← Book details Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 141

Sashe 90

Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

HALLAH ta gyada kai tana fadin" kwarai baya son ki, wace irin soyayya ce zai taya ki bijirewa umarnin wace ya san ta isa da mahaifiyarki ma bale ke? wato Inna, wace irin soyayya ce zai ci gaba da ganin ki yana take umarnin yayanki? Wanda ya san yake da baban matsayi a duniyarki ?Wace irin soyayya ce bayan dogon jiran nan da yayi yanzu ki neme shi ki rasa dan kawai kin ce masa yayanki na gari ya zamo zai ki daga kiran ki?, a yanzu kina nufin da hatta maganar da kike yi da shi msg babu ko? Bashi da gaskiya ne? Ko bayan nuna masa rashin sanin ciwon kanki ta hanyar nuna masa ke baki da wata tarbiyyar da zai mutunta ki ta hanyar bijirewa maganar wanda ya san tamkar uba yake a wajenki kika ci gaba da ganinsa matsayin saurayi harda kimarki kika zubar a wajensa?, FARHANA kanki kika bashi hala?......."

A zabure A'isha ta dubi HALLAH, sannan ta kalli FARHANA.......

FARHANA da ta fito da ido rai bace ta ce" Ki daina neman yi min abinda da yawa ke min wanda ya sa na karba na hadiye har na ji har cikin zuciyata cewar na yarda da hakan, kuma zan rayu da haka , na ajiyewa zuciyata bani da wani abu da zan iya zuwa da shi gidan miji saboda ba zan taba samun tausayi da riritar da wasu zasu samu ranakun aurensu ba saboda ana yi min kallon da na aminta da hakan na barsu da ALLAHNA da nauyin zato irin na kara min sharin zina Nur!, kar ki fadi abinda zuciyata zata yi nesa da taki Nur"

A'isha dake neman rikicewar ganin kamar zasu daku a sanyaye ta ce" Aya dan Allah kar ku yi fada kun ji? Dan Allah ku bar maganar"

Nur da itama yannayinta yayi sanyi tana duban Farhana ta sake kamo hannun ta

FARHANA ta doke hannun nata saboda hawaye ne ya bale mata, wanda ta jima bata yi ba a gaban kowa, wanda take ta rikewa lokaci mai tsayin gaske, wanda ciwon zuciya ke sakawa ta ji kamar zuciyarta a kumbure take, wanda ya sa du kauna irin ta kaka da jika ta ji kaunar Tata kakar ta wanke tatas a zuciyarta a duk lokacin da zata dubeta a gaban mahaifiyarta tace da ita fatan bata kawo musu dati ba, kuma fatan bata kwaso musu wata jarabar ba!

Still nur ta sake rikowa a hankali ta furta" ki yi hakuri, ba ina danganta ki da zina bane, ko daya, a tunanina in har kin ci gaba da jan zaren ki yana bin ki yana son ki da aure, idan ya ji yayanki ya sake zuwa zai yi iya yinsa ne ya nemi manyansa a sake zuwa inda yake a nema masa alfarma saboda ke yake so, shi ne namiji , shi zai yi kokarin ba ke ba................, Farhana a ganina zai sake gwadawa ko zai dace ne ba wai ya daina kiran ki ba kamar wanda yake gudun a kama shi da wani laifin......., kin kuwa san cewa nuna masa da kika yi kina iya take maganar magabatanki kadai kin yiwa zamanku ila idan har maganar aurenku ta yiwun? Yaya za'a yi ki nunawa namijin da kike tunanin yin zaman aure da shi cewar magabatanki basu isa da ke ba?"

A yau kam A'isha duban Nur take yi da matsanancin mamakinta, tamkar ba ita ba......, kwarai da ake cewa kowace mace da kalar baiwar ta haka ne, ashe ita ke kasa barci da tunanin halin da Nur ke iya shiga idan ta kamu da soyayyar Anas? Ashe ita aikin banza take yi da hankalinta ke kasa kwonciya du idan ta tuna cewar Anas na iya hurewa kanwarta kune da kudi ya cuceta? Ikon Allah

Duda ta san cewa Nur mutun ce mai matukar kiyaye maganar iyayensu, domin ko a lokacin da mama ke ta kokarin hargitsa mata wannan darajar Tata ta kiyaye bacin ran abansu..... Da wani abin ya rude ta, har ta nemi ta wuce gona da iri sai kuma ta zubar da komai ta nemi shawarar ta koda fada zasu yi kuma dauka take yi idan ta fada mata

Ba zata manta ba ranar da mahaifiyar Anas ta zo ta yi abin nan, Nur rantsuwa ta yi da farko cewar koda sonsa zai kashe ta ta haramtawa kanta shi, domin basu da abinda saboda shi zata rufe idannuwanta ta shiga gidan da iyayenta ma basu yi daraja ba bale ita da nufin zaman aure, ta san har ta mutu ba zata yi daraja ba a wajen nan, da kyar Auntynsu ta yi mata tsawa ta hannata ta nuna mata ai ba shi ya zage su ba, kar ma ta saki ta nuna masa wani abin, Ama duda haka da ya zo da dare da aka ce ta fita cewa ta yi ji wata jarabar kuma....Ni du na tsane shi wallahi, gani nake yi kamar shi ne ya zagi su Mama....................

