← Book details Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 141

Sashe 36

Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Malan ya girgiza kai da takaicinta ya nuno mata yatsa ya ce" Ina daf da kawo karshen zamana da yi maki iyaka da gidana da kuma ƴaƴana tabas idan kika ci gaba da yi min maganar jahilci da ha'inci a nan!, ke har kina da bakin cewa an maki iyaka da yarinyar da kike budar baki a gabanta kina cewa ba ke kika haifeta ba? Ke in ba dan yarinta da rashin sanin ciwon kai ba HALLAH har ta kuma kallon inda kike bayan abinda kuka yi a gabanta?, na ji kunya kwarai da gaske na kuma raina wayonki, na yi tir da Allah wadai da shirmen da kika aikata min yau a gidan nan, kuma ina mai tabbatar maki na karshe ne, kin ga, a kan Sulaimana, ko A'isha, ko NUR, idan na kuma ji kin budi baki kin aibata min ya'ya a bakin auren ki, haka kuma idan kika yarda kika kuma fita daga gidan nan ba da izinina ba sai na mugun saba Miki, ban idasa zama abin wulakantarwar da har zaki nemi maida min gida kamar dandalin mararsa tarbiyya ba!"

Maman yara sai ta aro abinda ta fi kwarewa a kai, wato kuka ta fashe da kukan ta ta mike ta nufi dakin ta

Tana shiga yaran suka takure waje daya, ta nufi kuryar dakanta ta zauna ta yi tsittttt da kukan kirjinta na dukan da ya wuce misali........

Toh, ikon Allah, ta haka aka bilo mata kuma?????, ai kuwa ya zama wajibi itama ta samu wata hanyar da zata ci gaba da samun nasara a kansu baki dayansu, tunda har Malan ya iya Tare ta ta wannan hanyar ya zama wajibi ta bi ta wata hanyar ta sake samun kansa......., a dole ta dane kanta bata fada yaran ba har dare ya tsala sosai sannan ta fito ta dage labule ta yi tsaye tana duban su, su sun yi shinfida daf da dakinta, ita kuwa auntyn yara tana daga ciki kusan dakinta itama, sai shinfidar Malan dake kusa da zaure gidan wace itace ta tare hanyar shigowar........

Huci ta fitar kafin ta koma cikin zafin nan ta kwonta tana ta sake sake....., Malan kenan, zaka maimaita abinda ka fada kwana kusa da yardar Allah!.

Bayan kwana uku da fitintinun nan.

Yau ma da aka tashe su daga makaranta babu irin yadda yaya ANAS bai yi ba dan su saurareshi, Ama IMTEE ta nuna sam bata huce ba, a dole ya yi hakuri ya koma cikin mota ya zauna yana hangen su da tunanin cewa zata huce ne ai, idan bata huce ba nan da wasu kwanakin kuma gaskiya zai je har gidan ya samu mamanta, ya tabbata zata yi mata magana.....shi kam bai taba ganin mutun mai fushi har haka irin IMTEE ba, ya zata ko dan abin alkhairin da yake mata zata kasa yin fushi mai tsayi da shi haka, Ama zuwa yanzu ya gama gane cewar shi ya fi son ta, kuma dukiyarsa ba zata sa ta kyale wulakanci ba, ba zata taba kyalewa a yi mata wulakanci ba, a gaskiya ba zai taba iya yafewa Na'ima ba, duda kuwa irin yadda mamansa tace yayi hakuri ya haɗa su biyun a tare tunda ba abin ya hade sun ya gagare shi ba ai, Ama a yadda yake ganin IMTEE da wahala ta yarda ya haɗata da wata a soyayya ma bale a maganar kishiya....shi kuwa a yanzu dai, a wannan gabar da yake, gaskiya zai iya hakura da kowace mace a kanta.

Fa'iza gaba daya yau sai ta kasa jurewa, sun koro da tafiya ta ce" IMTEE, wai me yasa kike yiwa yayana haka? Ko nauyina ba zaki ji ba? Ai ina ga ko saboda Ni ya dace ki daga masa kafa!"

IMTEE ta dubeta, sai dai ta kasa ce mata komai saboda bata san me din zata ce mata ba, ko A'isha ta yi ta yi ta bar maganar ta Dube shi haka kawai idan ta tuna a kan soyayyar da bata idasa nitso bane ake wulakantata sai ta ji ina da ta gama nitso? shiKenan sai ya karbi lasisin jazawa iyayenta zagi a banza a wofi? Ita dama ta san ba lalle ya zama sa'an yinta ba, Ama bata san cewa abin har ya kai haka ba.

A'isha ta dubi Fa'iza a sanyaye ta ce" Fa'iza kar ki dauki abin nan a wani kala, kin san ko da muna yara sosai Imtee bata yarda da du abinda zai janyowa su babanmu zagi, bata yafe irin abin nan, shine kawai dalilin fushin ta, ama Ni na san zata yafe masa, abinda ya sa take kara kiyaye shi saboda har yanzu baba bai bata damar ta bashi damar ya ringa zuwa gida bane, tace tana tsoron ta shaku da shi baba ya ki tarayyar su, ko fahimceta dab Allah "

Fa'iza ta girgiza kai, a raunane ta ce" Masoyi dai ba makiyi bane, kuma da kin san irin hukuncin da ya yiwa Na'ima da kin Dube shi tuni, IMTEE yaya Anas fa da darajarsa fiye da tunaninki, SO ne kawai mai kai bawa inda za'a wulakanta shi!"

