← Book details Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 141

Sashe 31

Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A tare suka ringa amsawa, sannan suka shiga bata hakuri

Anna ta dauke kai ta ce" Ku tashi ku tafi"

Mikewa suka yi a tare har sunna gaggawar fita, Anna ta ce" HALLAH ! Zo nan"

Dakatawa ta yi kirjinta na bugawa ta dawo a raunane ta duka gaban anna

Anna ta dube ta ta ce" Shekarun ki nawa yanzu?"

IMTEE ta dago a raunane tana cika idannuwanta da hawaye

Anna ta ce" Ba kuka nace ki min ba, amsa min"

A raunane IMTEE ta ce" Auntyn yara tace na kai 19, mama kuwa tace sha takwas ne wai!"

Anna ta Dube ta da dan mamaki ta ce" To auntyn yaran ita ta haife ki da zata fi mamanki sanin age din ki?.; Bama wannan ba ke baki san shekarunki ba? HALLAH bana so raina ya ɓaci"

A raunane ta ce" Ki yi hakuri Anna, a takardar haihuwa a shekara ta 2006 ne, kuma auntyn yaran itace ta haife ni wai....m, mama kuwa a wajen ta nake"

FARHANA ta dubeta ta ce" To wai din baki yarda ba kenan ko wayo zaki rainawa Anna ??"

HALLAH ta sakar mata harara ta ce" Kin ga dai ban shiga harkarki ba!"

Anna ta dauke dubanta a tausashe ta ce" baki ji ciwo a kirjin ba?, bude in gani ko kya ga likita???"

HALLAH ta zarro ido tana dan dafe kirji ta ce" Ai Anna na daku kam, ama ba sai kowa ya gani ba zan sha ciwo bakwai idan na je gida"

Anna ta yi murmushin ganin yada take wani sasada kai, kafin ta ce" To maza gida, saura in ji kin biye mata ko a anguwa ne, sai ranki ya bace"

HALLAH ta mike tana godiya kafin ta fita

FARHANA ta girgiza kai ta ce" Ban san me yasa kike ji a ranki kina iya son yarinyar nan kamar Ni ba Anna, Ama ina mai tabbatar maki kin fi so na da ita sosai da sosai, wannan da mai Zubin munafukai ce, ki daina yarda da ita, Bakya ganin yannayinta irin munafukan nan ne???"

Agogon dake hannunsa ya duba a hankali ya yi dan gyaran murya

Anna ce ta mike da sauri tana furta" Ya rab, habiby, kana online dama? Ya Allah "

FARHANA kam ta mike da sauri ta yi bayi a ranta tana ayyana ' munafukan da yawa ne a zagaye da Anna, Allah ka rufa min asiri in iya bakina kar a yi shiru a ji na aikata abinda zai bada damar a ci zalina"

Murmushi ya sakarwa Anna yana dubanta a tausashe ya ce" Oumi......, bana jin in zan iya kyaleki a cikin rigimar yaran makarantar nan idan na dawo......"

Anna ta yi yar dariya ta ce" Ba komai fa, Ni wannan din shi ke sakani nishadi, du yaron duniya ai baya ji, sai ana hakuri ana fada ana tarowa, Allah ya shirya mana su"

Murmushi ya yi ya ce" Zan fita, sai na kira"

Anna ta ce" Ok, by Habiby, Allah ya tsare"

Da amen ya amsa kafin ya kashe call din gaba daya ya dan jinginar da bayansa yana tunanin nan da kwana biyar in sha Allah yana gida, yana kusa da Anna, da Mama, and kakarsa .........ya rab shi kadai ya san irin yadda yake missing din su....., shi yasa Bama zai sanar musu cewar zai zo ba, idan ya zo sa hadu.

