← Book details Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 141

Sashe 9

Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hum................tana yar tsamar nan ne da kakarta, mahaifiyar Marigayin mahaifinta.........
Sam basa shiri, basa shan inuwa daya, bale da muguwar akidar da aka san buzaye da ita na kin auren jinsin da ba nasu ba, wanda a yanzu haka wasun su ke rike da wannan akidar tamkar wata ta addini tsabar yadda suka bata mahimmanci.......ya kawo mata rigima ta kirki sakamakon saurayinta ita wanda ba buzun bane, ita kuma kakar Tata tace sai dai idan bayan ranta za'a yi wannan abin kunyar, shine ita kuma Farhana tace ba damuwa a yi hakuri bayan ran kakar Tata zata yi auren, dan ba gaggawa take yi ba, in dai ba za'a aura mata wanda take so ba lafiya lau ne zata jira.....

Wannan dalilin ne ya sa har yanzu bata yi aure ba, kuma bata da niyar yi, dalilin wannan hukunci na kakarta ta dauki muguwar akida ta hanyar bashi kafar kai kawo da zama abokan siri ita da shi wanda ya dace ace ya zama abokin sirin nan nata ne har sai igiyoyin aurenta sun hau kansa......sai ta fake da haka take tafka tsiyarta da zuwan su ne suke yi mata KISAN MUMMUKE ta hanyar hanata abinda take so, itama take mayar wa da kura aniyarta dan a duniya Mutun daya take tsoro, shi kuma Allah ya sa na dan kasa bane, idan ka ganta a gidan nan tabas ana jin kanshin zuwansa kasa kwana kusa.

Bata ji dari dari ba sai da ta shigo falon nasu ta samu mahaifiyarta zaune saman darduma mai laushin gaske hannayanta rike da Alkur'ani mai girma, fuskarta a sake sosai , sai dai ba dariyar ganinta take yi ba, a'a , fuskar ce koda ta so daurewa taushi da sanyin hali ke hannata zama turbuk din nan , koda cikin fushi take kuwa ba lalle ka ga fuska ta yi irin muguwar hadewar nan kamar an aiko wa da mutun da sakon da ya gigitashi ba.

Murmushi ta sakar mata a lokacin da ta karaso da sauri ta duka gabanta hadi da kama hannayenta a tausashe sosai ta furta" Anna......"

Murmushi Anna ta sake fadadawa da shi, a nutse ta saka hannayanta ta janyota jikinta tamkar wata Y'ar baby ta rungumeta a jikinta sosai a tausashe ta furta " Farhana, sannu da sauka....., yaya aikin? Yaya gajiya?"

"Mtssssssssssssssssssssssssssss!" Uban tsokin da ya fito daga dayan bangaren ya sa Anna sakin Farhana da sauri hadi da rike Alkur'aninta da kyau , da idannuwanta kuwa ta ringa yiwa Farhanan alamun ta daga mata kafafuwanta, Ama da yake yarinyar nan ba ji take yi ba sai kawai ta share ta yi kamar bata gani ba ta sake dora kanta a gefen kafar mahaifiyarta ta yi shiru , bata tashin ba, haka kuma bata gaisar da wace ta yi tsakin ba dan sarai ta san du duniya a yanzu itace kadai ke iya yi mata wannan takakiyar .

Kai Inna Hajiya ta girgiza tana duban Anmy ta ce" Tun farko daga gareki ta samu sangarta, a wajen ki ta ga raina ni, a dole a yanzu ta ci gaba da min kallon banza, sai ki umarceta ta tashi ta je ta yi wanka ko zata zubar da du abinda ta kwaso, kina saman salaya ne zaki yarda ta rabeki bayan kin san cewa ta dauki zina ba a bakin komai ba?, Allah ya kyauta!"

Daga haka ta juya ta karasa ta dana lft ya bude ta shiga ta dana matakalar karshe inda dakinsu yake , nata da na jikanta dan kuwa a shekarunta in ba dan hutu da ni'imar lafiya da wasun ke samu da shi ba da yanzun ko yar yatsa ba zata iya dagawa ba, sai dai cikin ikon Allah tana duduken nan take du masifar da zata yi, ta muryarta ba zaka taba gane shekarunta ba, sai dai idan ka ganta zaka yarda cewar shekaru fa sun ja.

Shiru ne ya wanzu a wajen bayan ta haura sama,
Farhana kanta a kasa tana tunani kala kala ciki harda yaya aka yi du aka kwashe mutanen kirkin famillynsu suka rasu aka bar wannan ? Ita kam du ranar da tsohuwar nan zata mutu sai ta fi kowa farin ciki

" Ki tashi ki je ki yi wanka ki yi sallar azahar lokaci ya shige tuni" mahaifiyarta ta fada a tausashe ba tare da ta ba yannayin fuskarta mahimmanci ba, gaba daya ma nunawa ta yi bata gane halin da ta shiga ba, hakan ya sa ta mike ta nufi lft din itama tana cire abayar dake jikinta ya rage dogon wando da yar riga a ciki ta bude ta shige sanan ta haura nasu bangaren, wanda a nan ma akoy dakin yayansu da na matarsa a falo na biyun dake saman, wanda ba cika aiki suka yi da shi ba, sai idan baya kasa in sun ga damar zuwa suke aiki da shi, shima ba kullum ba, dan bangaren su daban yake da na ANNA.

