← Book details Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 141

Sashe 86

Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Farhana du sai ta tsargu, tana dubansu ta ce" Ba zaku gane ba, ba haka bane, abinda yake faruwa har ya sa haka ta faru fa mai girma ne, kun ga tsohuwar nan dake zaune? Du itace umul aba'isan haifar min da fitinar nan, ina cikin Rufin asirina, har yaya ya yarda da maganarsa tace ita idan ba buzu ba, ba zata yarda in auri bahaushe ba, tun muna wancen gidan namu ta sa yaya ya dakatar da shi......musulmi ne, mai usuli ne, haka kawai dan ta tsane Ni, karshe ta bi Ni da sharin da tsana da zagi....Ni kuwa na yiwa kaina alkawarin idan ta mutun sai in aure shi, har fa yaya Mutalab aka saka ya nuna yana so na , na tabbata dan kawai a gane in muna tare ne, basu san muna tare ba, ............, dan kawai a kara samun abinda za'a ce bana jin magana ne aka sa ya min rami a gane me nake ciki........., to kuwa in sha Allah idan ta mutu zan yi auren tunda har suka saka mata ido take wulakantani!"

HALLAH kawai dubanta take yi da mamaki kafin ta dubi A'isha ta yi mumushi ta ce" to kin ga wace ta fi Ni hauka ko?, sai ki bani lafiya da fadin Ban san duniya ba......, ke da kanki kin san a rashin sanin duniyar nawa na fi wannan , ashe Farhana ba hankali ban sani ba??????"

FARHANA a hankali ta ce" Nur, ba zaki taba gane me nake nufi ba, saboda baki san meye so ba!"

Nur ta yi murmushi tana duban ta ta ce" idan irin wannan ne, bana fatan saninsa....., me ake da shi? In dai haka yake Allah ya sa in mutu ban sanshi ba.....mtsssss!"

Farhana ta harareta tana nuna mata yatsa dan ta fara kaita bango ta ce"Kisan mummuke Page 55, and 56

Yan matan a kicin suke sunna aiki, sai dai du karfin aikin FARHANA ce , domin su abinda suka iya bai kai girman wanda ta iya ba, uwa uba aiki da kayan gaz du sai suka tsaya suna koya sannan sunna yin du abinda tace a yi cikin tarin tambayoyin da suke yi mata wanda ya dauke hankalinta daga yanayin rashin kwarin jiki da fargaban da take ciki

Anna da ta sauko ta shige kicin din da murmushi ta shiga duba abinda suke girkawa harda jus din da suka hada suka saka a frij, nan ta umarci mai yin sallah da ya je yayi ya dawo, wanda yake halin fashin sallah kuwa ya zauna ya kula da girkin

Su duka tafiya suka yi, hakan ya sa Anna tsayawa tana kulawa da girkin hadi da gyara fruits din Inna, domin su ta fi sha fiye da komai, bata cika fada abincin da ake yi ba, wannan ya sa bata haduwa da yawan ciwace ciwace...............

Saukowa suka yi yanzun su duka da hijaban Farhana saboda sallar da suka yi basu cire ba, sai dai sunna fitowa suka samu Murtalab da IMAD zaune sunna fira wace alamu suka nuna mai mahimmanci ce

Gaishe sun da FARHANA ta yi kusan tare suka yi da A'isha, a dole itama HALLAH ta yi sannan ya zamo ita ce karshe wajen nufa kicin din bayan ta bi wata kyakkyawar butar shayin dake tafasa saman wani kyakkyawan murhun garwashi dan Karami mai kyan gani a ido yana saman wani faranti na karfe wanda ke tare toka da yan kananun garwashin dake fadowa sama

Fira suke yi, firar ma mai mahimmanci domin Mutalab din ke fada masa zai so ya mayar da kaso mai tsoka na harkar reshen nemansa a nan, sannan yana so ya yi gini , domin shi fa Nijar ta masa, yana kyautata zaton zai dawo nan da zama gaba daya ne....., hakan ya sa IMAD fuskantarsa da kula ya ce masa ya dace yayi hakuri kadan ya kara tabatarwa zuciyarsa abinda yake so kenan, ba dan kowa kuma yake so ba sai dan kansa, saboda lamarin rayuwa kar halin rayuwa ya cenza masa abinda yake so din...

Ya koro da bayanin ne suka fito, a hankali ya ja bakinsa ya yi shiru yana dauke dubansa daga kan FARHANA da ta fara gaisar da su, sai dai sunna nufar kicin din ya sauke dubansa a kanta a lokacin da ta zamo ta karshe wajen shiga kicin din har shirunsa ya matukar bayana a wajen, har ma Murtalab ya zuba masa ido da tarin mamaki da kuma yarda da bayanin da Aliyu ya masa

A hankali ya dawo da dubansa ya sauke kan Murtalab, wanda yayi kamar ba shi yake kallo ba

A hankali ya jimke hannunsa kasa kasa sosai ya ce" Ina ga banda lafiya"

Mutalab ya zuba masa ido, a tausashe ya furta " Me yake damun ka? Subahanalah"

IMAD yayi shiru na dan lokaci, kafin a tausashe ya ce" Zan je in ga likita, kwanakin nan ina fama da bugawar zuciya, may be jinina ke son hawa......."