Su IMTEE kuwa cikin gaggawa suka fita suka dauki hanyar gida saboda abinda ya faru jiya ba zasu so ya sake faruwa ba

Sai da suka kusa isa gidan Yaya Anas ya cin musu, yannayinsa na nunin tashin hankalin da yake ciki

IMTEE sam ta ki tsayawa bale har ta bashi wata fuska, A'isha ce ma ta ɗan dakata a gurguje ta ce" Yaya Anas ka yi hakuri idan aka gan mu tsaye da namiji ran abanmu zai bace ka yi hakuri"

A hankali ya ce" A'isha, dan Allah ki bata hakuri ya saurareni...."

IMTEE ta juyo tana jin ranta na neman sake bacewa ta ce" Babu wani sauraronka da zan kuma yi, ka je ka fada mata Walahi ta cira bata nuna ba, kuma ka fada mata Ni namiji bai isa in bi shi ba, ko waye shi!"

Daga haka ta yi cikin gidan su ko Salama bata yi ba ta nufi dakin mama, sai dai tana zuwa ta ga a rufe, haka kawai ta ji kafafuwanta sun nufar da ita dakin auntyn yara wace ke bakin murhu tana fifita wuta

Shiru ta yi kirjinta na dokawa da wani irin farin ciki, duda ta kula hankalin yarinyar sama sama kamar ranta a bace haka, Ama da idannuwanta a gidan nan an taba yin lokacin da Imtee ta ringa ihu dan an ce ta shiga dakin aunty amarya saboda mama ta fita kuma lokacin damina ruwa ya sauko, ga dare ya yi, haushi ya sa sulaimana yi mata dukan tsiya ama yarinyar nan sai mahaifinta ya kai ta dakin soro shi kuwa yayi jiran maman nata a soro har ta zo sannan ta tashe ta suka je dakinta...., a daren nan auntyn yara rintsa ido gagararta yayi, ta ci kuka kamar ba gobe da kyar ta iya rarashin kanta ta yi hakuri dan bata da yadda zata yi....

Shigowa A'isha ya sa ta mike tana dubanta a sanyaye ta ce" A'isha, Nur dakina ta shiga, da kanta A'isha, ban matsa mata ba da kanta ta shiga, A'isha ta gane cewar ba zan kasheta ba ko? Ko A'isha??????"

Sai kawai hawaye ya shiga bin gefen fuskar auntyn yara

Wani irin tausayin auntyn yara ya kama zuciyar A'isha fiye da da

Duda a tsorace aishan take da irin yadda suka kwashe da mahaifiyarta a jiya bai hana ta rike hannayen aunty amarya kasa kasa sosai ta ce" Aunty, ki daina kuka, mahakurci mawadaci...., ki ci gaba da yi mata uzuri aunty.....Walahi ba a hankalinta take yi maki wasu abubuwan na, laifin mam..........."

Ta yi shiru , a hankali ta sada kanta kuka na son kubce mata ta ce" Ban san me zan ce ba, mahaifiyata ce aunty, ban san me zan iya fada ba, abinda na sani shi ne kwakwaluwar Nur a hautsine take da rikicin soyayyar da ta kasa bambance fara ce ko baka, Ni ban san wace irin soyayya ce wannan ba, Ama Ni na gane cewar akoy kulalaliya a cikin ta......, sam ba haka ya dace ace....ace....ace........"

Sai kuma ta yi sauri waigawa tana sakin hannun auntyn yara kasa kasa ta ce" Allah na madakata, ba zai bari ki tagayara ba, Aunty Malan yace gaskiya itace ba'a iya kurewa.....ki yi ta hakuri, ina sane da komai da kike ciki"

Wani irin mamaki ya gama kama aunty, wani irin sanyi ya idasa mamaye zuciyarta, lokaci daya kuzari ya sake kama jikinta, karfi ya shige ta, zuciyarta ta saku da zafin da ta riketa............., a hankali ta samu kanta da komawa wajen murhun nan ta zauna yana share hawayenta kafin ta saki murmushi a hankali ta furta" ashe ana ganin abinda nake ciki? Ashe hakuri na ne ke son gazawa? Ashe idan na kara jajircewa da addu'a da hakuri, da kokarin kwato y'ancina za'a iya wayar gari in ga haske a lamarin? Ya Allah ka tsare min Nur, ka kare ta, ka tsare A'isha ka yi musu albarka, Ubangiji ka shiryar da Sulaimana, ka shiryar da baban gida"...................

