← Book details Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 141

Sashe 34

Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Innalilahi wa Inna ilaihi raj'une, innalilahi wa Inna ilaihi raj'une, lahaula wala kuwata Ila bilah, IMTEE? Me nake shirin gani da idannuwana? A'isha me kuke yi haka da raina da idannuwana ina kallon ku????" mama ta fito hankali tashe tana fada da karfin gaske

Mama ta saka hannu ta warto A'isha ta jimke hannayanta ta shiga dukan ta hadi da fashewa da kuka

A rikice IMTEE ta nufe su, da karfi maman yara ta hankadata har sai da ta je ta daku da garu lokaci daya ta saka ihu dan hannunta har ya gurje

A gigice AUNTYn yara ta yi kanta tana taro ta , rai bace ta daga idannuwanta ta dubi maman yara zuciyarta na wata irin tafasa saboda bacin rai

Maman yara ta nuno su, idannuwanta na ganin shigowar baban yara ama bata wani damu ba ta ce" Idan ke a yau kin nuna min nonon wancen marar mutuncin kika sha, daga tsatson wannan marar mutuncin kika fito, ta hanyar yi min rashin kunya da rashin da'a a gabana zan iya kyale ki, Ama baki isa ke da uwarki ku shiga hurumin wace na haifa Ni kuma ku ce zaku min katsalandan ba...."

Jikin A'isha na wani irin rawa hakama na IMTEE, uwa uba na malam da na Aunty, maman yara ta juya ta dubi A'isha ta murde mata kune ta ce" Walahi Walahi a kan shiga harkar Rahama sai in tsine maki in salamawa duniya ke, saboda kin yi kadan ki daga min hankali ki bi nahiyar makiyiyita, ke A'isha a kan in wayi gari in ga kina shiga harkar wancen marar mutuncin gwara in wayi gari da gawarki a gabana! "

"Innalilahi wa Inna ilaihi raj'une, Ke, ke!" Malam ya fada da karfin da ya sa du suka juyo suna dubansa

Lokaci daya gabansa ya fadi ya zuba musu ido shima daga su har ya'yan nasu yana kallo , maganar Malan Hamza na dawowa a kwakwaluwarsa

Wani irin huci ya sauke mai zafin gaske lokacin da maman yara ta ce" Malan, mene? Nace mene? Bari ka ji, idan ba Ni kadai na isa da yata ba ka ce min shegiya nake, ko kai baka isa ka koya min yada zan yi da yata ba bale kuma kishiyata makiyiyita!"

"Dan ba Ni na haife ta ba?" Malan ya fada a hankali yana tsare fuskar mama da kallon da ya a idannuwansa ya ga ta wata zabura, kafin ta kale shi da sauri .....sai kuma ta ɗan ja baya, kafin ta zarro ido.....
Sanin abinda zai biyo baya a irin yanayin nan nata na idan ta Tsorata ba komai bane sai koke koke ya sa ya juya ya zubawa A'isha ido, wace ta fita a hayacinta, ta rasa ina zata nufa, kuka take yi bilhaki, dukiyar ta mata zafi, ta rasa baban bango mai daraja wanda kowani da ke takama da shi, wato uwa ta gari, ita kam ta jima da gane cewar mahaifiyarta fa uwa ce, Ama kuwa sauran zancen ba dai a raba shi da ta gari ba ya Subahanalah Subahanalah Subahanalah

Kuka maman yara ke yi da karfi tana fadin" Malan? Sheganta min yarinya zaka yi?, Malan wai sheganta min yarinya zaka yi? Wayo Allahna yau na cimma lokacin da zan ga wannan bak'ar ranar da idannuwana, lalle Malan ka auro jafa'in da har yau zata sa ka Dube Ni , Ni kace min yata ba taka bace!"

Hannun A'isha Malan ya riko, wace ke dubansa a firgice, ya haɗa da na IMTEE wace ta fi ta shiga halin kaka naka yi, ya ja su dakin AUNTYn yara

A gigice maman yara ta so bin ta, Malan ya mako kofar nan har ta dantse mata hannu kafin ya zaunar da su ya zauna ya sada kai , kansa na mugun sarawa yana jiyo maman yara tun tana ihun kuka har ta koma gunji har abin yayi nisa da dakin, kai har ya ji alamun kamar ta fita daga gidan kafin ya sauke dubansa a kan ya'yan nasa da suke dubansa a gigice a zaune daf da su

A hankali ya sauke ajiyar zuciya kirjinsa na daukan zafi , a raunane sosai ya ce" Kukan ne kuke yi har yanzu???"

IMTEE da ta zamo auta, kuma wace ta fi kusanci da shi a kaf ya'yan nasa ce ta karasa ta kama hannunsa tana kuka ta ce" Aba, daga cewa auntynmu ta zauna mu je, mu mu nemo ka shine ran mama ya bace, shine har tace zata tsinewa A'isha, aba dan Allah ka cewa mama idan ranta ya bace ta daina zagin auntynmu, aba auntynmu ta daina neman kashe Ni, ta daina tsanata, mama tsoro take ji kar ta kashe mata Ni, Aba Ni na san ba zata kashe Ni ........."

"Aba, kai ba abana bane?" A'isha ta katse IMTEE, sannan ta zubawa aba ido da duban da ya sa ya dubeta shi ma kirjinsa na bugawa

A hankali ya mika hannu ya riko nata itama, ya hade nata da na IMTEE, a tausashe sosai ya ce" Waye ya kawo wannan maganar?, waye yace maki Ni ba mahaifinki bane? A'isha Ni babanki ne, Ni ne na haife ku , ku duka kun ji????"

