← Book details Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 141

Sashe 24

Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ok, ba sai ta fada ba, daga yau ya gane cewa Anna shi ta haifa ba ita ba, ba zata iya yi masa kara ba

Maganar ciwon ta, da maganar tafiyarta in dai har Anna bata sani ba to fa bata da wata magana da zata fada da zata wanke kanta, a nan take ya watsa numbarta a Blacklist dan a yanzu ba zai iya sauraron ta ba ko kadan

Jikin MAZNA na rawa ta mike tsaye tana fashewa da kuka ta ce" Na shiga uku, yaya aka yi ya san ban sanarwa anna tafiyar nan ta Saudiya ba? Yaya aka yi ya san bata san na yi ciwon ciki ba????"

Jauhara dake cikin tiktok tana kallo ce ta mike da sauri tana rike ta ta ce" Aunty, kar ki fadi mana, menene wai? Me yake faruwa ne? halan ya gane Bakya Nijar?"

MAZNA ta rike ta da karfi tana sake saka wani kukan ta ce" Ban sani ba, ban sani ba, kin ga ina shigar da kira baya shiga, kin san idan ransa yayi mugun ɓaci yake saka Ni a Blacklist sai ya sauko yake cire Ni, dan ya san ba zan kyale shi da kira ba, gashi baya aiki da layika da yawa bale in tabo wani layin, wayo Allahna, ban san yaya aka yi ya ji cewar ban sanar mata na tafi Saudiya ba, da kuma karyar ciwon cikin da na masa ina yi shima yace bata sani ba, yanzu Ni Anna zata hada da mijina?"

Jauhara ta zaunar da ita fa kyau tana fadin" Zauna dai, ki daina wannan nishin da karfi kar ki karawa kanki wani ciwon......"

Sai da ta zaunar da ita da kyau a sanyaye ta ce" Aunty, kin cika zafafa soyayyar da kike yiwa big broth, Ni du sai in ga abin ya yi yawa......., Bama wannan ba anya kina gani anna tana da damar hada ki da mijinki kuwa? Kai bana tunanin zata Miki wani abu dan ta haɗa ku, saboda ai ba yau ake yin abinda zai iya sakawa ranta ya bace har ta haɗa kun, Ama ai bata taɓa wannan yunkurin ba, ina ga dai an yi Sa'a ne kawai ya ji, "

Ta miko mata ruwa ta kafa kai tana sha a gora

Ta ɗora da fadin" Ni ban san me yasa kike son yiwa Anna haka ba, sai ki ce ke ba zaki wani yarda wani abu na shakuwa ya haɗa ku ba, to wai idan bata shaku da ke ba ta shaku da wa?, um bama wannan ba to ai idan fushi ne ya yi kin ga ke ma ta kwana gidan sauki, kafin ya sauko ya neme ki kin ga mun koma gida ko????"

MAZNA ta zuba mata ido, a raunane ta ce" Kina tunanin ina iya zaunawa a nan bayan na san fushi yake yi da Ni har sai ya sauko? Ai ko in dami abokan nasa su hada mu a waya ko kuma in je in same shi ne, ba fa zan iya ina jin yannayin muryarsa a haka in yi ta zama har sai ya neme Ni, ke yana iya kin nema na har sai ya zo ma hadu, bale abinda ya shafi Anna ne fa, sam baya min da wasa a kan lamarin wannan maman nasa!"

Sororo JAUHARA ta yi tana kallon ta kafin ta gyada kai ta koma ta zauna a ranta tana ayyana ' lalle, wannan ai dole ma big broth ya ringa maki abinda ya ga dama, wannan shegen naci haka? Har shi namijin zai iya yin fushi ya kashe maki waya ke mace ke ce zaki je kina bashi hakuri? Allah karya ne, aikin banza Ni ba'a halicci namijin da zan nuna masa na fi sonsa da kaina ba, salon gobe ya nuna min ya fi son takalmin ƙafarsa da Ni ko? Hum....'

A bayane kuwa sai ta ce" Aunty, kin san ustazun mijinki yana da hakuri, zai neme ki ma ko dan ya ji yaya jikin ki, ke dai ki kwontar da hankalin ki, ki rike haka matsayin wata dama da zaki iya gama trtmnt din ki har ki koma gida ki samu annar ki bata hakuri, itace zata sa ya neme ki, kin sani sarai , Ni ban taba ganin mutun mai hakurin matar nan ba, Allah dai ya kara mata lafiya kawai...."

Shiru MAZNA ta yi tana ta tunani, ita kuwa ta komawarta tiktok tana ta shan dariyar fadace fadacen yan tiktok....., kai lokuta da yawa sai ta ga kawai ana cutar ta ne, irin yadda big broth ya saka dokar ko da wasa kar ya hango su a tiktok dan ba wani mutunci mace ta dauki kanta a ciki tana dirkar rawa, adininta bai lamunce mata haka ba, zata wulakantar da tarbiyyar ta, zata ci amanar ƴaƴanta, zuwa gaba sai ya zame mata baban abin kunyar da bata taba tunanin zata tardo irinsa ba a rayuwa, kai da an ci uwar sabada da ita, to ta san idan ta taka dokarsa tabas zai sani ne, kuma babu wanda ya isa ya shiga tsakaninsu da ita.

