Sashe 42
Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A tausashe bayan ya zauna saman kujerar da malan ya bashi ya ce" Har yanzu dai jiki na nan malan???"
Malan ya sauke ajiyar zuciya, a tausashe ya ce" Jiki na nan IMAD, sai hakuri da addu'a kawai, dan a yanzu bana tunanin ko yarinyar nan ta gani in zata iya zama dai-dai......, ta riga ta yiwa abin mugun daukan da ya yi mata baban ila, yanzu fa zata yi maganar hankali, sai kuma ta juye gaba daya maganganun su koma na marar hankali, ka ga dai a wanke take tasss, ba dati ko kadan, wuni take tana aiki tana girke girke a gidan nan, idan ta dauki karatu kuwa sai ka dubeta, Ama kuma a cikin hakan ake sakin zancecekun da suke tabbatarwa cewar ba a cike ake ba....., sai hakuri kawai, da ake cewa da batan mutun bat a rasa gane a raye yake, a wani hanu yake, gwara a san mutuwa yayi ban yarda ba sai a kan mama da abinda ta haifa, Allah dai ya bata lafiya"
IMAD ya sauke ajiyar zuciya, wannan lamari na mama likitoci sun tabbatar masa dépression ne ya yi mata mugun kamu, an ce a barta a asibiti malan ya kasa hakura....., a gida dai take daukan magani a da kafin daga baya sam ta kiyewa maganin
A da idan ta dauki maganin bata surutun nan haka, sosai da sauki, Ama tunda ta kiyewa maganin abin ke yin gaba, sai addu'a kawai da Malan ke yi mata ba dare ba rana, domin idan aka kwatanta yi mata maganar abinda ta haifa yanzu zata birkice, bata gane rarashi a kan abin, bata gane komai, abu daya take ganewa shine za'a miko mata, likitoci zasu miko mata babynta.....Allah sarki
A tausashe ya furta" Allah ya bata lafiya, bari in je ciki sai na fito"
Malan ya mike yana fadin" A fito lafiya, Allah ya kara girma da daraja, Ubangiji ya kara rufa asiri "
Murmushi kawai IMAD yayi yana tafe a nutse mama da ta dauko katon hijab na biye da shi tana bashi labarin da du yayume yayume ne, sai ya saurareta da kyau a tausashe sai yace da ita " Mama, ki yi addu'a mana, ba kyau yawan magana kina tune?"
Sai kuma ta yi wani dan tsai kafin ta kwashi karatu, sai kuma ta buge da zikiri harda dukan kirji, shi dai yana tafe har suka zagaya bangaren bakinsa ya nunawa mama wajen zama yace da ita yana zuwa , kafin ya shige
Abdul bassit kadai ya samu a farke, yana buga game a baban TV din dake jikin bango makale
Gaisawa suka yi kafin ya zauna yana dan lumshe idannuwansa
Abdul bassit ya Dube shi ya ce" Kwana ka yi kana aikin da ka fi kwarewa ko?, ka san Allah ka rage fa, bayanka zai saki da wuri.... tam"
IMAD ya dube shi kafin yayi murmushi yana girgiza kai ya ce" An gaya maka kowa kai ne?....., man idan ba'a huta ba ai ko aikin aka yi ba za'a gane ribarsa ba........, Ni da aikin nan sai na huta.........."
Abdul bassit ya kame haba yana dubansa
IMAD ya mike ya ce" Bari in leka Anna...., jirgin karfe nawa zaku bi?????"
Abdul bassit ya ci gaba da dukan abin game din nan ya ce" Inaga na karfe daya na dare, but mutalab ba zai je ba fa yace sai an kwana biyu"
IMAD ya gyada kai ya ce" Ok, idan mun yi sallah ma fita ko???"
Abdul bassit ya ce" In sha Allah broth"
Daga haka ya fice suka yi gaba da Mama
A filin gidan ne su Anas suka karaso su ma da fara'arsu suka shiga gaisawa......
Da kula, da kuma sakewar fuska yake amsar hannun du Wanda ya zo dan su sake gaisawa, kafin su ci gaba da nufar bangaren Anna tare da ANAS da FU'AD
A tausashe ya dan dakata yana duban FU'AD ya ce" FU'AD, yaya aiki????"
Da sauri JAUHARA dake taya auntynta jera kayan abincinsa cikin basket masu kyau ta ce" Aunty, yana yiwa Fu'ad magana, Allah ya sa kar ya saki bakin ya ringa ratabo abinda aka tambaye shi da wanda ba'a tambaye shi ba"
MAZNA dake mak'up ta ɗan leka itama kafin ta koma ta zauna tana fadin" Yi ki gama hada min, duba ki ga Anas din nan mai shegen kan tsiya, ai ya zo kuma ya fara like masan"
JAUHARA ta yi yar dariya ta ce" Ni kuwa bana ganin laifin gayen, inda zaka samu ai a cen kake, kai aunty mijinki mai classs ne, haka kuma Allah ya masa mutane kala kala, kin ga mahaukaciyar maman nan itama yanzu ƙafarsa kafarta"
MAZNA ta dafe goshi kafin ta ce" Kai, inada aiki ja a gabana, na rantse matar nan sai na mugun tsoratara ta yadda zata daina bi min miji, koda yake baki ga ko yanzu idan ya nufo nan bata biyo shi? Ai tunda nace mata in tana biyo shi wajena sai na sa an sace Mata tsohon mijin nan nata take tsoron biyo shi "
Jauhara ta bushe da dariya tana dubanta ta ce" Aunty baki da kirki, mahaukaciyar ma baki bari ba?, yanzu dan Allah Ni abinda nake so ki sa yaya ya sama min daya cikin abokan nan nasa mana, aunty wallahi idan na samu daya na haye, duda ba zasu taba kamo yaya ba, Ama su ma manyan gayu ne....."
