← Book details Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 141

Sashe 5

Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Yan Naija Mutanen mu 1k ne a kan wannan account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank* sai a bani shedar biya ta layi na kamar haka +22793811618

*Yan Nijar mutanen mu zaku turo da hoton kati ta airtel ta dala dari , wato 500francs cefa a kan Numbarna kamar haka +22793811618*

*Na gode, sai kun zo.....taku ce SAJIDA NIJAR*

Tallah......tallah .....tallah....

*JAMA'A NAZOMUKU DAWANI TSARI NASAMUN KUDI TA HANYAR AMFANI DA WAYAN HANNUNKU
WANNAN TSARIN SHINE METAFORCE

MENENE KASUWANCIN METAFORCE* ????

*Metaforce kasuwancine ingantacce halattacce Wanda yake biya 100 💯 Wanda ake Gudanar dashi da wayar hannu,METAFORCE is also a part of network marketing,is a 100 percent decentralized project da aka daurasa Akan Blockchain technology Wanda babu wani mahalukin daya Isa YAYI editing,hacking ko deleting wani abu acikin sa,Kuma yanada matakai yanada rassa Wanda kowane reshi ka rike a METAFORCE to ka samu GUDUMAR DUKAN TALAUCI*🌎

METAFORCE ANASAMUN KUDI ACIKINSHI SOSAI MATUKAR ZAKAYI ABUNDA AKEBUKATA

zaku iyahada miliyoyin kudi aranadaya acikin wannan kasuwanci me albarka in sha Allah

Duk wacce tashirya zata iya tuntubanmu akan wannan number
09136899615
Hajja Data
*3*

A hankali ta shige din itama, takalmin dake kafarta slipas ne, hakan ya sa ana iya ganin duk wani abu dake kafar hatta abin da ta shafa wanda in dai mutun na sallah baya shafawa, ga kumbunan kafar tata du sun yi zako zako

Kai mama ta dago tana amsa Salamar ta cen ciki itama kafin ta dan zuba mata ido tana binta da kallo har ta dauki hanyar dakin maman yara

Dauke kai mama ta yi zata ci gaba da aikinta ta ji alamun tsayuwar mutun daf da ita sosai

Sake sauke dubanta ta yi a kanta, sai kuma ta zubawa fuskarta ido da irin yadda take ta murza yan yatsunta ama ta kasa budar baki sau daya jal ta yi wata maganar kanta tsaye zuwa gare ta ita mahaifiyarta

Ajiyar zuciya auntyn yara ta sauke bayan ta gama yarda cewar sai fa ta yi mata magana zata iya yi itama, dan haka a hankali ta ce" wani abu kike so NUR?"

Idannuwanta ta dauke a hankali tana jin irin yadda kirjinta ke wata irin harbawa du idan ta kusanci mahaifiyarta....., haka kuma tsoron ta take ji kamar me, to ai mama ta fada mata kar ta ringa matse mata waje wai da tana jaririya akoy lokacin da ta nemi wurgar da ita cikin rijiya dan tsagwaron tsana, dan haka a hankali ta ce" Ba komai......"
Sannan ta ɗan ja baya idannuwanta na cikowa da kwallah

" Ya dace ki daina shafa pentin nan a kumbunanki, ina ganin kin san cewa haramun ne shafa shi, ko Bakya sallah ne Nur?"
Mama ta karashe tana saka tabaryarta ta shiga daka a hankali , hankalinta na kan yarinyar nata, sai dai bata nuna hakan a bayane ba

Samun kanta ta yi da zuba mata ido bayan ta dubi kumbunan nata, eh kwarai ta san cewa haramun ne , hatta tara kumbunan haka ba kyau, to ama ai mama ce ke cewa su yara ne, ba wata damuwa, shi yasa take siya mata ita kadai du ire Iren abubuwan nan, saboda bata ba yar uwarta su.

Juyawa ta yi ta nufi dakinsu , bata cewa mahaifiyarta komai ba, haka kuma yanayin mahaifiyar nata ya tsaye mata a rai sosai.

Bayan ta zauna maman yara ta dubeta ta ce" Me kika je yi wajen matar cen? Wato ba zaki daina matse mata waje ba sai ta ilata min ke ko?, menene take fada maki? Ko fadan da ta saba da wulakanta min ke din da ta saba ne take yi? ........kai Ni kam ina ganin tashin hankali da wannan baiwar Allah, koda yake wanda ya ajiyeta zai dawo ya gama yi mana tsakani da ita, ta fita harkarki kawai bana so, ta bar min tunda ta haifa tace bata so Ni ina so, dan haka ba wanda zai takura min ke in dai ina raye!"

Da farko bata yi niyar bata amsar tambayar abinda ta je yi din ba saboda gaba daya jikinta a mace yake, sai dai da ta ji tunanin da Mama ke yi cewar auntynsu dukanta ta yi ya sa a hankali bayan ta cire hijabinta na islamiyya ta ajiye kudin da Mama ta bata da zata fita sannan ta karasa wajen kwondon dake dauke da kayan kwaliyar A'isha ta duba ta ciro reza a hankali ta ce" A'a, tuna min ta yi rashin amfanin shafa abin nan ga Musulmi koda kuwa bana sallah"

Daga haka ta shige ciki ta zauna a hankali ta shiga yanke akaifun kafafuwanta kafin ta shiga kankarewa tana cire pentin da ta shafa musu da kuma datin dake jikinsu.