Bayan wannan a lokacin da na'imar nan ta zage ta da talauci cewa ta yi in sha Allah ba zata fito a tsatson iyayensu ba kuma ta ja musu zagi, Anas din ma ta yaye shi ɗan wallahi ba'a yi namijin da saboda shi zata rinka janyowa iyayenta zagi ko ta bijire musu saboda shi ba......, kwarai ta san ta wannan fanin fa yar uwar nata na bata mamaki, bale da mama ta shiga cikin wani halin rayuwa ta mayar da su gefe take ta kanta, ya zamo aunty na sake wanke mata kwakwaluwa a hankali a hankali da ilimin rayuwa, sai kawai ta sake karbar wani aji da akida mai kyau a cikin zuciyarta ta boye.......

A tausashe A'isha ta ce" Ikon Allah, NUR ke ce?"

Nur ta dauke kai ta mike ta kama abayar nan ta kwashe ta, hakan ya sa daga ita sai wandon dake ciki mai santsi da yar riga fara mai siririn hannu ta nufi wajen kayan FARHANA tana fadin" Ban ga abin tashin hankali a nan ba, ba an ce ki ce masa ya fito ba?, sai ki fada masa ai, sannan ki ji me zai ce, idan ma baki same shi a wayar ba ai ba zaki gaza sanin inda yake ba, sai mu dauki adaidaita mu tarda shi ai mu sanar masa......., sai dai ina mai tabbatar maki idan na ga zai kawo raini a lamarin Anna da Inna wallahi zan fasa masa kai, dan gaba daya Ni kaunar innar nan nake yi, kin kuwa san mu kakaninmu sun rasu? Yau na yi kaka , ko A'isha? Ke ma kina son ta???"

A'isha ta yi mumushi kawai tana duban FARHANA da ta dulmiya a tunani a tausashe ta ce" FARHANA, kar ki yi fushi da maganar NUR, ki yarda bata jingina maki zina ba, tambayarki ta yi dan ta san dalilin da yasa zai dauke maki kafa , ko bashi da waya ne?"

FARHANA ta girgiza kai, muryarta cen ciki ta ce" Ba matsalar waya bace, ya fi karfin waya"

A'isha ta ce" Sake buga Numbar tasa mu gani?"

Farhana ta dauki wayarta a hankali tana dubawa....., sai kuma ta dubi Nur ta ga ta saka wata yar sket dinta da ta wuce gwuiwa da dan yawa domin a gwuiri take, kuma iya kugu kadai ta ɗan rike, a bude take daga kasa, sai kuma ta saka riga itama budadiya ce kafin ta kirma hula ta zauna tana kallon mirror tana murmushi

Kai ta girgiza dan idan tace zata biye mata bata san in gidan nan zai ishe su ba, bari ta tabbatar mata cewar saurayinta na son ta sai ta biye mata

Numbar tasa ta shiga danawa kira, Ama fir ta kasa samu, sam bata ringin, bata shiga kwata kwata

A hankali ta dubi A'isha kasa kasa sosai ta ce" Ban taba aikata zina da shi ba, da kowa ma ban taba ba..........

A'isha ta dube ta da kula a hankali ta ce" Alhamdulilah, Ama me yasa ita take cewa kina yi???"

Farhana ta yi murmushi a tausashe ta ce" bana jin yin zina a raina kwata kwata, kyankyamin zina nake yi gaba daya, a raina nake jin idan na yi zina ai na gama wulakantar da kaina.....shin in na tashi na je na yi zina da me na sakawa Yaya da Anna da irin rikon da suke min????, "

Nur ta taho a hankali ta zauna tana duban ta .......a hankali FARHANA take shigewa c'en cikin zuciyarta, a hankali take yi mata wani kallo irin wanda take yiwa A'isha kadai a duniya......

A tausashe FARHANA ta ce" Rashin jin maganata yawo ne........., na san ina fita a gidan nan lokacin da na so, in shigo lokacin da na so idan yaya baya kasa..........., ina matukar jin dadin in ficewata in hadu da shi mu yi ta yawon gari ba tare da na yarda ya kai Ni gidansa ko hotel ba, sannan in yi yadda zan yi Inna ta san da shi nake tare.....dan kawai in kai ta bango tace ya fito a mana auren ko kuma in bata mata rai, ko in kiyayewa haduwa da ita.....saboda a raina nake jin na tsane Inna saboda yadda take yiwa mahaifiyata......"

Ta yi mumushi ta ce" Ban taba maganar nan da kowa ba a duniya........., ban taba yin ta da kowa ba......., kuma kun san wani abin mamakin? Baban rashin jin nan ya sa a yanzu ko Anna ba zata ce maki Ni FARHANA bana zina ba, dan du idan na fita na dawo Inna cewa take yi in yi wanka kafin in rabi Anna......, shin wani irin so zan iya yiwa matar nan?, a gabana ta tsani mahaifiyata haka kuma ta haɗa da ni..............ko ji take Ni na kashe mata d'anta ne?"

Ta karashe tana sada kanta wasu hawayen na biyowa a fuskarta, a hankali ta share gaba daya
Chapter 90 · 0% Book details