Daga haka ta cenza hanyar, domin yau sam na zata iya yin doguwar tafiyar da su ba ....., gani take yi sam basu yi mata kara ba, zuciyarta ba zata iya daukan irin wulakancin da ake son yiwa ƴaƴanta ba.

Ajiyar zuciya IMTEE ta sauke ta sake kan jakarta da kyau tana ta nanata addu'ar da Anna ta koya mata a yau

A yanzu fa, kullum sai Anna ta yi mata karatu na minti talatin a kala, idan aka fido su hutun cin abinci da sallah da dan hutun minti ashirin haka , take zuwa office din Anna ta yi mata abinda ya samu, a yanzu haka yau ta bata hardar huruful hj'iya, tace kuma in sha Allah gobe zasu hau na gaba, tace tana so a dan lokaci ta iya haɗawa ta karanta kadan kadan har ta kware, haka kuma tace in sha Allah zata hade mata harda na Turanci......, ita da kanta a yanzu idan ana musu karatu a pasali ta fi maida hankali saboda tana so ta zo cikin masu bada harda

Basu cewa juna komai ba ita da A'isha har suka isa gida....., suna zuwa kuwa jakunkunnan su suka ajiye suka shiga yin wanka suka dauki abincin da aka ajiye musu suka ci sanan suka yi aikin da auntynsu ta raba musu , wato shara da wanke wanke wanda a yanzu kullum su ne ke yi, sai girkin yama da ya dawo hannun su, in dai aunty ce ke girki to su suke yi tana kansu tana nuna musu komai.
______________________________

Sai da yama ANAS ya dauko su Anna ya nufi gida da su

A hanya FARHANA ce ke yiwa Anna firar irin yadda ginin nan ke sauri da kuma irin yadda ginin ya dauko mahaukacin kyau tun ba'a gama ba, ta dubi ANAS ta ce" Broth, kai da kanka ka san ginin nan ya haska anguwar nan ko? To wanan ai ko a wancen anguwar tamu aka watsa shi sai ya dake manyan ma'aikatun anguwar nan bale a nan wajen......"

Sam Anas bai ji abinda take fada ba, har sai da ta Dube shi ta ga ya zubawa hanya ido ne kawai yana tuki , fuskarsa ba wani annuri, hankalinsa du a ba a jikinsa ba

Baki ta tabe ta maida dubanta bakin hanya har suka karaso aka bude musu get din suka shiga

Bayan ya tsayar da motar ne Anna ta fita tana duban Fu'ad dake gaisheta hadi da yi mata sanu da zuwa, wato kamin MAZNA, ta amsa shi da kula sannan ta nufi bangaren ta zuciyarta da tunanin yau kwana hudu kenan da take ganin alamun yayarsa ta sauka a gidan nan, Ama har yanzu bata zo ta gaishe da su ba,....yaran yanzu dai kam basa jin magana Allah ya kyauta.

Fitowa FARHANA ta yi daga motar ta zagaya ta bangaren Anas ta ce " Kai lafiyarka kuwa??"

Anas ya dubeta yana langwabar da kai abin tausayi ya ce" Ba komai sister"

FARHANA ta tabe baki ta juya zata wuce suka yi ido hudu da Fu'ad.....

Idannuwanta ta janye daga kansa ta yi gaba ba tare da tace da shi komai ba

Fu'ad kuwa idannuwansa masu cike da kishi ya sauke a kan Anas wanda yake ta kansa ko gane komai bai yi ba, domin daga nan ma kawai motar ya juyar ya fice ya nufi gidansu, kansa yake ji yana ciwo da zuciyarsa , wajen da zai samu nutsuwa yake so , lalle lalle a yau kuwa sai ya je gidan su IMTEE, ba zai iya ba, ba zia iya sake hakura wani daren yayi bai ji daga gare ta ba.

________________________________

Bayan sallar magariba

Mai gadi ne ya wangale Babar kofar get bayan ya leka manyan motoci biyun da suka tsaya a gaban kofar , irin motocin kamfanin lokarin din mota baba na garin Niamey ne, .........

Wanda ya gani cikin motar ya sa bai iya tsayawa gaishe da su ba da gudu ya koma ya wangale katon get din jikinsa na rawa ya rage tsayinsa sosai yana jimke hannayensa hadi da marabatar mutanen dake cikin motar har direbobin dake jan motocin suka yi cikin gidan da su suka tsaya a inda aka umarce su sannan suka yi jira sunna kallon nan da nan irin yadda mai tsaron get din nan ya fara gangamin bakin da suka iso, nan da nan filin gidan da ba kowa ya dauki zaratan samari, cikin su harda Malan da wasu daga cikin amintatun almajiransa da suke shigowa nan din, suka nufo motocin kowane fuskarsa dauke da wadataciyar fara'a suka tsaitsaya suna jira a bude motar a fito....., mai tsaron get kuwa haka yake walagigi farin ciki ya gama kashe shi ya rasa ina zai nufa, gashi basu da damar zuwa bangaren su Hajiya Anna da Hajiya MAZNA, da tuni ya wuce cen din da tarin abinda yake bakinsa mai dauke da daraja da farin ciki zallah.......

Murmushi ya sauke, a hankali ya lumshe idannuwansa yana shafa gefen fuskarsa ya kai dubansa kan ABDUL Fatah ya ce" HOME........sweet home"

Abdul Fatah ya yi murmushi ya bude motar ya fita a tausashe bayan ya bude bangaren yake ya furta"..........................

21
Chapter 36 · 0% Book details