Sashe 11
Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A'isha tana dubanta ta ce" aya, aya, dan Allah kar ki mayar min da farin cikina ciki, ke kin san matar cushe ce bata daraja ba wace ake bi ba, ba ruwanki da yan matan anguwar nan, ke du inda namiji yake ai yaya Anas ya kai, gaskiya Ni yau farin cikina ban san inda zan iya kai shi ba, duba ki ga yadda yake maki barin kuɗi daga farawa da iyawa, saura ki koya masa kin amsa idan shi din mijin ki ne in an daura kuma ya ki baki, dan kuwa yawancin lokuta mu ke janyowa kanmu da iya yin tsiya mu ɗorawa kanmu fitinar da ta fi karfin mu, kudaden nan fa sun kai dubu talatin kika ki amsa......"
Wani irin dokawa da kirjin maman yara ta yi sai da ta ji kamar jiri zai debeta ya buga da kassss
Da sauri ta rike garu ta rintse ido tana fitar da numfashi har ta ji zuciyarta ta saku sannan ta yi motsin da ya sa suka gane da mutum a ciki, ai kuwa nan da nan sai suka bar firar, ya zamo ma ita A'isha ta fice dan tara ruwan wanka, ita kuwa Imtee ta shige ciki ta shiga yiwa mamansu ɓaci irin na sangartar nan wai ita auta.
Cijewa sosai mamansu ta yi bata nuna musu komai ba har ta haɗa kayan girkinta tace su zauna ta musu su ci, suka zauna din kamar yadda ta saba musu ta gwammace ace aiki zai kasheta da ta sa su dauke koda tsinke, dan kuwa zata yi bakin cikin ace sun taya matar babansu aiki koda da sanu ne bale har a kai su kama mata aiki dan ta huta.
Tana jan jiki da girkin nan har sai da suka yi sallar isha'i ta zuba ma kowa ta saka suka dau nasu suka shige dakin su, tana nan zaune ta kasa ta tsare , auntyn yara bata zo ta dauki nata abincin ba, hakan ya sa ta sake shaƙar wani bakin cikin zuciyarta kamar zata fashe dan tunanin ta ya gama bata cewar kudi ne da ita shi yasa bata ringa kai kawo tana dakon a gama abinci ta dauka ba, gayanan har ta yi ta gama bata dauka ba
A haka malan ya shigo ya sameta da fitilar kwoi a zaune ta haske mata inda take.
Karamar tabamar da suke shinfida masa ne ta shinfida masa sannan ta kawo masa abincinsa
Bayan ya saka jalabiyar zama a gida wace ta gama mutuwa murussss ya zo ya zauna a hankali sannan ya bude kwanon abincin yana amsa gaisuwar da take masa sannan ya dan dubeta ya ce" Yau lafiya kuwa ba'a kai mana abincin rana ba Sai kwado Sulaimana ya mana muka ci?"
Maman yara ta tabe baki cikin duhu ta gyatsine bakinta sannan ta dube shi ta ce" Na yi girkin kuwa, bai zo ya dauka bane kawai dan ya ja min fushin ka, sulaimana na kara girma kishin mahaifiyarsa na sake kama zuciyarsa da gasken gaske, sai dai Ni Allah na rike ba kowa ba, na tabbata zai min maganin komai....."
Ya dakatar yana dubanta dan yana son gaskata zancen ta
Gannin hakan ya sa ta sake gyara zama tana sauke ajiyar zuciya ta ce" Ka duba ka gani, ita din da kanta haka na ajiye mata na rana, sai daukewa na yi na bada sadaka, ga kuma na daren nan shima zai kai wani lokacin bata dauka ba, malan idan wani abin dadi kake bata a daka tana ci ya sa bata kula kwanonta ranar girka na sai a sanar min in fasa cire rabonta, in kuwa a tsayin zaman da na yi da ita shekara ashirin da daya har yanzu bata yarda da Ni ba ko kuma tsoro take kar na zuba mata wani mugun abin shima sai a sanar da Ni in sani, tunda kana gani, bata kiran ya'yan nan cin abinci sai ta ga bana nan, ta zuba musu abinci daga ita sai su ta yi ta nuna musu Ni din nan makiyiyarsu ce, ama da ace kiyaya nake yi da su ai da ban rike IMTEE har tsayin lokacin nan a hanuna ba, Ni ce kashinta, Ni ce fitsarinta, yau in Rahama bata gode min ba ai gani nake na wuce ta zage Ni, ta zarge ni ko kuwa ta wulakanta Ni ko?"
Har ga Allah sai da gaba daya abincin ya fice masa a rai, haka kuma sai jin zafin auntyn yara ya sarke zuciyarsa
Shin yaya zai yi da ransa ne?
