Sashe 77
Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta riko hannun Farhana tana dubanta ta ce" yaya zai yi tunanin bamu san abinda ake ciki ba?, ko dan ya ga ina dariya yana tunanin ban san abinda nake ciki ba? FARHANA bari ki ji irin rayuwar da na yi da mama, ...........tunda na fara wayo a duniya aka hargitsa min kwakwaluwata, ya zamo mahaifiyata da ta haife ni nake tsoro kamar wace zata dauki raina, bani da wajen dora kai in yi rigima sai a kirjin mama, bani da wajen da zan yi rigimar kudi ko kaya ko wani abin a mun nan take sai a wajen mama, mama bata kwabata bata hantara ta, bata duka na, bata zagina, bata matsa min in yi du wani abinda bana so, ..........idan wanka nace bana so haka zata ce in yi gurmazu in fito, idan wankin jiki ne ma haka......., tsakanina da mahaifiyata in ta ga wani abin da yake neman wuce gona da iri zata so tsawatarwa, a lokacin ne kuma mama zata nuna min na ga abinda take kwatanta min ko? Mahaifiyata bata so na, burinta ta ga baya na........."
Ta ɗan dakatar da maganar saboda yadda Aliyu yake kai kawo, nesa da su sosai, Ama kuma du idan ya juyo sai ya saci kallon su, wanda hakan ke sakawa tana jin kamar a takure take
A hankali ta ce" Shekara nawa na yi a cikin wannan halin? Goma sha tara, a cikin ta Ashirin din nan ce ake ta fito min da bayanan dake neman haukata Ni!, wai ashe gatan da nake ganin mama na min ba shi ne gata ba?, irin yadda ta daure min, sai abinda na yi, sai abinda na zaba da rayuwata , ba shi ne asalin gatan ba, ......umana da na rayu tare da ita nake tunanin na fi kowa saninta ce aka wayi gari yau da baban laifi irin na satar d'a, kuma ta sato ne dan ta yi me? Dan ta muzgunawa matar da ta rayu tana nuna min ita ce muguwa, ita ce mai bak'ar zuciya.............., ta sato yarinyar mutane ta rike ba dan har cikin ranta burinta kenan ba ta samu nata itama, a'a sai dan ta wulakanta matar da ta kwashe rayuwarta wajen nuna min mu ji tsoron ta, idan ta samu dama sai ta wulakanta mana rayuwa??????, FARHANA ace an yi tsaye da mama a gaban kowa an yi mata irin wannan abin, gaskiya ta yi hakinta, maimakun in ga nadama a fuskar mama sai kalaman da suka idasa fitar da Ni a hayacina???, FARHANA ina yin bakin kokarina dan in matsar da abin gefe Ama yace wai ban san abinda nake ciki ba???????..........., Farhana shin sai na fadi na buya ina kuka zai gane cewar mama ta gama rusa Ni.... ..........."
"Look at me !" Farhana ta fada tana rike hannayen Hallah da kyau ta girgiza ta sosai , kafin ta sake fadin"KISAN MUMMUKE PAGE 48 AND 49.................
Kasa kasa Farhana dake zaro ido ta furta" Anna na shiga uku, me nake gani haka????"
A lokacin Anna ta sake kai dubanta, a lokacin ne kuma NUR ta fito hankali kwonce da nufin karasawa wajen motar.........
Lokaci daya ya zarro idannuwansa yana dubanta, ......
Da gudu A'isha ta fito ta damki hannunta ta ja ta ciki da dan gudun da ya sa tana juyawa dukan abinda gudu ke iya motsawa suka motsa
Da sauri ya dauke dubansa ya maido kan Aliyu, sai ya ga Aliyu kasa yake kallo, sam shi Allah bai sa ya ga wannan mahaukaciyar ba ................
Hannunsa na dama ya kai wajen goshinta yana dafewa a cen cikin zuciyarsa ya ayyana ' Innalilahi wa Inna ilaihi raj'une.....'
