← Book details Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 104 OF 141

Sashe 104

Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Samun su ta yi a falo , su biyu suna cin abinci, Auntyn yara na ta jan carbinta, Nur kuwa ta zauna cen gefe ta cire hijabin ta turo baki, ga dukan alamu wata makar ta samu ko kuma fushin wace aka yi mata ne bata daina ba

Zaunawa Ana ta yi tana murmushi hadi da sake zubawa Nur ido, kafin ta kalli FARHANA ta ce" tashi ki kawo mana abincin mu ma mu ci da auntyn yara, kuma ina fatan kin fadawa su salamatu a gyara dakin dake kusa da nawa saboda auntynku?"

Farhana ta mike ta nufi hanyar kicin tana fadin" eh Anna, bari in kawo muku abincin ma sai in je in gani"

Anna ta gyada kai ta dake duban NUR a tausashe ta ce" Zo nan, taho nan yar albarka, hala sake cin zalinki aka yi?"

Nur ta taso ta dawo ta zauna daf da Anna tana dora kanta a gefen kafar Anna a hankali ta ce" Anna, Mamana nake son gani"

Anna ta zarro ido, ta dubi AUNTYN yara da ta yi kwafa da abin haushi haushinta, ta yi wani murmushin a tausashe ta ce" To ai wannan yayanku zaki gani, ki ganshi kawai ki masa kuka, na tabbata idan kika masa kuka zai yi wani abin kin ji?"

Nur ta daga dubanta tana kallon Anna kafin ta TURO baki tana girgiza kai ta ce"Anna ki fada masa dai, ki ce masa na yi alkawarin ba zata kuma yin abinda ta yi ba, a yafe mata a sake ta, idan ma kuɗi yake so in bashi sai in tara a rumfar Abanmu in bashi ya sakar min Mama, Ni ya tsane Ni Anna idan na fada masa hararana zai yi, ban yi masa magana Bama hararana yake yi fa"

AUNTYn yara kam sai ta rungume hannaye tana ta hailala tana kallon ikon Allah, ji take kamar ta janyo NUR ta yi mata dukan uku uku irin na jijiga mutun din nan, kai ikon Allah a gaskiya wasu lokutan idan ta ga irin halin da aka saka mata yarinya sai ta ji da wahala in har zata iya mantawa

Anna kam tana murmushi ta ce" A'a fa, idan ke kika fada masa ne ma zai gane cewar kin damu, kin ga ana cewa da sako gwanda zuwa da kai, in kika ganshi kika fada masa halin da kike ciki ki hada da kuka , zai ce shiKenan ki bar kukan hakanan, sai ya gani in kudin zaki bashi kin ga sai ya yanka, sai mu harhada mu biya shi ya bamu Mama ko?"

Nur ta yi dan shiru kafin ta gyada kai, kasa kasa ta ce" yanzu zan fada masa?"

Anna ta girgiza kai ta ce" Yanzu sai kin ci abinci, ki je ki yi wanka ki yi sallah sai ki huta, in sha Allah da safe kya fada masa, kin ga abinda yace sai mu yi aiki da shi ko?"

Nur ta gyada kanta tana murmushi , Auntyn yara kuwa tana ta harararta, har suka dawo dauke da abincin da suka zubo mararsa nauyi domin A'isha ta sanar mata ita Nur Bama ta cin na dare , haka take, auntynsu kuwa ta fi son ta ci da Yama, idan bata samu ta ci bane take cin na daren, ita kuwa bata da zabi ko wane ta samu tana so, shi yasa Aishan ta zubawa Nur dan abinda zata taba a plat, suka dauko na Anna da Auntynsu

Amsar nata ta yi tana zaunawa da kyau, wanda hakan ya sa wandon dake jikinta zuwa har saman cinyarta, saboda dama ba tsayi gare shi sosai ba, kuma budade sosai, du idan ta zauna da shi dama bajewa yake yi, sulaimana ya sha idan ya shigo zai wuce dakin auntynsu ya dauki takalmi ya seta ta ya cila mata sai a cinya, idan ta bare baki tana ihu mama ta fito ta shiga zage zage sai yace Walahi a kiyaye shi tunda ba KANWAR mutun ya taba ba, kanwarsa ya taba, kuma saboda zama da yan iskan kaya a cikin gidan nan sai ya mata sakin yan iska idan ya so sai ta zama full irin su.

Auntynsu ce ta Dube ta fuska a daure ta ce" Ke gyara zamanki mana"

Da sauri ta janye wandon tana gyarawa, Farhana ta gyada kai a ranta ta ayyana ' in dai kandalar Anna ce?, ai ba wani ji take yi ba, kuma Ni murmushin nan na Anna kuwa na meye wai?, bari dai in yi shiru dan kwanakin nan ta tsane Ni, kar in janyowa kaina wani abin'

A'isha ce ta zubawa AUNTY ta mika mata,

AUNTY ta ringa kallon abincin, a tausashe ta ce" Anna, shi din Malam din, zai samu abinci kuwa a cen din?"