*NUR*

Tunda aka tashi daga makaranta take boye kusa da kofar office din Anna, du Wanda zai shiga sai ya ganta, haka du Wanda zai fito, anna kuwa dake ciki a zaune tunda ta hango ta murmushi kawai ta yi, bata ce da ita komai ba, ta ci gaba da aikinta ɗan a yau ta samu visit din iyayen yara sosai, wasu suna so su saka ƴaƴansu, wasu kuwa ya'yan nasu sun kai musu bayanin ire Iren gyaran da ake yi da sauran su , shine suka zo dan jin abinda yake faruwa da tsoron kar aje ko kudi aka kara musu na karatun yaran? Wasu kuwa sun riga sun sakawa zuciyarsu ko nawa za'a nema a makarantar sai sun biyawa yaran su saboda a gaskiya a zahiri suke ganin irin yadda yara ke ɗaukan karatu a makarantar, sai dai godiyar Allah, kwarai ana samun ci gaba

Tana nan Rabe Farhana ta karaso cikin shiga irin ta abaya baka sidik da nikaf , ta dan dakata ganin mutun rabe kafin ta bude ta shiga da Salama ta karasa saman kujera ta zauna tana sauke ajiyar zuciya hadi da cire nikaf din a sangarce ta ce" Gaba daya makarantar nan yan saka ido sun yi yawa anna, ga kauyancin tsiya, tunda na shigo suke kallo na, ban san Bama me suke kallo tunda na rufe komai , da zan shigo nan ma kawai sai ido hudu muka yi da wata budurwa itama ta tsareni da kallo, wai da na kalleta irin yadda ta kalle Ni sai kawai ta sauke harara kasa, fitsararun banza fitsararun wofi....."

Anna ta gyada kai tana sakin murmushi ta girgiza kai ta ce" Ke kam Allah ya shirye ki, ama wace ke kofa ba ke ta ƙalla ba, an dai yi katari kin kalleta ta kalle ki, waje na ta zo"

Farhana ta kalli kofar, ta kalli Anna,, har zata ce to me take nema a waje, sai kuma ta share tana fito da kaffafuwanta masu dauke da dogon wando mai santsi ruwan kasa , wanda ya saje da fatar jikin ta sai ya zamo ya mugun lafewa kamar ba komai a jikin nata, a hankali ta ce" Anna, plz ki sa baki a harkar course din nan nawa....., dan Allah ya bar Ni in je in karo karatun nan, duka duka bai fi shekaru uku ba fa zan gama karatun......, dan Allah ban so ya zo ina kasar nan, gashi ya sa na dadako na dawo ashe Bama yanzu bane zai zo, Shikenan duniyar ta min zafi, ga kakarsa a gidan cen ta hana Ni sukuni, jira take ta ga na fita ta min Shari, ga wannan idon nasa ta biyu wace ko baya nan ita tana nan , itama na san son da take nuna min na a min wayo a san me nake ciki a Rayuwa ne dan idan ya zo ba sai ya sha wahalar sanin me nake ciki ba, Anna ya dace ki kwata min y'ancina tun kafin su fitar maki da Ni a hayacinnnnnnnnnnnnnnnnnn

Bata idasa maganar ba yanzu kam IMTEE ta buga da karfinta Sannan ta murda ta shiga, saboda ai haka ta ga ana ta yi, du wa'inda suka shigan nan haka ta ga sun yi kafin su shiga,

Rai bace Farhana ta dubeta ta ce" Ke kuwa mahaukaciyar ina ce da zaki mana irin bugawar nan? An gaya maki kurame ne mu?????"

IMTEE da mamaki ta Dubeta ta ce" Sai dai a Dube Ni a Dube ki a gane mahaukacin, tunda har kika iya yiwa mutun magana da zagi bayan baki san shi ba!"

Ido Farhana ta zaro tana mikewa ta nuno Hallah da hannunta ta ce" Ke Ni zaki cewa mahaukaciya? Ni sa'arki ce?"

"Ki yarda ki taba Ni ki ga yadda zan lalasa ki a wajen nan!" HALLAH ta fada da karfin itama dan wallahi ba zata kyale wannan figagiyar ta zageta ba, aikin banza ta san halin da take ciki ne? Tunda safe da ta zo take zagayen office din nan ta kasa shiga, tunda aka sauka kuma A'isha ke jiranta tace mata kashi take ji, ta zo nan take sake yin wani zagayen kamar barauniyar dake sando ta dauka, a gabanta du wa'inda ta rigaya suka shiga suka fito ita bata shiga ba, shine itama zata zo yanzu yanzu ta shiga har ta nuna mata zafin kai, yau zata kifata a kas idan ya so sai su yi irgen shekarun daga baya!

Anna da ta zarro ido harda sakin baki tana kallon su ne ta ce"

*JAMA'A NAZOMUKU DAWANI TSARI NASAMUN KUDI TA HANYAR AMFANI DA WAYAN HANNUNKU
WANNAN TSARIN SHINE METAFORCE

MENENE KASUWANCIN METAFORCE* ????

*Metaforce kasuwancine ingantacce halattacce Wanda yake biya 100 💯 Wanda ake Gudanar dashi da wayar hannu,METAFORCE is also a part of network marketing,is a 100 percent decentralized project da aka daurasa Akan Blockchain technology Wanda babu wani mahalukin daya Isa YAYI editing,hacking ko deleting wani abu acikin sa,Kuma yanada matakai yanada rassa Wanda kowane reshi ka rike a METAFORCE to ka samu GUDUMAR DUKAN TALAUCI*🌎

METAFORCE ANASAMUN KUDI ACIKINSHI SOSAI MATUKAR ZAKAYI ABUNDA AKEBUKATA
Chapter 24 · 0% Book details