Sashe 71
Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A lokacin ne kuma ya bude, ya zamo sun bayyana tsamo tsamo gaban mutanen dake falo, wa'inda su auntyn yara da A'isha da mama matar Malan zaune kasa kusa da kafar IMAD tana ta kallon A'isha wace ke jikin auntyn yara an sa lalle lalle su ci abinci Ama sun kasa sakewa sama sama dai auntyn yara ke ba A'isha abincin tana kallon mahaifiyar aishar ita ma, saboda da suka sauko har zai wuce da ita Anna ta dawo da shi , domin su Malan sun fita su hudu harda Sulaimana suna cen filin gidan suna ta jajantawa da sake yiwa juna bayani ne, a dole Anna ta dawo da shi, ta nuna masa fa lalle sai an hada mama fa yarinyarta....., da farko ya nuna yana so su zauna ta samu nutsuwa ne kafin ya fada mata, sai Anna tace a wani lokaci take samun nutsuwar? Ciwon ta ai bashi da lokaci, kawai a sanar mata, cikin ikon Allah suka zauna ya ringa yi mata bayani a hankali a hankali har ya dasa Aya ya nuna mata A'isha......., sai kawai ta yi wani irin shiru, bata ce um, bata ce um'um ba ta zubawa aishar ido, ko me take ta tunani a ranta? Hakan ya sa wajen ya samu sauƙin hayaniya har ma ya dan lumshe idannuwansa sakamakon shirun da ya wanzu a wajen bayan Anna ta tambaye shi NUR? Ya kasa amsawa ne suka bayyana a gaban al'umma a lokacin da Nur ta yi maganar nan, ita kuma FARHANA dariya ta kubce mata tana zarro ido ta ce" Cizon ta kika yi? Kika cije ta? Kandalar Anna dole ma ki shiga uku a garin nan....kika cije ta?"
Sai kawai idannuwanta suka sauka a kan na jama'ar da suka zuba musu ido, wanda bayyanar su ya da A'isha mikewa da sauri ta nufi elevator din tana fadin" NUR......ina kika shiga kika barni????"
Hannu Farhana ta mika ta janyota ciki ta kuma dana da sauri jikinta na dan daukan rawa ta ce" Tunda na hadu da ke kike ja min masifa da yaya, ...........dama yana nan? Ya ji me na ce? Innalilahi wa Inna ilaihi raj'une gwara mu koma mu ci uwar juna a sama da mu sauko nan ya haɗa min jini da kwakwaluwa yace na zama yar iska a gabana aka rungume shi na lalace.........!"
Mikewa Nur ta yi tana zarro ido ta ce" Farhana maida mu zaki yi? Na gaji wallahi kar mu koma cen kin ga harda namiji kar su mana tarayya, AISHA koma daga bayana ba fada kika iya ba kar ta fara marinki, marin nan da ta min ba karamin zafi na ji ba , hannu kamar mai laushi ama ko Gatari albarka, bari in rufe fuskata kar ta lalata min fuska....yau Ni na ga jaraba A'isha boye da kyau kar abin ya maki yawa......."
A tsorace, A'isha ta budi baki a lokacin da elevator din ya sake budewa ta ce"
41
Happy weekend my peoplePage 42 ND 43
A rikice A'isha ta ce " NUR, ki rufa min asiri, abin ya min yawa, NUR yaya zan iya da maganar fada kuma?, wa kika janyo fada? Innalilahi, wai meye wannan muke ciki kaina juyawa yake yi, NUR kina ganin mahaifiyata? Kin ga mahaifina? Nur kin gani ko da nake ce maki mamanmu bana jin ta a cikin zuciyata kamar yadda nake jin Auntynmu ma ko? Kin ga..............."
Farhana ce ta fara fita tana lekawa a hankali, ganin basa nan da sauri ta musu alamun su fito, suka fito suka yi dakin ta da gudu ta rufe kafin ta kai zaune tana fashewa da dariya, sai kuma ta yi dif tana tafka tagumi ta dubi NUR dake mata kallon dariyar fa? Ta ce" Ban san yaya zan iya kallon yayana ba, kin saka Ni a wani hali yarinyar nan"
NUR ta zauna tana rike da hannun A'isha ta ce" A'isha kina jin yinwa ko?, ki ci wani abu sai mu yi magana kin ji?, Dan Allah Farhana bata wani abin ta ci sai mu yi magana, ki daina min maganar wannan ya'yan naki Ni du abinda kike tunanin na aikata ki dauka a ranki cewar har cikin raina ban ma san na aikata ba, a tsorace nake, na gani kuma daga Ni sai shi a wajen nan... Kuma ya fara sanar min yana iya dukana.........yaya zan yi kenan?....Ni ban yi dan wani abu ba kuma ma ko matarsa ta ki ta saurareni ne, Ni kuma ba zan kyale ta ta dake Ni ba, dan wallahi ko Sulaimana ya kawo min duka zan rama ne.....dan haka ki ma daina daga hankalinki a kan wannan dan Allah "
A'isha dake dubanta a lokacin da FARHANA ta ce" Lalle ma, kawai dan kin Tsorata sai ki rukunkume ustaz? To ke tsoratarki abin gudu ce ai........, waye Sulaimana?"