Da ace yana iya hakura da auntyn yara da ya jima da sawake mata , ta yadda zai samu hutu a zuciyarsa da cikin gidansa, saboda fitinar da kullum ta Allah zata hadasa masa a cikin gidan nan, sai dai kashhhhhhh, a yau idan ya rabu da ita ya tabbata hatta nutsuwa irin ta gangar jiki sai dai ya gani a mafarki ba dai a tare da maman yara ba....., to maman yara fa tsakaninsa da ita yanzu sai dai su yi fira irin wannan, tuni ta sahalema kanta lalurori masu saka shakuwa tsakanin mata da miji, tuni ta ajiye diyoyin dake kanta.....to maman yara ai ta yaranta kawai take, shi kuwa har ga Allah har yanzu da dan saura, dan wani lokacin idan lamarin ya juyo masa tamkar mai shekara arba'in haka yake jin kansa, kuma mai daukan lalurar dai auntyn yara ce, ita kuwa zuciya da kwalafa wa abinda take so yake sakata a shauki
Kai, shi bai ga meye auntyn yara ke nema a duniyar nan ta rasa ba
Shin tsabar godiyar Allah ce ya sa take so dole sai ta bakantawa masu son ta, take iya jin dadi a ranta?
Daga shi har maman yara ai masoyanta ne na karshe a duniyar nan, Ama kuma daga shi har maman yaran bata bari ba da fitintunn yau da kulun.....
Rai bace ya daga murya yana kiran auntyn yara
Kirjinta na dokawa ta karaso ta duka da nufin gaishe shi ya dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu rai bace ya ce" Rike gaisuwar ki isashiya! Kiran da na maki dan in tambayeki ne shin Ni da hanuna na dau kwandala na baki ko kin samu hanyar shigo da kudin da bani da labari a gidan nan?"
Auntyn yara ta Dube shi, fuska a raunane sosai, dan wallahi ita yinwar da take ji ma ta isheta, jira take yi idan sun tafi kwonciya ta dau abincinta ta tura hakanan da wanda ya rage , dan ta tabbata idan ta bude kwanon nan abincin kadan ne ba zai isheta ba, shi yasa take jira in ya gama sai ta bi kwanukansa ta hade da wanda aka bata ta ci, dan maman yara bata cika bin ta kan kwanuka ba, sai da safe take wanke su bayan sun gama tsumama din nan
A sanyaye ta ce" Kudi kuma? Ni kuwa ina zan samu kudi? Na yi me da su kudin ma to?"
Yar yatsarsa ya nuna mata ya ce" Ki kiyayeni, Ni zaki tambaya inda zaki samu? Ki fada da bakinki tsakanin ki da Allah na taba ware ki na kawo maki wani abincin da zai sa ki ki cin na gidan nan?"
Zuwa yanzu auntyn yara ta gama gane mai aiki ce ta gama aikinta, dan haka sai ta ari hakuri ta sakawa zuciyarta sosai ta ringa ayana sunnayen Allah a cikin ranta
A sanyaye ta ce" Aa ko daya"
" To ki fada min dalilin ki na kin cin abincin ki, kina tunanin maman yara zata maki wani abu ne da zai cutar da ke?" Ya sake fada rai bace
Auntyn yara ta yi murmushi domin yawancin lokuta idan yana fada, tak da tak abinda aka kuno masa ne yake maimaitawa, dan haka a sanyaye ta ce" A'a fa, azumi nake yi yau, kuma ka ga da na sha ruwa sai kawai zazabi ya rufo min, tun Dazu ai jira nake ta leka ni sai in ce mata ta taimaka ta zubo min abincina a kwano in ci a daka, sai na ji shiru, na tabbata aiki ya mata yawa, maman yara banda lafiya shi yasa baki ganni ba du wunin yau, ki yi hakuri dan Allah "
Maman yara ta zuba mata ido da mamakinta, shima malam sai da yayi mamaki , dan a da takan fashe da kuka ne kawai ta nuna an mata kage, Ama yau ta amshi laifinta ashe ma bata da lafiya ne????
A sanyaye ya ce" Allah sarki, sannu auntyn yara, Allah ya baki lafiya, je dakin ki kwonta zan kawo maki abincin, ko kuma ita zata mika maki, zan sa sulaimana ya samo maki magani ki hadiya, Allah ya baki lafiya"
Auntyn yara ta amsa sannan ta mike ta yi ciki abinta,
Yana juyowa da nufin sanar mata ta mika mata abincin nata sai ya ga mama na wani irin abu irin na idan ranta a mugun bacen nan, tamkar kububuwa ta mike daga zaunen da take ta ce" Ba laifi, sai ka ci gaba da goya mata baya, Ama Ni kam ba zan kai mata wani abinci ba, ka yiwa matarka kashedin tsare min ya'ya tana kitsa musu munafurci, bana so, bana so a daina min , idan kuwa kunne ya ki ji, jiki magayi!"
Daga haka ta yi dakinta rai bace, hakan ya sa ya kame haba a ransa ya ayyana ' Ikon Allah, yau maman yara ranta a bace sosai, Allah ya sanyaya, bari Ni in kai mata, du tsanani ai za'a daga mata kafa tunda bata da lafiya, wannan yan ciwo na auntyn yara Allah ya sa mai tafe da zigege ne'