Sashe 110
Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shi dai bai ce komai ba har suka idasa shigewa, sai dai a yanzun IMAD dake gaba ne ya dakata a hankali yana kokarin kai dubansa wani wajen sakamakon abinda idannuwansa suka gani.........., wato Blackboard irin WA'INDA ake dauka din nan a gusa su ne aka kawo daya falo, dama AKOY su a gidan sosai saboda na makaranta ne........, ya zamo an girka guda a nan, Anna na zaune saman kujerar dake duban Blackboard din tana rike da litafi tana kallon NUR dake rubutu a jiki, wato lesson take yi mata tunda suka karya , domin bayan sun karya take tambayarta auntynsu, nan ta sanar mata sun wuce asibiti ita da A'isha, Ama ba zasu jima ba zasu dawo, a dole ta yi shiru bata ce komai ba saboda tunanin ita fa? Sai su tafi su barta?, karshe da Anna ta ga kamar hankalinta a dan tashe sai ta sa suka kamo Blackboard din suka sauko shi kasa suka shiga yi mata lesson, Inna kuwa dama tuni ta yi barci a saman doguwar kujerar falon....... Da yake hayaniya ba damunta take yi ba, sai suke yin lesson din su
Kasa kasa Abdul bassit ya furta" wauh, wannan angel din fa"
Kusan duka samarin banda IMAD da ya dan dakata sun karasa inda Anna take ne suna kai mata gaisuwa da tarin kauna da girmamawa...., ita ma fukarta a washe take marabatarsu cike da farin cikin ganin su ta mike tana duban IMAD hadi da bashi litafin dake hannunta na koyarwa ta ce" Lalalallaa, ANDADI kama litafin nan, plz yiwa yarinyana lesson, bari in kamawa Farhana saukar y'ayana, kai yau ina cikin farin ciki Masha Allah yaushe kuka sauka?"
Litafin da ya amsa Abdul bassit ke kallo, kafin ya mike ya mika hannu ya ce" Bani litafin in mata, Ni wannan ko Ni zan ringa mata daga yau? Anna wannan fa???"
Ya fada yana nuna NUR, wace ta juyo ita ma tana dubansu da kuma sauraran Yaren turancin da suke bajewa tamkar ba irin turancin da ta iya ba ita ma...., domin wannan kam mai zafi ne, haka kuma tana so ta gaishe su da turancin kunya ma ke hana ta bude baki saboda tsoron kar aje ta yi kwaba.
Rike litafin da yayi ya ja, bai iya amsa ba saboda bai sakar masa ba, hasalima da idannuwansa ya masa alamun ya zauna mana
Kafin ya kai dubansa inda take tsayen nan ya bi suturar jikinta da kallo
Bai ce komai ba ya karasa a nutse ya kama abin rubutun ya juya shi, ta yadda ya mayar da wajen rubutun cen baya, sannan ya Dube ta a tsayen da take tana kallon yadda da hannu daya ya juyar da abinda sai da suna nishi ita da Farhana kafin su iya fito da shi, da hannunsa ya mata nunin ta zagaya, hakan ya sa ta zagaya a hankali tana ta tunanin ta yaya zai yi mata lesson mutumen da baya magana daya bai saka larabci ko turanci a ciki ba? Ta yaya zata fahimta ita da ba komai take ganewa kai tsaye ba?
Cikin nutsuwa ya zagaya din shi ma, sannan ya tsaya dan nesa kadan da ita yana kallon rubutun da ta yi, abubuwan da suka yi ita da Anna, kafin ya sauke dubansa a kan fuskar ta
Ashe ita ma shi din take kallo cike da tunanin ta inda zata fara tambayarsa abinda Anna tace ta tambaye shi.........., wato maganar mamanta....hakan ya sa ta tsare fuskarsa da kallon da sai da kirjinsa ya buga a lokacin da ya Dube ta, kuma shi ma sai ya tsaida dubansa a cikin idannuwanta da duban da ya sa ta sada kanta a hankali tana fitar da ajiyar zuciya boyayiya.
Murmushi Abdul Fatah yayi yana shafa bayan kansa.....
Ikon Allah
Lalle da Mutalab yace shi da kansa baya gane abinda yake yi in dai abu ya shafeta ne haka ne?
Wauh.....shi sai abin ya zama wani sabo a idannuwansa
Abdul bassit kam dariya ke son kume shi, sai kawai ya bude wayarsa ya fada tiktok ya dano wajen abin dariya ya kuwa yi abinsa son ransa
Shi kuwa Mutalab du a kiyaye yake, domin ya sani ne idan har Abdul bassit ya so gigita masa tunani zai gigita masan ne hankali kwonce ....., dan haka sai ya kame kansa kawai yana so su yi su tashi su fita daga dakin
Mamakin sada kanta yake yi, gashin dake gaban goshinta kuwa shi ya fi zubawa ido.........
A hankali ya samu kansa da furta" Baki gaishe Ni ba fa"
Dagowa ta yi ta zuba wa fuskarsa ido....., a hankali ta sake dauke idannuwanta.......kasa kasa ta ce" Ban san da Yaren da zan gaishe ku ba......"
Bakinta dake maganar yake kallo, kafin ya dauke dubansa ya samu kansa da yin dan murmushi a hankali ya ce" Ba ki gaishe su nake nufi ba, Ni ne baki gaisheni ba Nur"
A yanzun kam da ta zubawa fuskarsa sai ta kasa daukewa.....
