← Book details Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 141

Sashe 55

Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sokoko yayi yana kallon ta ta bude motar ta shige tana kada kafa, sai kuma ya bada waje saboda zuwan da IMAD yayi ya budewa Anna motar kasa kasa sosai bayan ta shiga ya gyara mata abayarta ya ce" Me yasa kike so ki yi motar ki daban da tawa Anna ?"

Anna ta yi murmushi kasa kasa itama ta ce" Yaya za'a yi in hada mota da kai bayan hidimar ka daban? Kuma kace MAZNA ba zata je kampani aiki ba daga yau sai dai ta koma makaranta a bata poste, idan haka ne kafarka kafar matarka ba zan zamo a cikinku ba koda yaushe......, kawo kanka in maka addu'a, Allah ya tsare min kai....sai kun zo"

Murmushi kawai yayi yana kallon ta har motarsu ta tashi kafin ya juya ya nufi tasa motar

Anna na kallon farhana ta yi murmushi ta ce" Sai ki dago kan FARHANA mun bar gaban nasa"

FARHANA ta dago kanta tana sauke ajiyar zuciya kafin ta girgiza kai ta ce" Anna, wai baki kula ba kamar kin sangarta yaya da yawa??, ANAS wai baka kula ba kamar ta goya yaya? Ni ce autarki fa, Ama idan yana waje kamar Bakya ganina, murmushinki ma baya sauka daga fuskar ki, in fa yana nan Anna yadda kika san ki masa shagwaba Allah kuwa, Inna take cewa wai Bakya faranci da yaya, ni kuwa a da gani nake halin Inna ne marar dadi......., sai daga baya na gane wallahi Anna kamar haka din ne, Ni ce auta, Ni ce mace daya da Allah ya taimake ku ya baku a dangin nan, Ama kamar Ni ake daf da shakewa idan yana waje.....Ni kam abin nan na bani mamaki"

Anna da ta kame haba har tana daga baki ta dungure kan Farhana tana duban Anas ta ce"

33

Anna da ta kame haba har tana daga baki da mamakin Farhana ta dungure mata kai tana duban Anas dake tukinsa hankali kwonce ta ce" Ka ji ba?, ka ji yarinyar nan ko?"

Anas yayi dariya ya ce" Anna, Ni fa ta fara wankewa, wai a kan me zan yi kuka dan an bani gida daya da mota daya, maimakun in ce basu isa ba? Lallema to ai bata sani bane, in ina zata je zamu je ne kafarta kafata, zan ga wanda zai gaji da Ni ita....., a aikin oga ai ba zan taba gajiya ba"

Anna ta yi murmushi ta sake gyara zamanta tana kallon irin yadda aka yiwa garun makarantar domin har sun iso

A lokacin da su Anna suka daga, sai da suka fita daga get sannan ya juyo wajen da MAZNA ke tsaye

Ido ya zuba mata, ta sha sutura irin wace ta fi kwontar masa da hankali da tsayar da nutsuwarsa yadda yake so

Murmushi yayi kafin ya daga mata hannu, domin sai da ta shirya tsaf yace da ita sa fa, ba tare da ita zai je ba, shi yasa ma ta masa rakiya kawai

Murmushi ta yi tana kallo ya juya ya karasa ALIHU ya bude masa mota suka shige shi da Murtalab sannan ya zagaya ya shige ya tayar da motar ya ja ya fice da mugun gudu

Ajiyar zuciya ta sauke boyayiya kafin ta juya ta nufi bangaren ta tana neman layin kanwarta, wato Jauhara wace ke haukan son Mutalab ....domin gaba daya idan ba nemanta ta yi ba, Bama ta zuwa inda take, tana cen tana ta gadin ta ga ya wuce koda ba zai ga da mutun a inda take ba .....

Tana zuwa ta zauna saman kujera ta yi shiru kirjinta na bugawa da tsagwaron kaunar mijinta da baban tsoron da ya fi daga mata hankali, wato tunanin da take yi barkatai marar anfani

Bata jima ba ta same ta a dakin ta cire hijabinta tana fitar da numfashi ta ce" Aunty, gaskiya yanzu zaman gidan ki ya cika matsala....., abubuwan sun yi yawa, yanzu fa ba'a isa a yi yawo ba hijab baba ba ko a yi yawa a kowani time, Ni ba abinda ke bani tsoro irin sabon mai kula da mijinki, gaskiya muna addu'ar Allah ya sa yayi gaggawar komawa , idan ba haka ba abin ya mana yawa sosai"

MAZNA ta dubeta da idannuwanta da suka dauki launin ja kadan da kuma ruwan da suka tarun mata a ciki, a duniya bata da kawa, ko wata da ta san sirinta sama da JAUHARA....., tana yin maganar da ta wuce misali ita da JAUHARA, tun JAUHARA bata kai girman yanzu ba take tare ta da maganganun da suka shafi ita da mijinta kawai....har ya zamo JAUHARA ta gane komai har take da gudunmawa kala kala da take ba yayar Tata, idan ka ji wasu kalaman na fitowa daga bakin JAUHARA sai hankalinka ya nemi tashi, duba da budurwa ce , zaka iya tunanin wai a ina ta san abubuwan nan????????

Da yanayin tashin hankali MAZNA ta dubeta ta ce" Ina tsoron idan MINE ba budurwa yayi ba!"