A'isha ta sauke ajiyar zuciya a hankali ta ɗora kanta a gefen kafadar imteee

Aba ya hana kansa zubar da hawaye sosai ya Dube su ya ce" lokuta da yawa, kuna samun kanku a tashin hankali irin wannan, ina so ku dauka cewar yanayin rayuwa ne kawai ya zo muku da jarabawa ire Iren wannan, ku yi hakuri ku ci gaba da yiwa iyayen ku biyaya, ba ruwanku da fadan iyayenku , kar ku dauki furucinsu a cikin fushi ku saka a zukatan ku, iyayenku ne, babu wace bata son ku a cikin su kun ji?, AUNTYn ku ba zata taba yi muku ila na, hakama mamanku, kun ji ko?"

A tare suka amsa, hakan ya sa Aba yayi murmushi ya ce" Bari in je, Ku zauna a nan, za'a shigo muku da abin kari, idan lokacin makaranta ta yi kuma maza ku shirya ku wuce kun ji? Allah ya muku albarka"

Yanzun ma amsawa suka yi, kafin ya mike ya fita

Bayan ya tabbatar cewa mama ta fita sai ya bude su sannan ya nufi dakin soro, AUNTYn yara ta mike daga tsugunin da ta yi ta bi bayansa

A hankali A'isha ta ɗora kanta a saman cinyar IMTEE da kaffafuwanta ke mike suka yi shiru su duka, babu mai cewa yar uwarta ufan, kowace ta afka a dogon tunani.

A hankali AUNTYn yara ta karasa gaban baban yara ta duka tana kallon fuskarsa da hawayen da ya cika masa idannuwa

Hankalinta ya tashi matuka, a raunane sosai ta furta" Ya Allah, Malan kuka zaka yi? Dan Allah ka yi hakuri kar ka daga hankalinka, shi yasa duk abinda zai faru nake rike nawa fushin nake iya yina in rike harshena dan ban san inda maganar zata kai ba idan nace zan rama ko zan yi fito na fito da wani tashin hankalin da idannuwana ke gani a gidan nan, ka yi hakuri, laifina ne da na yarda su min rakiya dan mu je nemo ka, in sha Allah ba zan kuma bari dogon abu ya shiga tsakanina da yaran nan ba in dai har hakan daga maka hankali zai yi , ka yi hakuri dan Allah "

Tausayi, tashin hankali hadi da tsoro ne suka ringa lulube zuciyarsa

Ba zata kuma yarda wani abu ya shiga tsakaninta da yaran ba in har hakan zai daga masa hankali? To me ta yi da zata ringa bada hakuri? Yarta ce fa, magana ake ta yarta ta cikinta,

Nan da nan sai ya shiga tariyo rayuwarsa ya shiga auna du lokutan da yake hawa kanta da masifa da alkawarin saki da wulakanci idan ta taɓa maman yara.....

To wai taɓa maman yaran menene take yiwa maman yaran?

Yawanci fadan a kan maman yara ta tarbe shi da batun an daki Imtee ne, an zagi Imtee ne, an hana Imtee hutawa, ana son takura Imtee da aikace aikace......, an matsawa Imtee ta yi kitso, an matsawa Imtee ta yi sallah koda bata yi...., an takurawa Imtee, jira ake a ga Imtee ta yi wani laifi yanzu za'a takura mata......

To wai dama idan ba yar kwabar da sakawa a hanyar anya za'a ci ribar tarbiyyar ya'yan kuwa?????

To in ba'a takurawa yaro ya je makaranta, yayi karatu, yayi aiki, yayi tsafta, yayi ibada a kan lokaci, ya kiyaye furucinsa, ya lulube jikinsa me za'a yi da shi in ba wannan tarbiyyar da kuyayewar?, to wai dama du da yake yi mata kallon muguwa kamar yadda maman yara ke fada ya taba jin ta daga murya tana fada suna fada da mugwayan kalamai na tsoratarwa har zuwa na tsinuwa ne???

Innalilahi, wai dama sun taba shiga halin da ya tardo aunty na a gidansa tana aibata masa yaya?

Shin ya taba ji ko gani da idannuwansa lokacin da aunty ta budi baki zata yiwa yaran nan tarbiyya ta ware wane ne nata wane ba nata ba har ta zagi A'isha ne???????

Wani irin huci ya fitar lokaci daya maganar malan Hamza na dawo masa cewar yaushe rabonsa da yayi zama na nemawa yayansa yanci irin na samun kusanci da gane ainihin me suke ciki??????

Lahaula wala kuwata Ila bilah

A mugun sanyaye ya furta" Allah ya sa lokaci bai kure ba Rahama"

AUNTYn yara ta sake dubansa hankalinta na mugun tashi, a raunane ta ce" Malan, me yake faruwa? Kurewar lokacin me? Malam saka na zaka yi ne? Malam idan ma sakina zaka yi sai ka ware min daki a gidan nan, dan ba inda zan je Malan, dan Allah ka yi hakuri da rashin ji na, ka yafe min Malan, ina sulaimana yake? Malan Ni da SULaimana mun gama daga maka hankali ko? Malam ka yafe mana dan Allah "

A hankali ya ce" Rahama ki sassauta dimuwa mana..., shin in sake ki kuma wa ya rike mu Ni da y'ayana???"

AUNTYn yara ta zuba masa ido tana kalonsa
Chapter 34 · 0% Book details