Budewar Anna da fitar ta tana fadin" Barka da warhaka Malan Ahmadu, ya gida ya auntyn yaran? Dama su muka kawo kafin mu wuce gida ina fata sun same ku kalau"
A hankali ya bude idannuwansa ya sauke kan Malan Ahmadu,
A dole ya bude motar ya fito ya mika masa hannu suka gaisa kafin ya ce" Alhamdulilah jiki da sauki" Sakamakon tambayarsa mai jiki da Malan yayi
Malan ke ta kokarin su shiga ciki, sai dai kiraye kirayen sallah ya sa Malan din shiga da sauri ya daukowa samarin butoci, matan kuwa suka shige ciki dan gabatar da Allah, domin idan suka ce sai sun isa gidan zasu yi mazan ba lalle su samu sallar a jam'i ba
Wasu butocin auntyn yara ta ba su Anna, suka daura alwallar gaba dayan su sannan suka hau dardumar da tuni ta yiwa Aban yara shinfida da tabarmarsa mai tsafta da dardumar sa, ya zamo Anna ta fara yi kafin ta ba yan mata suka jirga dardumar suka kabbarta sallar su ma, auntyn yara kuwa tana gamawa a ɗakinta ta fito ta kawowa Anna ruwa a kwanon shan ruwanta mai tsafta , ga kanshin tulu gwanin dadi
Amsar ruwan anna ta yi a nutse ta sha sannan ta shiga bin gidan da kallo da hasken watan da ya haske gidan, ya zamo kana iya gane tsaftar mai gidan ko akasin haka, cikin ikon Allah kasar filin gidan tas tas take, takalma a kimtse a waje guda, tukwanen da aka yi daguwa an wanke an girke su an rufe, kwanoni a rufe ruf , komai a kilace a inda ya dace sai kanshin turaran haki da ya gama ko'ina Masha Allah
Suna gamawa suka yi addu'a, sai Salamar Malan ta tabbatar musu sun dawo
Anna ta mike tana murmushi ta dubi auntun yara ta ce" Aunty, mun gode Allah ya saka da alkhairi zamu wuce gida"
Auntyn yara tana murmushin itama ta ce" Anna mu muke da godiya, Allah ya kara girma........... Bari in taka muku"
Du sai suka nufo soron kofar a lokacin da Aban yara ke fadin" Na gode sosai Elhaji, na ji dadin wannan karamawa da kuka min, kuma in sha Allah ni ma zan muku ta gaske, da ikon Allah du lokacin da ake so ta je kawai a sanar min, Ni da kaina zan kai ta, haka kuma gobe idan Allah ya nuna mana daga makarantar su bi Annar ta su, dan su je su ga ita Maman, in ya so in ma a cen zasu kwana sai a sanar min, idan kuwa zasu dawo nan ne to sai a kawo su, bisa amana na yarda har zuciyata na aminta Allah ya taya mu riko ya bata lafiya"
IMAD yayi murmushi yana duban dattijon nan, sosai yayi tunanin dai sun kai ruwa rana shi da shi, sai ya ga ba haka ba, hasalima sai alkhairansa da yake gani
A tausashe ya furta" Na gode, Allah ya saka da alkhairi"
Daga haka suka yi Salama, su Anna suka nufi gida, su ma suka juya cikin gidan
Suna komawa Aban yara yayi kiran Auntynsu dakinsa na soro ya ringa bata baki a kan maganar dukan nan, a karshe dai ta yi murmushi ta ce" Ba zan dake ta ba abansu, Ama zan yi nata nasihar ta ringa kama kanta, gaba daya yarinyar Nan bata da nutsuwa abansu, ka taya Ni da addu'a dan Allah "
Daga nan suka shiga tadin kirkin mutanen nan da mamakin me yasa ake musu mugun kazafi irin wanda ake musu? Kuma sun shaku da mamakin yarinyar da ake cewa bin maza take yi a gidansu......, daga bisani Aban yara ya gabatar mata da kayan da ANAS ya kawo da bayanin abinda ya faru, hakan ya saka ta dariya ta ce" To Aban yara ai Ni bani da abin fada sai fatan alkahiri, sako kuwa yara su dauka su raba ma junan su, wanda aka ce namu ne kuwa mu raba in ajiyewa mama nata, dan Allah ka bi bayan lamarin maman yara, kishi ba abinda baya saka mutane, kuma ka ga ta dauki A'isha dan ita ma ta samu Tata ne, ka ga Aban yara idan har za'a dub......"
"Ki yi hakuri, idan muna magana kar ki kuma sako min maganarta kin ji?" Aban yara ya katse ta ya mike ya kama mata akwatin dan ya kai mata wajen yaran da kansa
A dole ta yi shiru ta dauki sauran ledojin ta bi bayansa.
A bangaren su Anna suna zuwa gida IMAD bangarensa ya wuce dan wanka yake son yi ya canza tufafi kafin sallar isha'i,
Su Anna ma suka nufi nasu ɓangaren bayan ta salami Anas dake jiranta cewar ya je gida ya huta ba inda zata je haka ma FARHANA.
Sunna shiga Anna zamanta ta yi a falo dan ta yi sallah kafin ta haye tana tambayar wace ta bari dan kula da ina halin da ina take ciki bayan ta ji yadda ta wuni, ta yi murmushi ta ce" Har yanzu bata kwonta ba?, bari in yi sallah in leka ta"
Daga haka ta zauna tana jan carbinta har lokacin sallah ya shigo ta mike ta shiga gabatar da sallar a nutse
Bayan ta gama sallah ta yi addu'a sosai ne ta mike da nufin zuwa dakin Ina ta ganta kafin ta je nata dakin ta yi abinda zata yi ta kwonta, duda ta san IMAD zai leko ta kafin ya kwanta , tana kyautata zaton su hade ma a dakin Ina
A lokacin da ta shiga ta samu ina zaune saman salaya tana sallarta a zaune, hakan ya sa ta duba wajen magungunanta ta ga ta sha su yadda take bata, ta duba wajen madarar da take sha da dare ta ga ita ma ta sha, komai da komai a kan tsari sai ta ji hankalinta ya kwonta ta zauna tana jira ta gama ta gaisheta kafin ta je nata dakin
Bata jima sosai ba ina ta salamce sallar sannan ta mike da kyar