar nan ta tarban bako

Maman Anas ta dubi Anas ta ce" Ka je mota in yi magana da shi, ba sai mun karasa cen ba, ka je ina zuwa"

Fuskar mahaifiyarsa ya bi da kallo, cike da tunanin kamar yannayinta yannayin da take yi ne idan zata yi fada ko magana mai tsauri.........,
Dan haka a tausashe ya ce" Mama, mu karasa gidan mana ko? Kin ga dama nace maki nan din da wahala ku yi firar nan a tsanake ?"

Rai bace ta ce" Yanzun ma musun zaka min? Nace yanzun ma musun zaka yi da Ni????"

Sai kuma ta dubi Malan tana kama habar hijabinta ta shiga share hawaye ta ce" Malan, ban zo nan dan in maka rashin kunya ba, ko wani abin, sai dan in rokeka ka min arziki ka min maganin abinda yake nema ya fi karfina"

A rikice Anas ya ce" Mama? Dan Allah ki yi hakuri kar ki daga min hankali"

Da wani bacin ran ta ce" Idan ka kuma budar baki ka min magana in ba Ni na baka dama ba, sai na tsinewa maganar soyayarka da yarinyar nan!"

A hankali Malan ya furta" Subahanalah" sannan ya shiga waige dan kar mutane su tarun masa a wajen, domin ta fara daga murya, a tausashe ya ce" Ki yi hakuri Hajiya, ku je zan zo gidan naku"

Kai mama ta girgiza tana hawayenta ta ce" Ka yi hakuri, abinda yasa nake baka hakuri saboda na san zaka min adalci Malan, kai dai ka san menene rike gida saboda a cikinsa kake, to ka ga da uban yaran nan ya rasu, Ni nake ta fama da abina har aka kawo lokacin da ya samu rufin asirin nan wato aikin nan, .....sai dai a kwanakin nan, ko in ce a shekarar nan ya hadu da jarabawa ta soyayya wace ta sa tunda nake bamu taba musu da shi ba dai a kanta"

Ta kara dubansa ta ce" Malan, ban san yarona da yi min musu ba, ban san shi da kiyewa abinda na tsara ba, abinda na yanke shi muke yi da d'ana, Ama a kan yarinyar nan ya nuna min ba zai yiwu ba, karshe ma yau ta ce masa ya kai su wajen wasu samari , har ogansa ya kama su a cen, in ba Anas ba, ka san motar da kake aiki da ita in ina ka shiga da ita za'a sanar da oganka, shi ne ya yiwa budurwa biyayya ya kai ta wajen wasu samarin da har ogansa ya kama su a cen, maganar da nake maka a yanzu bamu san makomar aikinsa ba, sai yadda ta yiwu da shi, Ama shi ne dan rashin sanin ciwon kai yaron nan yake duban idannuwana yace da Ni wai a yi a masa aure da ita hankalinsa ya kwonta???????, to Malan ka yi hakuri Ama ko asiri ta masa Walahi karya take yi, domin yan matan yanzu babu abinda ya gagare su, Ama yarona kam Walahi sai dai ta yi hakuri da shi ɗan ba zan taba yarda da wannan abin ba, da farko na masa alkawarin idan ya auri A'isha sai in yarda a yi da ita yarinyar nan, Ama a irin take takensa ina mai rantse maka a yanzu da wahala in kuma amincewa ya auri yarinyar nan, sai dai ya auri A'isha ita kadai, ita ce daidai da shi!"

Ta karashe a zazafe tana sake sakarwa Anas harara sannan ta dubi Malan da yayi sokoko kamar kazar da kwai ya fashe mata a ciki hankalinsa a mugun tashe ta ce" Ni dai ban zo dan in maka rashin kunya ba, shi yasa na zo nan, saboda matanka jahilai ne ba zan je inda suke ba su zage ni, Malan in fa ana so in yarda d'ana ya auri yarinyar nan sai an yi mata magana ta daina shiga hurumin aikin yarona, ta daina saka yarona yana kai ta wajen wasu mazan, ta daina saka shi yana bijire min, ta bashi lafiya ya auri A'isha sannan ya aureta, ba zan kiya ba, ama ta bari ya fara auren dai-dai da shi ba ita ba, in ya so ta kwada shi ta cinye bayan auren, Ama yanzu kam ba zan taba yarda tsayayyen d'ana mai kula da Ni da ahalina ba a mayar min da shi shashasha ta yadda soyayyar banza soyayyar wofi zata ja har a kore shi a wajen aiki ba, Ni dai na fada maka!"