A'isha ta sauke ajiyar zuciya ta ce" Ya'yanmu ne, shi ne baba a gidan mu........., kin ga irin horon da mama ta bata ko? Ko shi ya tsaya tsayawa take yi a gabansa sai dai idan ta ji jiki da karfi da yaji ki ga ta rusuna Ama ba dan Allah ba, dambe ta yi hala? Ai bata bari ta kwana, hudubar da kullum take yi mata idan zamu fita fa shi ne du ubanda ya taɓa ta ta taɓa shi ko dan waye komai tsufansa....., da sauki ma da bata zagin manya, da abin yayi yawa"
Farhana ta zuba musu ido, bayan ta daukowa A'isha madarar itama ba daya bama sannan ta sake zaunawa cikin su, haka kawai take so ta ji koda kadan ne a cikin labarin su......haka kawai take ji a ranta zata so jin wani abu da ya shafe su wanda yake da darajar zamowa siri a duniyar su.....haka kawai take ji a ranta zata yi magana da su mai mahimmanci...., bale idan ta dubi HALLAH sai ta ji har cikin zuciyarta zata so sanin wace ita wai....?...............
A dakin JAUHARA kuwa, zaune suke, JAUHARA a gefe saman kujera tana kallon FU'AD dake rike da MAZNA a jikinsa tana ta kuka har yanzu, gaba daya hankalinta ba a jikinta bane, MAZNA bata iya control din kishin ta ba, idan har ta ga abin dake yi mata barazana da taba lamarin mijinta fita take yi a hayacinta.....bata gane komai bata sauraron komai....
A hankali ya sake riƙe hannayen ta ya ce" MAZNA, ya kamata ki ringa sasautawa zuciyarki a kan lamarin Big broth, ya kamata ki sakawa ranki fa yanzu ko an jima yana iya ganin watan ki ya aura, idan har kika sakawa kanki Salama kika yi hakuri kika rayu da hakan a zuciyarki ko hakan ya tabbata ba zaki sha wahala ba, kuma Allah in ya ga kin dauke kai sai kin fi daraja a idannuwansa....., ke baki san ya muke bane, kin ga namiji ko? Idan kika nuna masa halin ko in kula sai ya fi neman inda kike, Ama ke rayuwar ki kin kasa yi masa haka kin nuna masa kin fi son shi fiye da ke son da yake maki, dan Allah yaya za'a yi ya ki wulakanta mana ke????, haba dan Allah ya dace ki yiwa kanki fada Aunty....."
Idannuwanta da take budewa da kyar ta bude tana dubansa ta ce" FU'AD, idan ka kuma hada IMAD da wata macen ina mai tabbatar maka ina iya tsanar ka!, kishi halal ne, kuma a musulunci ina da damar kiyawa a min kishiya, dan haka na zabi barin kiyawar....ba zan taba lamunta mijina ya auri wata ba har abada....., kuma yarinyar nan kana kallo ta mare Ni, a gaban ka ta mare ni ka kasa shigar min fada ka barmu daga Ni sai JAUHARA, bayan kana gani bayanta ne FARHANA take shiga dama ba kaunata take yi ba ko????"
JAUHARA ta tabe baki ta ce" Yaya kike so ya shiga fadan bayan ya tsayar da rayuwarsa da tunaninsa a kan wace ke masa kallon dan daudu? Baka Sani bane Farhana kallon jinsinku daya take maka dan haka ka ba kanka lafiya tun wuri ka samo mai son ka, ......Ni abinda nake son tattaunawa da ke aunty nake so ki Dube Ni ki saurareni!"
Ta gyara zamanta tana dubanta ta ce" Har yanzu kin kasa gane waye mijinki, har yanzu kin kasa gane ba fa yaro karami ba kuma wani gaja kike aure ba da har abubuwan nan zasu kai shi inda kike so...., kin kasa gane idan kika ce zaki yi fito na fito da mijinki a nan ne zai nuna nasa ikon da sai kin yi kuka risris da idannuwanki, aunty sam kin ki ki gane cewar ba fa ta hanyar nan bane zaki samu abinda kike so da big broth ba....., ga hanyoyin da idan kika rike wallahi sai dai a maki fada da shi kina kallo har a rarashe ki Ama sam kin kiya, kullum fada maki nake yi, ki girmama mahaifiyarsa, ki so mahaifiyarsa, ki yi mata biyayya, ki yi hakuri da kanwarsa daya kwalin kwal da Allah ya bashi, ki yi hakuri da kakarsa komai abinda take maki, ki kyautatawa mutanen dake kasa da ku........, ba ruwanki da harkar shi da mata, aunty da ace mijinki mai shinshine shinshine ne da yaya kenan?, na tabbata ba zaki iya hakura da leke lekenshi ba, du kin hana kanki sukuni aunty, da kudinki a banki da harkar dake kawo maki kudi wato mijinki ama sai damun kanki kike yi har ki ce wai kin ce masa wai dan ya samu wannan yarinyar ce ya juya maki baya??????, kin fa san waye shi, kin sani sarai waye mijinki, to ai da sauki ma da ya tabbatar maki eh dan ya same ta ne ya juya maki baya da bai hada da wani abin da zuciyarki zata buga ba, Ni kam gaskiya kar Allah ya jarabeni da irin wannan natacen son me ake da shi...."