← Book details Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 141

Sashe 45

Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kai ta girgiza a hankali ta ce" To ai idan yaya ne yace ka min wannan wasan shi ya san wanda nake so........, ya fi kowa sanin wanda nake so,..........ko ya zata na sauka daga ra'ayina ne?, ina nan a kan ra'ayina, kuma ya min alkawarin ba zai min dole da kowa ba, haka kuma ba zai taba take abinda ita wancen take so ba ko?????, to ai ita kakarsa ta haramta mana auren Yaren da ba namu ba, ka ga a nan ma ba wannan maganar sai dai in tana nufin Yaren da ba namu ba banda mai kudi........"

Sai kuma ta yi yar dariya a hankali ta ce" Yaya, i'm sry plz, na zarce da maganganu......., bari in sanar a zo a kawo, ka huta lafiya"

Daga haka ta juya da dan sauri ta nufi bangaren su,

Tana shiga ta samu IMAD zaune daf da mama ya rike hannayen ta da kyau , fira suke yi , wace dama ta san a kala sa dauki lokaci kafin su gama irin firar nan, koma tace ba zasu taba gama irin firar nan ba saboda kullum ta Allah sai sun yi zama irin wannan daga shi sai ita

Tsayinta ta rage , muryarta da alamun raunanawa sosai ta ce" Anna, sun farka"

Anna dake duban IMAD ce ta dubeta da sauri saboda amon muryarta ya cenza sosai

Mikewa FARHANA ta yi da sauri zata nufi elevator

Anna ta ce" Ina zaki je kuma baki ja an kai musu da ke ba???"

Da dan gagawa ta ce" Anna bayi zan shiga cikina ke ciwo"

Sai kuma ta wuce da sauri ta shige elevator din ya hayar da ita sama ta fito a hankali ta nufi hanyar ne ta hade da su MAZNA da kannenta sunna tsaye sunna fira........

Du irin yadda ta so tsokanar MAZNA da abinda ya faru ita fa Ina, sai kawai ta share ta nufi dakin Anna ta bude ta shige , sannan ta rufo harda murda ky ta karasa ta zauna saman kujerar dake gaban mirror a hankali ta zubawa fuskarta ido........

Da mutuncinta, da girmama manyan ta, da kare mutuncin ahalinta ta taso........
Muguwar akida, mugun riko, ya sa ta biyo ya tsarin ahalinsu wanda ake hana mutun auren wanda yake so, har aka ja mata layi irin wannan aka hanata mu'amalantar wanda zuciyarta ta aminta da shi..........gashi yanzu zuciyar kanta bata san ina take a cikin kirjinta ba...........

Shine za'a sa yaya Mutalab ya yi mata magana irin wannan? Dan kawai bata da karfi bata da wani iko?........

shiKenan ai, ta sani bata da wani karfin ja da wanda Hajiya ta sako a cikin lamarin, shi kuwa tunda ya kasa karantar ta har ya gane halin da take ciki ya tallafa mata a da, shiKenan ai sai ta yi ta zama a gabansa dan kuwa ta rantse a yanzu auren ma ba zata yi ba, to mema zata kai a gidan auren ne? Tana ji tana gani yau da gobe da zama da saurayinta sai da suka ringa sasabawa fiye da kima..........., to ita idan ta yi aure ta kai me gidan auren???????, hum.

MAZNA kuwa tsaki ta ja bayan FARHANA ta nufi dakin Anna, ta dubi JAUHARA ta ce" kun gyara dakunanku jiya ne?"

Jauhara ta ce" Eh Ni na gyara nawa da safe"

MAZNA ta nufi dakin tana fadin" Bari in je in kwonta dan a gajiye nake, ya zo kenan barcin safe zai gagari mutum, hum Ni dai wallahi du Ni aka kwara da wannan tsare tsaren"

A falon kasa bayan FARHANA ta haye Anna ta maido dubanta kan IMAD tana fitar da ajiyar zuciya a hankali ta ce" Yadda ka tsara za'a yi, du abinda kake gani , Ama kamar yadda na fara yi maka maganar harkar kudin makarantar nan shine nake so in idasa maka..........."

Ta sauke ajiyar zuciya tana dan kallon kasa a hankali ta ce" Ka ga wajen nan, na ga kokarin iyayen da suka dage suka saka ƴaƴansu a makaranta irin tamu, saboda ta zo musu da diyar kudi wanda basu san shi a da ba a harkar makarantar islamiyya, duda ba wani abu ne mai yawa ba, Ama sun yi kokari ainun......., A yanzu da ake shirin mayar da ita haka, zan so ace mun yi musu wani kokarin da zasu ci gaba da samun kwarin gwuiwar turo ƴaƴansu a makarantar......., idan har hakan ba zai zamo takura a wajenka ba"

Murmushi yayi sosai yana sake riƙe hannayen Anna a nasa , kwarai yannayin firar tasu ta cenza salo tunda Farhana ta shige, ya san cewa Babar damuwar mahaifiyarsa na tare da ta kanwarsa ne....., shi din ma Babar damuwarsa a yanzu kam Farhana ce, sai dai baban dalilin dawowarsa gida saboda Farhana ne...., yana sakawa ransa in sha Allah zai yi maganin damuwar nan, ya zo ne da nufin bata abinda take so, kuma in sha Allah zai yi maganin abin ta hanyar fara nunawa Inna illar rashin amincewar ta sannan ya nuna mata halaccin abin, idan ya so sai a zauna a hada shiKenan hankalin kowa ya kwonta.