Daga haka ta juya, fuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuu bata tsaya ta kuma bi ta kan ANAS da hannayensa bibiyu ke saman kansa ba , da irin firgicin dake saman fuskarsa ba, ta bude motar ta shige sai girgiza take yi !

A rikice Anas ya karasa gaban Aban yara da ya kasa daga idnanuwansa saboda abinda yake gudun ya faru domin matan dake zuwa siyan yan kayan miyar magariba masu daren tuwo du sun tsaya da mamaki suna kallon abinda yake faruwa....., ya duka a rikice ya ce" Aba dan Allah dan Allah ka yi hakuri, aba ka yi hakuri, hankalinta ne ya tashi fa, kuma na fada mata ba zan taba iya auren A'isha ba, ai a zuciyata A'isha haramun dina ce tunda Y'ar uwar Nur ce, Malan dan Allah ka yi hakuri ka yi hakuri, dan ba kai ka haifi A'isha ba ba zai taba zamowa dalilin da Ni Anas zan aureta ba....."

Wata zabura Malan yayi yana kai hannunsa saman kirjinsa da ya buga masa da karfin gaske, A'isha? Wai dama A'isha take nufi? Wai dama bayan wannan cin mutuncin harda tonon sililin abinda dam bai sakawa zuciyarsa ba dan ma kar ya saka shi a halin tashin hankali da tunani marar anfani , ashe ashe shi ne aka masa yamadidin nan a bainar nasi???

Ai kuwa du Wanda ke wajen ya kuma san su waye A'isha da nur sai aka shiga kallon kallo

Kirjin Malam ya rike masa, a hankali ya juya ba tare da ya iya bi ta kan runfarsa ba bale har ya iya tattara cinikinsa ya adana Kayan siyarwar ya rufe ba, idannuwansa na neman rufewa, hakan ya sa ya shiga neman hanyar gidansa zufa na keto masa.......

Dama Malan, mutun ne da sam baya son tashin hankali

A kwanakin nan kuwa, babu kalar wanda bai gani ba da ya hade ya hade masa a cen karkashin zuciya ya daskare.................

A hankali yake dafa garun soron gidansa , har ya kai hannunsa wajen iska a tunaninsa ya kai kan garun ne ya dafa, sai kawai hannun ya tafi a iska shi ma ya silale gaba dayansa ya fada kan...........

😍😍😍😍😍😍😍🥹🥹🥹🥹🥹🥹🥹🥹🥹🥹🥹🥹

Page 58.59 and 60Kisan mummuke page 61......62

A hankali yake dafa garun soron gidansa, yaron dake biye da shi wanda zai yi shekarun sulaimana kuma yaron wani makocinsu ne da suka zauna tare kafin ya SIYAR da nasa gidan ya tashi, sanadiyar wannan mahaifinsa ya saka shi a hanyar kasuwanci saboda kudin da suka yankawa gidansu ba kadan bane kuma aka basu, yayi silar samun dukiyarsa mai dan kaurin da ta sa a yanzu yake da matirkilinsa harda motarsa ta hawa, yanzun ma ziyarar da yakan kawowa anguwar ce ya kawo, ya tarar da abinda yake faruwa, kuma shi ya rufe kofar rumfar Malan da sauri ya biyo bayansa , ya zamo a kan idannuwansa Malan ya dafa iska ya fadi ne ya bude baki da dan karfin amon murya ya ce" Subahanalah, Malan, Malan.....??????"

Kasantuwar Auntyn yara da yan matanta suna filin gida sunna nashin dan wake ne suka jiyo wannan lamari, hakan ya sa kusan a tare suke kokarin nufar soron saboda muryarsa kwarai ta tabbatar musu ba lafiya ba....

Auntynsu ce kawai ta iya wartar hijabinta a jikin igiya ta zuluma ta nufo soron a lokacin da Nur ke ihu ta nufi inda bawan Allahn nan ya kama Aban yara yana ta kama sunansa da kokarin talaba shi

Gabanta ya yanke ya fadi, a tsayen da take kawai sai kaffafuwanta suka dauki rawa, lokaci daya ita ma ta nemi fita hayacinta, du irin yadda take da jarumta sai kawai gawar tsohon mijinta ta fado mata a rai, hakan ya sa jikinta ke rawa, kuma ta kasa katabus tsabar tsoro da shiga firgici.....
Chapter 99 · 0% Book details