Da yammacin ranar nan daga kanti Malan ya dauki sulaimana suka shige adaidaita suka nufi kauyen su Malam din, wato Magarya

Kwarai sulaimana ke tunanin me zasu je yi? , sai dai Malan bai bashi damar tambaya ba har sai da suka sauka a gidan abokinsa, baban malamin alo, mutun mai nagarta da kiyaye dokokin Allah

Bayan ya marabace su da mamakin ganin su a irin lokacin nan suka zauna aka kawo musu ruwa harma matarsa ta shiga dama musu fura , wato suka dan huta da tafiyar mai dan tsayi dan a kadan ana yin awa uku a hanya idan ba Babar mota bace...............

Da kula baban yara ya ce" Malan Ya rayuwa ya kasuwa ya kiwo"

Malan ya yi murmushi ya ce" Alhamdulilah malan Adamu, komai na tafiya cikin aminci da ikon Allah, ya gida ya yara, ya ciwulwutar rayuwa kuma?"

Baban yara ya furta" Alhamdulilah"

Sai kuma shiru ya wanzu a wajen na dan lokaci kafin baban yara ya dubi abokinsa a hankali, cike da fuska mai dauke da jimami, tare da tarin tashin hankalin dake zuciyarsa wanda ya Hanna shi rintsawa tun daren jiya ya ce" Malan, na san zaka yi tunanin ko lafiya ka ganmu haka ko??"

Malam yayi murmushi yana sake bashi hankalinsa ya ce" A kowani lokaci ka nufo nan wajen zuwan ka ne, kwari kai din ka zama dan uwa Malan, ina fata kana lafiya dai"

Baban yara ya fitar da huci a nutse ya ce" eh to....., na rasa ina zan nufa da tarin tashin hankalin nan, sai kawai na yo nan, domin hankalina ya kasa dauka......"

Ya nuna Sulaimana da ya yi tsuru tsuru yana dubansu da tunanin to mi aka yi kuma??? Ya ce" Ga dai yaronka nan, ka ganshi nan a gaban ka, rashin jin magana kala kala muna cikin su sai godiyar Allah, ka san bayan zama cikin bata gari da ya riga ya zama shima bata garin, har yan kwayoyi Sulaimana ke afawa idan ransa ya bace ko idan yana cikin nishadi......, to dai ta yiwu abin ya kai ga taba kwakwaluwa ko yaya? Ni dai abinda ya sa na nufo nan dan ka dubi yaron nan, ka gane min, idan har abin asibiti ne in kai shi, in kuwa abin na alo ne ka daure shi, dan kuwa Ni yanzu bana iya bari sulaimana ya shiga cikin gidana da zuciya daya, sakamakon abinda na ji yana fadawa amininsa a jiya da magariba"

Gaban sulaimana sai da ya yanke ya fadi, ya kame haba ya furta" Innalilahi wa Inna ilaihi raj'une, Ama kuma kace ba abinda ka ji. Abanmu....., Ama Fisabililahi nima ai da na fada cewa na yi ina jin na haukace, shiKenan kuma sai ka tona min asiri"

Aban yara ya daga hannu ya ce"*JAMA'A NAZOMUKU DAWANI TSARI NASAMUN KUDI TA HANYAR AMFANI DA WAYAN HANNUNKU
WANNAN TSARIN SHINE METAFORCE

MENENE KASUWANCIN METAFORCE* ????
Chapter 31 · 0% Book details