A tausashe ya ce" Inace maganar nan zamu yi ta daga baya Ummi, du abinda kika tsara za'a yi da harkar makarantar nan......, makarantar ki ce, idan kika ce kyauta za'a yi in sha Allah Allah ba zai hana min yadda zan kular maki da malaman ki da komai ba..........., now tl me abt U, UMMI yaya na barki da fitintinun rayuwa, yaya kika rayu da Inna? Yaya kika rayu da su MAZNA.......Ummi yaya kika rayu da FARHANA????"

Anna ta ja wani numfashin da bata shiryawa janshi ba, sai dai tambayoyin da ya jero mata ba tare da nuna gajiyawarsa wajen yin su na suka sauka a daidai inda ya fi mata kaikayi har suka tabo cen cikin zuciyarta......., sai dai me zata iya budar baki tace a matsayin amsa a yanzu a gabansa???? Wa zata ce ya yi mata ko bai yi mata ba??, Inna uwa ce a wajen ta, shin tana nufin ba zata iya hakuri da abinda Inna ke yi mata a rayuwa dan ba ita ta haifeta ba? Ai ko bata haifi mahaifin yaranta ba ta dauki shekarun da dole a duka mata a kuma yi hakuri da ita, koda Inna bata kai shekarun da a yanzu ta kaba gabar rigimar da fitinar ce kawai aikin yi ta dauki shekarun girman da dole za'a mutunta ta, Inna ai uwa ce, ja gaba ce, sanyin idanniwa ce, Inna ce za'a yiwa biyayya koda ba'a so ga dan kirki wanda baya son Allah ya hadu da shi.........

Bayan Inna, laifin wa zata fada? Na MAZNA zata fada? Shin zata fito ne tace da shi ga irin abinda take gani a tare da matarsa wace tunda aka yi auren ma dama bata nuna ta amshi tayin son zama uwa a gare su ita da kannenta ba? Ko kuma nuna masa zata yi cewar matarsa baya mutuntata bata darajata bata dauketa a bakin komai ba, tana yi mata abinda ko sa'anta ba zata iya yiwa haka ba.......? Ta ina zata fara fuskantar d'anta da ta sani ciki da bai ta yi masa maganganu irin wadinan? To ai tana da yakinin a yanzu a nan zai iya Salama aurensa dake tare da yarinyar nan kuma yayi mata rabuwa ta har abada daga ita har kannanta bayan ita ba haka yake so ba, tana so yarinyar da kanta ta gane cewar abinda take yi ba dai-dai bane harma ta gyara mu'amalarsu.......

Zata so ace sun samu ladan rikon kannenta da ita din kanta tsakani da Allah ta yadda zasu ci ribar hakan gobe kiyama,

To idan bata yi hakuri ta kawar da kanta ba , in ga fada masa komai ya lalace ya watse ina ribar take ne???????, uhum

Farhana............

Me zata ce a kan FARHANA???????

Lamarin Farhana na gigitata fiye da tunanin bawa

Farhana ce daya jal y'arta mace kamar yadda yake namiji

Ta ga kyan nasa saboda a yanzu matakin da ya taka koda jarabtar Ubangiji ya samu a gare shi na rasa komai tana da yakinin tawakalinsa zai sa ya fuskanci rayuwa ya ci gaba da kaiwa Allah kukansa...................

Sai dai Farhana fa?

Farhana tana cikin launin al'ummar dake daukan abu a zuciya da zuciya harma ta yi riko ta yiwa kura mayar da aniyarta .

Farhana ce ke duban idannuwan Inna ta fadi abinda ita da kanta mahaifiyarta sai ta Tsorata, Farhana ce ta yi iya yinta har sai da ta zamo abokiyar gabar Inna ya zamo ina na kiranta mai dati mai Dauda wace ke yawon ta zubar.......
Farhana fa bata shiri da MAZNA ko kadan

Farhana bata girmama kowa a gidan nan, idan ka yi iya yinka kuna ganewa junna to, idan ka yarda ta tsane ka komai girman ka ba zata girmamaka ba sai yadda hali ya bada.....

To wai ita yanzu ta dubi lamarin farhana ma tace me??????????

Duban fuskar mahaifiyarsa yake yi, zuciyarsa na son daukan nauyi da tunanin shiKenan abinda yake ta fargabar ne ya faru da ita, wato sun hadu sun daga mata hankali gaba dayansu????

"UMMI, wa da wa ya bata maki da bana nan? Fada min" ya fada a tausashe yana sake riƙe hannayen ta

Anna ta sauke idannuwanta a kan fuskarsa, irin yadda ya hade rai yanzu sai da ta ji wani sanyi na sake ratsa mata zuciya.....

To ita kuwa meye ma zai daga mata hankali idan yana nan????

Wannan fa shine wanda yake iya tarbar duk wani abin da ya tarbota koda kuwa ya fi karfinsa......

Tun yana yaro ya nuna cewar ya karbi girman daukan hawayenta a tafukan hannayensa
Chapter 45 · 0% Book details