Jauhara ta dube ta tana zato ido ta ce" kai, zaki fara ko? Zaki fara janyowa kanki mugun fatan ko? Fada kuka yi yake miki fushi shiKenan zaki fara tunanin wata yayi ya sa yake maki fushi bayan kin san mijinki da zuciya in dai kuka yi fada yana iya yin sati bai kula ki ba???"

MAZNA ta girgiza kai tana mikar da yar yatsarta ta ce" JAUHARA, gaba daya abin ba nan ya nufa ba, ke kin san waye mijina a fanin Sex, na sha fada maki nacinsa da abin, ke da kanki kin sha ganin irin yadda nake farkawa idan safiya ta yi a kusa da shi......shine fa yau aka wayi gari kwanansa biyar a garin nan bai nuna min komai ba, ke yanzu hakan ba suspect bane a wajenki?"

JAUHARA ta yi shiru tana kallonta kafin ta ce" gaskiya da mamaki, Ama kuma ke me yasa zaki fara tunanin mugun abu irin wannan? Idan kina nufin yayi budurwa kina tunanin yaya zai iya kwonciya da wata ba aure ko kina nufin aure yayi Anna ma bata sani ba?????"

MAZNA ta zarro ido hannunta na rawa ta ce" JAUHARA ....., abinda nake ta tsoro ne, JAUHARA kar dai aje wata balarab......."

Jauhara ta girgiza kai tana duban ta da mamaki ta ce" Lalle, kin bani mamaki aunty, ki yi hakuri amma gaskiyar kenan, wai yanzu ke maimakun hakan ya dadada maki zuciya kin ga kin gama warkewa shiKenan sai ku je zuwa shagali ko..... Kamar yadda likitanki ya fada , ya zama zaki iya ko meye hankali kwonce ba ya fi ba?...wai aunty idan ya nema din yanzu da kina nan kina ta neman wata mafitar fa?, ki fa yi tunani fa, ki cire komai daga kanki ki manta da komai, mijinki yayi sunan da ba zai yi wasa saboda mace sunansa ko na ahalinsa ya bace ba, wai idan ma baki yarda da tsoron Allansa ba kenan, , gaskiya gwara ki yi kamar ba kya ganin komai, share ki da yake yi ba fa wani abu bane kin ki ki sakarwa mahaifiyarsa jiki, Ni ban san abin nan naki ba me kike nufi....., ama kuma mai daki shi ya san inda yake masa yoyo.......kawai kema ki share a hankali komai zai koma yadda ake so kin fahimta?"

MAZNA ta zuba mata ido, kwarai hakan ya dace ace ta yi, sai dai gaba daya bata jin in har zata iya

Mikewa ta yi ta ce" Bari ki ji, to in ma menene zan bincika kuma zan sani, idan ma wata budurwa ke son dauke min hankalinsa wallahi karya take ko Y'ar uban waye , in kuma auren ne ma Ni nan ina da damar da zan batar masa da matar ya neme ta ya rasa a duniya!, na zan taba iya daukan tunanin IMAD da wata y'a a duniya ba......, ina zuwa zan kira docter, abinda yake so in fada masa ke zan fada masa yau, ta yiwu in ya ji yanayin girman mijin nawa ya gane cewar ina iya amsar mijina a yanzu, ke ko bai yarda ba Ni zan yarjewa kaina.... kwakwaluwana ba zata iya jure tunanin ko wata ke wawurar min miji ba!"

Daga haka ta yi bangaren dakinta ta bar Jauhara tsaye, baki sake tana duban hanyar da ta bi kafin ta girgiza kai ta ce " Ni ai ba auren Bama, wannan fitinar, kana tunanin da ka yi aure ka rage wasu matsalolin ama alamu sun nuna sai ka yi auren ne ma jarabar duniya zata same ka? Aunty fa bata taɓa hutawa ba baiwar Allah, in yau bata yakin neman yadda zata hana mace kallon mata miji, gobe tana na harkar kayan mata, jibi tana faman na fata, gata tana na jikinta ga Kuma sutura......ba wani abu nata da ya huta gaskiya..........hum Allah ya kyauta!"

Tana gama fada ta mike ta nufi cikin ita ma........................

Da yawa sun shiga karatu tun karfe takwas, daidai ku ne basu shiga ba irin yan ajin su NUR sai karfe goma su din ma suna zuwa suka tarar da malamin da ya shiga mai tsauri ne mai duka , gashi sun zo a latin da suka san lalle zasu karbi bulala, hakan ya sa Nur ta ɗan tsaya tana leken lokacin da A'isha ta karasa malamin ya mata alamun ta miko hannayanta....sai kawai ta zagaye ta yi baya a hankali ta nufi Library, domin a gaskiya bata zo yau dan a yi mata dukan tsiya ba, sam a yau da take baza kanshin nan ba zata so hawaye ya dame mata kwallin da aka sha kokowa wajen saka shi, da irin darzar da aunty ta sa ta yiwa jikinta da tafin kafafuwanta da akaifunta....., kai a gaskiya a yau fa, idan har aka gigitata ba'a yi mata adalci ba, shi yasa ta je bayan zuciyarta cike da tunanin idan aka tashi zata wuce ne neman Anna saboda kiri kiri ta gagara samun yin magana da abansu, gidan nasu a mugun rikice yake kwanakin nan, ba'a yin dare safiya ta waye ba'a samu wani tashin hankalin ba
Chapter 55 · 0% Book details