Mutalab ya zarro ido yana kare masa kallo, da girmamawa ya ce" Subahanalah, eh gwara mu je, ka tashi mu je yanzu, sannu Yaya"

IMAD ya sauke ajiyar zuciya ya ce" Zan je, fira zamu yi da Anna idan muka gama zan je......." Ya karashe yana tunanin bari su gama firar ya tisa keyar MAZNA su je su ga likitan tare, saboda shi bai wani yarda ba cewar wai ta warke duda ya same ta da yan uwanta sunna ta fira da dariya yanzu ma, Ama kawai zuciyarsa bata bashi cewar MAZNA tana lafiya ba

Da kula ya sake duban Mutalab ya ce" kar ka yiwa abih firar nan ta waya, kuma kar ka yi masa ita yanzu, ka ga magana ce mai girman gaske kuma mai mahimmanci, ka bari zuciyarka ta kara aminta da haka, sai ka je ka same shi, abinda ya yanke kuma shi za'a yi ok???"

Mutalab ya dan turo baki irin na shagwababen kanin nan ya ce" Kai da na zo dan ka kama min?"

IMAD ya girgiza kai ya ce" Akoy abinda zan kama maka ido rufe, ana akoy wanda dole zan sa mu bi a hankali......"

Mutalab ya sauke ajiyar zuciya sannan ya mike yana fadin" Bari in je in shirya zan raka ka ganin likitan nan....."

Ya karashe yana murmushi ya fice, IMAD kuwa sai kawai ya gyada kai a ransa ya ayyana ' Eh zan je, kwarai zan je, ba normal bane wannan abin, kuma na san komai isar mutun da du wani abinda yake iya takama da shi na baiwa ko na cutarwa bai isa ni ya kayar min da gaba ba......, just yannayi ne ke zuwa a kan lokacin da nake hada ido da........da........da.......hm zan dai ga likitan'

Daga haka ya daga kansa yana kallon Anna da abinda ta riko

Mikewa yayi ya amsa ya ajiye yana murmushi ya ce" Ke kika girka Anna ?"

Anna ta yi murmushi ta zauna saboda a plate ta zubo abincin , a lokacin da FARHANA ke tafe tana turo kayan fruits da ta jero da su jus tana kallon Anna, Anna ta ce" Eh to, Farhana ce da su HALLAH "

Spoon din da ya dauka ya dan rike a hannunsa kafin ya mayar wa Anna kayanta bai ce komai ba

Ajiyewa FARHANA ta yi ta juya a ranta tana ayyana ' Yaya kenan, dama ka taba, da da wahala ka kuma cin na bangaren ka saboda ko shake Ni za'a yi na yi girki a shake nawa dai ya fi na MAZNA dadi saboda Ni ba kalar chef din da Anna bata sa ya koya min girki ba'

Anna ma murmushi ta yi ta ce" Ba zaka ci abincin y'ayana ba? Ka kuwa san bani da dar du inda zasu shiga su girka a ci na yarda????"

Fruits din nan kawai ya janyo ya shiga ci a hankali ya yi murmushi ya ce" Ci abinki Anna"

Anna ta yi murmushi itama ta ci gaba da ci har ta gama masu aiki suka kwashe saboda su Farhana sun haye sama da nasu ne

Da kula Anna ta ce" Andadi dangane da maganar Farhana ne da manemin auren nan nata nake so mu yi magana"

Da kula ya dubi Anna ya ce" Manemin auren ta?, Farhanan tana da wani saurayi ne Anna ?"

Anna ta ɗan sauke ajiyar zuciya a tausashe ta ce" Ka san yaron nan fa, inaga suna tare"

Da mamaki ya ce" wani yaron? Wanda na yi mata iyaka da shi?"

Anna ta dubi yanayinsa, ta ga kamar ransa na neman bacewa hakan ya sa a tausashe ta ce" Andadi, ka kwantar da hankalinka ka nutsu mu yi magana dan Allah, bana so ko kadan ka bata rai ko ka ce zaka yi wani abu a kan wannan lamarin, Ni na san cewa addu'ar da nake yi idan ba alkhairi Allah zai ture abin nan da kansa, tunda har Inna ta ture shekara nawa ba'a bar abin ba a yi hakuri ka yiwa Inna magana ka ce kai kace ya zo ya same ka , dan na fada mata a yau yau ya zo ya same ka , saboda na gaji ......na gaji IMAD....."

Sai Anna ta sada kanta saboda idannuwanta da suka tara kwallah

Hankalinsa ne yayi masifafen tashi

A hankali ya riko hannayen ta yana dubanta ya ce" Kuka ne kike yi? Ya Allah menene take yi yarinyar nan da ban sani ba har haka? Dama abinda Inna ke fada gaskiya ne? Ta ci gaba da ganinsa ne? Ya Allah"

Sai kawai ya nemi mikewa

Da sauri Anna ta saka hannayanta tana riko shi sannan ta saka karfinta dan ta nuna masa so take yi ya zauna

Kasa ya koma ya zauna a hankali yana daga dubansa ya saka a cikin idannuwan Anna a tausashe ya ce" Bana so ki mata kuka, idan kika mata kuka ai ta shiga uku, gwara in je in zane mata jiki in fasa mata jiki da in bari ki zubar mata da hawaye Anna "

Anna ta girgiza akai a tausashe ta ce" Ba na fada maka haka bane dan in daga maka hankali, hawayena kuwa ina yi ne a inda nake iya yi dan in ji sanyi kawai, saboda abinda ke saman zuciyata mai yawa ne Andadi......."
Chapter 86 · 0% Book details