Maman yara ta jima a zaune a inda take,
Ganin da gaske tashin hankali ne ke tunkarota ya sa ta mike ta ja abin rufa ta fice a gidan ba tare da ta sanar musu cewar zata fita ba, domin idan har ta kara wasu lokuta gani take yi komai na iya faruwa

Ita kuma auntyn yara girkin nan ta tsaya ta tsara, sannan ta dauko kwanoninta Samira sababi ta wanke tassss ta juye na malan ta kai ta ajiye ta kuma zuba na dakin maman yara ta kai ta ajiye .

Har zata fito ta samu kanta da dan dakatawa, a hankali ta ce" A'isha"

A'isha dake ciki ta mike ta fito tana duban auntynsu bayan ta amsa

A tausashe sosai auntyn yara ta ce" Barci kuke yi?"

A'isha ta girgiza kai tana kallonta

Auntyn yara ta yi murmushi ta ce" Na gama girki, ko na zuba mana mu ci tare?"

A'isha ta yi sororo, cike da tunanin anya kuwa? Idan suka ci abinci da auntyn yara Mama ba zata yi fada ba kuwa?, sai dai irin yadda auntyn yaran ta tsareta da ido irin na Imtee sai ta ji ta gaza musawa, domin wani irin launin ido ne da su mai saka a yi musu biyayya koda ba'a so,
Cikin shaku ta gyada kai sannan ta shige dan fito da imtee

Zuwa mama ta yi ta share karkashin Dalbejiya ta shinfida tabarma, a nata abincin ta zuba musu harda su jan ruwa ta kai ta ajiye tana jiransu da tunanin ta yiwu ba zasu fito ba domin kamar da wasa an kwashi minti ashirin da gayyatar da ta musu na cin abinci ama basu fito ba.

Har ta cire rai da fitowar tasu ta hangi sawayensu, A'isha na jan hannun imtee da karfi kamar wace za'a kai bakin wuta tana dan tirjewa har suka karaso wajen tabarmar

A'isha ta fara zaunawa kafin ta ja hannun imtee da karfi ta zaunar da ita sunna dan yake

Murmushi auntyn yara ta yi ta zuba musu abincin sannan ta Dube su bayan ta fara saka hannu a hankali ta furta " Bismillah, ku taba mu ji girkin na yau, Allah ya sa ban yi faduwar murhu ba"

Ta fadi haka da dan barkwonci ne, tana hankalce da irin yadda imtee ke kallon A'isha da ta dauki abincin ta kai bakinta a nutse tana taunawa............

Har ga Allah yanayin kallon da imtee ke yiwa A'isha na jira ta gani ne idan abincin ba zai yi mata ila ba, domin bayan ta cin sai da ta dan taba gefen cikinta tana kallonta ta ga ta ci gaba da ci kafin a hankali ta saka hannunta ta dan diba ta kai nata bakin itama duk a tsorace dan a bayane yake a tsorace take.........

Ajiyar zuciya ta sauke a karo na biyu kafin ta ci gaba da ci ba tare da ta ankara cewar ci gaba ne ta yi da ci din ba ka'in da na'in dan dandanon girkin da dadinsa har sai da Salamar mahaifinsu da yayansu suka shiga kunnayensu suka dago a tare sunna amsawa, wanda ya dan ja yana kalonsu da mamaki, sai kuma wata annashuwa ta mamaye fuskarsa wace auntyn yara ta jima bata ga irinta ba lokaci daya ya nufo su yana amsa gaishe shin da suke yi a tare kafin ya dan dakata daf da su, shi kuma Sulaiman na hararansu daga nesa, Aban yara ya ce" Ikon Allah, yau me aka samu da dadi haka har inuwa daya ta hada ki da ya'yan naki?"

A dole ta ɗan tsare fuskarsa da ido kafin ta yi murmushi ta sada kai tana duban hannayen Imtee ta ga ta yanke akaifun, wani sanyi ya kara shiga zuciyarta har ta kara yarda cewa kwarai zuwa yanzu lokaci yayi da ya dace ace ta fara koyon zama irin na hakuri da dabara bayan sake nin'ninka addu'a dan ganin ta ci ribar zama da mutumen nan da kuma ƴaƴanta na cikinta dan ta gama yarda cewar abinda zai rabata da gidansa mutuwa ce , sai ko mummunar kadara, ya riga ya zama wajibin rayuwarta!

A hankali ta ce" Abincin ku na dakina, bari in dauko"

Aban yara yayi yar dariya ya ce" A'a yi zamanki, Ni ai in dai irin zaman nan zaki ringa yi da ya'yan Mama farin ciki fal raina, ina maman yaran take ne ? Na san yau itama hankalinta a kwance farin ciki fal ranta, Ka ga babban gida dauko abincin mu je mu barsu su ci gaba da zantawa tsakanin uwa da ƴaƴanta "

Baki Sulaiman ya tabe ya nufi ciki ya dauko farantin dake dauke da abincin nasu ya fito ya yi waje, haka shima Aban yara ya bi bayansa suka nufi kantinsa dan su ci tare da abokin aban yaran wanda ya kawo masa ziyara yau

Mikewa auntyn yara ta yi a tausashe ta ce" Idan kun gama, ku kirawoni in tatare wajen kun ji? Bari in barku ku gama....."

Haka kawai A'isha ta ga kamar bai dace ace sai sun kirayeta ta tatare ba, cike da jin nauyin magana da ita saboda irin yadda aka nuna musu ko waje kar su matse mata tana iya hautsina musu dukan wani farin cikinsu, aishar ta ce" A'a AUNTY, zamu tatare"

Aunty yara ta saki murmushi a hankali ta ce" Allah ya muku albarka, Allah ya tsare ku daga dukan sharin abin ki, Allah ya sa mu yi alfahari da ku a nan gidan duniya da kuma lahira "

Daga haka ta yi gaba bata kuma matse musu waje ba
Chapter 5 · 0% Book details