Sai kuma ta yi shiru ta sake zubawa IMAD ido ta girgiza kai ta ce" Allah ya baki abinki, ki kara rikewa fa, dan Allah hango damatsunan mutumen cen, aunty mijinki irin su ne idan kina son kwonciya a kirji ki yi barci ga waje nan a wadace......., sai masifar iya soyayya wayo Allahna "
MAZNA ta dubeta tana sakar mata harara ta ce" Ke ban son iskanci fa, na raba ki da yaba min miji haka fa, ki gama hada min Ni in tafi kar a ja min wata maganar, wai da kika sauko tana me ita wannan Annar???"
JAUHARA ta tabe baki ta ce" Sunna kasa su dukansu harda tsohuwar nan, tana ganina ta fara tambayar yaushe na zo garin? Ke kam dangin mijinki ne yan sa ido bama mamansa ba!"
A ranta kuwa tana ayyana' Su aunty dai shegen kishin BALAKI, ko Ni na yabi yaya sai ta ji haushi, Gayanan saboda kishin ta da gudun kar wata ta birge shi ta je ta bambarowa kanta aikin dake iya hadasa mata matsala, ita ke min kallon wace ban san abinda nake yi ba, Ama ai ita da bakinta ta fada min cewar yaya baya iya hakura da sex din kwana biyu ma........, hum !'
A waje kuwa IMAD sun dan zanta da FU'AD kafin ya maida dubansa kan ANAS ya ce" kai, wai yaushe zaka yi aure ne??"
Anas yayi yar dariya yana sada kai ya ce" Sir ai kai kawai nake jira ka nemo min auren yarinyar, na samu mata fa"
FU'AD ya sakar masa harara cike da jin haushin sa, dan shi kawai gani yake yi FARHANA shi take so.
IMAD yayi murmushi yana dan taba gefen kafadarsa ya ce" Haka ya fi, ka wani tsofe min a gida......, idan na gama zama ɗan gari zamu je mu ganta yarinyar"
Anas yayi murmushi yana kara sada kai, dan kuwa ya san ogansa mai zuwa ne ya raka shi din, kai shima zai ji dadin haka sosai....ya tabbata IMTEE zata karra daukansa da mahimmanci idan ta ga wanda ya zo har gidan su......, kai yana fatan goben nan ta yi ta yi ko zai samu ya je inda take.
Da kula IMAD ya ce" Idan an jima zaka je ka dauko min ALIYU, ka je da Babar mota da kuma wata motar dan tare yake da iyalinsa da kayansu ka sauke su a plateau cikin gidajen nan dake daf da gidan cen......, plz a sa a wanke musu komai kafin su sauka....and idan da abinda za'a sake du a sake, nan da 4hrs zasu sauka in sha Allah "
Anas ya rage tsayi yana amsawa kafin ya juya dan cika umarnin bosss dinsa, duda wani abu ya tsirga masa a zuciya cike da tunanin me ya kawo Haidar Nijar harda iyalansa? Dan kuwa ya san waye Aliyu, shine hannun daman ogansa , mutun ne tamkar basamude, yana cikin security din ahalin SAWIRIS, ba karamin mutun bane, yau da gobe ya da da kansa ya nemi alfarma zama amintance, direba haka kuma mai tsaron lafiyar IMAD, hakan kuwa ya tabbata ya zamo inda IMAD ya saka kafa to fa haidar zai maida tasa....., irin yan gidan nan ne da ko da ido uban gidansu yayi magana sun san me yake nufi da maganar bale a kai ga yi da baki....., shi kam bai san me ya kawo shi ba, Ama ko meye ba zai so ace aikin da yake yi masa a Saudiya zai yi a nan ma, ina a Nijar shi ne hannun daman ELHAJI IMAD , daga shi ba wani!.
Bayan ya bude kofar sai da ya ba Mama hanya ta fara shiga da salamarta kafin shima ya shigo falon yana mai yin Salama hadi da murmushi ya dan dakata yana duban Kakarsa
A lokacin da Mama ta shigo da Salama Hajiya Inna ta shiga lalubar gilashinta tana fadin" Wai ina tabarauna?, ke tashi ki dauko min tabarauna, sai wani sune kai kike da wani hijab na meye ne? Ko dai wani abin kika je kika aikata kike boye min.....? Mtsssssss wai wace ke Salama kamar zata fasa min kunne? Ni kam ina cikin tashin hankali da mutanen nan......"
Sai kuma ta saka gilassss din idannuwanta suka sauka kan IMAD dake dubanta da dan yannayin mamakin jin ba dai zata daina wadinan maganganun nata na tashin hankali ba ko????????
Ido ta zarro tana nuno shi, sai kuma ta shiga kokarin tashi
A dole Farhana ta je da sauri ta kamata, sai da ta mike ta sakar mata rankwashi tana fadin" Ka ga mai halin munafukai, dan ubanki me hadina da ke da zaki wani rungumo Ni? Dan fa yace haka take min da baya nan, algunguma ai uwarki shaida ce har kadata kike kina wucewa, kauce min Ni in gana da yarona............ Allah sarki AHMADU........"