A hankali ta furta" Barka da safiya yayan FARHANA"
Ido ya dan fitar........, sai kuma ya yi dan murmushi iya lebensa kafin ya samu kansa da dan duba agogon hannunsa .........sai kuma ya maida dunansa kan alon dake gaban nasa yana sake dubawa a hankali ya ce" Read"
Hankali ta maida ita ma tana kallo.....a hankali ta karanta din, sai dai tana gamawa ta juyo tana dubansa gaba dayanta a tausashe ta ce" Dan Allah....., ka saki mamana, zuwa yanzu ta yi nadamar abinda ta aikata........."
Yanzu ma ido ya zuba mata da son gane asalin abinda ke hadasa masa faduwar gaba dan kawai ya kalleta sai kuma ya miko mata litafinta a hankali ya ce" Ba a haka za'a Miki koyarwa ba, zan cenza salon koyarwar ki............"
Daga haka ya juya da nufin zagayawa, dan ya ga shirun da aka yi a falon ma ko na menene, saboda tsitttt ko dai du sun fita ne???????
Yana juyowa dai ya ga abinda ya fi karfinsa, wato gaba daya har FARHANA bangaren nan suke kallo kowa yayi tsittttttttttttttttttttttt, Anna ce kawai bata nan, ta yiwu tana falo
Da mamaki ya budi baki zai yi magana a raunane Nur ta katse shi ta hanyar fadin"Page 69.....70
Cikin murya sansanya, mai fitar da amon yannayin rigima Nur ta ce" Ka tsaya ka ji mana dan Allah............"
Dakatawa yayi da saurin da bai san lokacin da zuciyarsa ta saka shi yin biyayya ba, haka kuma ya juya din yana tsaye a inda yake yana dubanta
Tahowa ta yi dan nesa da shi kadan, ta shiga murza idannuwanta a hankali ta ce" Dan Allah ka fahimceni, kuma ka yarda da bayanina...., zuwa yanzu mamana ta gane kuma ba zata kuma ba, ka yi hakuri ka janye fushinka ko dan shekarunta mana, yaya kake so ta rayu a gidan yari cikin wahala ne?......., kuma Ni kuwa yaya kake so in rayu a haka ne? dan Allah ka tausaya mata ka yafe mata, tunda bata cutar da A'isha ba, ai da sauki ko????"
Ta karashe a yanzun bata nemi kukan ba hawaye ya cika mata idannuwa
Anna da ta so fitowa kuwa, komawa ta yi kicin din ta shiga yanka fruits hankali kwonce tana murmushi
Idannuwansa ya lumshe a hankali kafin ya matsa daf da ita ta kusancin da ba normal ba, wanda ya sa ta nemi ja baya, ama ya hana hakan ta hanyar yi mata nunin ta tsaya
Wai ko dai yarinyar nan na dauke da baiwar dake iya Tsorata Mutun ko ta saka mutun abinda bai yi niya ba?.......
Abinda ya fi bashi mamaki irin yadda idan magana take masa yake jin dadin hakan har cikin ransa
Kasa kasa ya ce" Kuka zaki yi saboda maganar da kika san baki da wata gaskiya a ciki?"
A hankali Nur ta sake zubawa fuskarsa ido hawayen na kokarin bin gefe da gefen kumatunta, a sanyaye sosai ta ce" Ina da gaskiya, plz ka duba"
Ajiyar zuciya kawai ya iya saukewa kasa kasan nan ya ce" Ki fara duba halayanki, idan kika gyara sosai , sai in gani ko zamu yi firar......, now ki bude litafin cen ki yi karatu, zan ga idan kin iya da dare ok?"
Kai kawai ta iya gyadawa, haka kuma suka yi shiru na dan lokaci kafin ya sake juyawa
Yana juyawa FARHANA ta duke ta shiga tatare wayar Mutalab da ya zuba a nan, sai kuma ta ajiye tana zarro ido ta juya ta dauki hanyar fita ba tare da ta kara second daya ba
Mikewa Mutalab yayi ya bi bayanta yana yin dariyar rikicewar da ta yi, ya zamo su biyun nan ne kawai suka zuba masa ido kamar yadda ya zuba musu da alamun tambayar kallon fa?
Karasowa yayi ya zauna tsakiyarsu yana lumshe idannuwansa hadi da sake kai dubansa inda yan kaffafuwanta suke ta kasan blackboard din nan, tana dan wasa da su, tana buɗe su tana rufewa, wanda ke masa nunin ko karatun take yi, ko kuma tunani, sai dai ba'a ganinta ta koma ta boye....., haka kawai yake ji a ransa ya dace ya bata damar da zata koyo rufe jikinta ko dan darajar annarsa....., kuma a hangen sa bai ga wani kalma da zai fada mata da zata dauka da mahimmanci sama da ya dangana da mamanta......., Ama ai ita ma ta san ba ta yadda za'a yi ta sa ya saki barauniyar matar nan marar tausayi marar imani, to ita din banza ma zata sa ya saki matar nan? Ai ba zai yiwu ba!
Abdul Fatah ne ya Dube shi ya ce" me kenan?"
Shi ma ya Dube shi da alamun tambaya ya ce" A ina fa?"
Da yaran larabci ya ce" Kar ka min haka mana, wannan din budurwarka ce?"
Sai da Imad ya zaro ido tamkar ya ga wani abin sabo , da tarin mamaki ya ce" Astagfrullah "
Da wani mamakin Abdul Fatah ya ce" Astagfrullah?, sabo na yi?"
IMAD ya Dube shi ya ce" Wannan ai kusan haka, haba kai ma, ya zaka fadi kalmar dake tafe da kalar saitin raini ?, hum plz ku tashi mu je wajen Uncle AKOY maganar da zan yi da shi!"
Murmushi Abdul bassit yayi ya ce" Kana nufin ba budurwarka bace, kuma baka son ta?"