Murmushi Anna ta yi ta ci gaba da karatun da take yi a nutse ba tare da ta bari wannan yanayin ya hargitse mata farin cikin dawowar y'ar tata ba, ta sani ne kowani tsanani yana tare da sauki, kuma in Allah yayi duniya dan manzo wata rana sai ta ga Farhana a kan hanya madaidaiciya.

A gidan su Fa'iza

Kusan karfe biyu na rana Imtee ta gama yiwa fa'iza kunshin , dan ma bata da sauki ne da tuni ta gama shi, sai dai basu tafi ba saboda mahaifiyar su fa'izan tace su zauna tana zuwa, duda sun nuna aa tafiya zasu yi sai fa'izan ta nuna musu mamanta ba zata ji dadi ba idan ta zo ta tarar da sun yi tafiyarsu, a dole suka zauna din suka ci gaba da yar fira suna zaman dako har suka yi sallar azahar sannan suka sake jira kadan su gani, idan bata shigo ba sai su tafi kamar yadda Imtee tace.

Basu jima sosai da yin sallar sallar azahar din, sai ga yaya Anas ya dawo da tarin ledoji ya zube su a falon gaba dayansu sannan ya zauna hankali kwonce yana sake bin Imtee da kallon da ya sa ta ji gaba daya ta tsargu , domin du yadda ta so basarwa sai da ta gane ita din dai ne yake kallo da irin kallon nan da ya wuce misali

Dan tsaki ta ja kasa kasa wanda ya saka shi sake zarro ido yana kallonta kafin ya kalli Fa'iza da mamaki ya ce" Sister, da gaske alamu sun nuna zamana a nan na takura kyakyawar fulawar nan"

Imtee ta dan sake dubansa sai kuma ta mike tana gyara hijabinta da kyau, kasa kasa sosai ta dubi aisha tace" Ki sameni a gida"

Fa'iza da kunshinta ya bushe ne ta mike tana duban Imtee da mamakinta ta ce" Dan yayan nawa ya zauna da mu ne ranki zai bace? , Imtee yayana ne fa"

Imtee ta dubeta, a hankali zata yi magana, salamar mahaifiyarsu ta katse musu hanzari, shi kuwa ya sake gyara zama yana sakin murmushi zuciyarsa fari tassssss yana tunanin wannan ai ita ce ta dace da shi ba kowa ba, domin shi lamarin ta birge shi yake yi ma.

Amsa sannun da yan matan ke mata take yi kafin tace" A'a, yaya na ganku a tsaye, hala har tafiya ce? Fa'iza ina fata kin basu abinci?, dama nace su dakata ne dan yayanku ya zo in amshi kudin kunshin in bata, ƴaƴansu dan bani dubu guda ka ji?"

Da sauri A'isha ta dubi mahaifiyar su Fa'iza sannan ta dubi Imtee da ta ɗan yatsina baki alamun firar bata yi mata ba, sai dai bata nuna komai ba , ko dan ta ga baba ce mahaifiyar ta Fa'iza?

Dan murmushi ta yi ta ce" A'a mama, ai ba dan ta biya mu muka zo ba, kawarmu ce kyauta muka yi mata, zamu wuce mama mun gode"

Ai kuwa ta yi mamaki maman ta su Fa'iza, fa'izan kuwa sai alamu take yi mata cewar ta daina maganar kudin ama sai mamansu ta kai dubanta wajen Anas da ya ciro yan dubu dubu har goma yana miko mata ta karba tana zare daya da nufin tursasa su su amsa ne ta ji yace" Mama, dan Allah hade musu duka, su hau abin hawa, ba biyan su za'a yi kudin kunshi ba, ai.....a gaskiya......idan biyan za'a yi kudin sun fi haka ko Imtee?"

Imtee ta dube shi ido cikin ido a karo na biyu, bata ce komai ba sai kawai ta juya tana sake baza hijab dinta ta yi waje ba tare da ta amshi kudin da yake so lalle ta amsa ba

Kasa zama yayi ya mike da sauri ya bi bayanta, hakan ya sa suka bi shi da kallo su Dukansu

Da sauri ya sha gabanta yana kallon irin yadda ta ɗan tsorota na tare tan da yayi haka kikam

A hankali ya sassauta yannayin damuwar dake fuskarsa a tausashe ainun ya ce" Tun kafin ki san ni zaki fara tsanata?, me zai hana ki fara bani dama , idan kika san waye ni in bai maki ba sai ki tsane ni? Koda yake sani ne baki yi ba, idanma ke Bakya so na ba komai, Ni zan hade na mana so din na mu biyu kin ji kyakyawar flower......"

Tunda imtee take, bata san da ranar da zata zo irin wannan har zata tsaya haka kusa da kusa da namiji ta ji kalaman bakinsa har karshe ba, tana da farin jinin maza su nuna suna son ta sosai, sai dai bata da sakewar fuskar da zata ce musu koma meye bale har su samu damar haurawa wajen da take yawan tunanin cewar ba wata zuciya mai iya karbar so, dan akoy wani dan acaba da ya taba biyota ta ringa jifansa, ba shiri ya tafi yana tunanin ashe mahaukaciya ce?????
Ita fa, ta dauki cewa ba wani so a cikin zuciyarta, kai zuciyar bata da wani amfani sai wanda zata buga dan anfanar da gangar jiki, daga wannan ba wani, sai gashi lokaci daya ta ringa sauke dubanta a kan fuskarsa har ta samu kanta da jin kunya na son lulubeta............
Chapter 9 · 0% Book details