Anna ta yi murmushi ta ce" AUNTY ai Malan zai samu abinda yake son ci, kuma idan ma ya ki ci zasu tursasa shi ne, kin san ki kwontar da hankalinki Auntyn yara , Allah ya taimaka an kai Malan asibiti a kan lokaci, in Allah ya yarda babu abinda zai faru da shi sai alkhairi, asibitin nan baban asibiti ne , suna matukar kula da marar lafiya "

AUNTY ta yi murmushi kafin ta fara ci a hankali tana duban Nur da ta gama da nata ta mike ta nufi kicin din nan ta darwaye plat din ta ajiye sannan ta dawo tana cire ribom din kanta hakan ya sa gashinta kwontawa a gadon bayanta sosai ta karaso tana sosawa hadi da yin hama domin barci take ji

Anna ta ce" Ku je ku yi wanka ki yi sallah, kar a manta addu'a sannan a kwonta..... FARHANA tare zaku kwonta ko kuma kin da a gyarawa kowace daki?"

FARHANA ta ce" Anna, tare zamu kwonta a dakina"

Anna ta yi murmushi ta ce" Oya maza ku tafi, sai mun hayo"

Da to suka amsa sannan suka wuce a falon, wanda Anna ta zuba wa Nur ido har ta bacewa ganinta kafin ta lumshe idannuwanta ta afka a tunani mai zafin gaske, tunanin da ya sa zuciyarta daskarewa da kai kawo..........., tunanin da ya sa ta so daga hankalinta a lokacin da ta tuna wacece MAZNA, me duniya zata ce da ita idan ta bashi y'a? Ita din Maznar me zata ce?, ita din Nur anya zata so shi kuwa???

" ki yi hakuri da halayyar Nur Anna, dan Allah ki yi hakuri, ina ta kokarin ganin ya zama koda kadan ne a yadda nake so, Ama sai a hankali, gaba daya yarinyar ta tashi da abubuwan da suke damuna, Nur nada rigima, fitina, ga rashin tsoro, har mamaki take bani idan tana fada da manya.......Allah ya shirye ta"

Anna na murmushi ta dubi AUNTYN yara a tausashe ta ce" Kai AUNTY, Ni kam gaskiya ki Bara min yarinyata hakanan , me ya yi ne?"

AUNTYn yara ta yi murmushi tana dafe haba ta ce" Anna, ni duba ki gani dan Allah yadda take son shako yaron nan, yanzu idan aka samu masalaha aka ce shi din ne mijinta ai sai kunya ta dame ta ko?, bata raga masa, tana iya yin fada da su Wanda ya taba ta, abin nan na damuna, rayuwa ai yar hakuri ce ko? Bale ga y'a mace"

Anna ta sauke ajiyar zuciya a tausashe ta ce" Kin san ko? Ki yi hakuri sannan ki ci gaba da godewa Allah, a gaskiya a irin yadda na fuskanta ba haka aka so Bama a barta......., Ni a haka ai ban ga wani laifinta ba, to ai Y'ar halal kenan ta bi kaidin mutuncin iyayenta ko?"

AUNTYn yara ta yi murmushi a tausashe ta ce" Dadina daya Anna, bata son duka, kuma du yadda ta ga eh da gaske raina ko na abansu a bace, zaki ga tana ta zagaye da son neman sulhu........, Ama kin ga, halayar kam? A gaskiya sai a hankali , ina fatan Allah ya ci gaba da gyara mana, domin ta samu horo irin na kisan mummuke ne, .......baki Bama zai iya furta wasu abubuwan ba sai dai zuciya ta hade, Allah ya sa ba'a kai ga mutunci ba, kuma ya sa ba'a ajiye wani abin a fada ba, shi ne kawai ribar"

Anna ta sake yin murmushi ta ce" AUNTY, kin ga HALLAH?, sai kin yi alfahari da ita.............., kwana kusa ma kuwa da yardar Allah "

AUNTY ta yi murmushi ita ma a zuciyarta ta amsa da Allah ya da, a fili kuwa sai ta alkinta alkunya.

A dakin Farhana wajen kwonciya fada ya laure, domin Hallah tace ita zata hau karshen gado, suka ce sai dai su saka ta tsakiya , ita kuma ta juya ta fice tana kumbura ta shiga neman dakin Anna, sai dai sam ta kasa tuna wanene kofar hakan ya sa ta bude wace ta gani ta shigewarta tana kumbura hadi da kuna fitila

Inna dake zaune bakin katifarta tana jan carbi ce ta dubo hanyar yana sake kankance idannuwanta dan ta samu gani mai kyau

Murmushi ta saki ta ce" To, kamar jikata"

Nur ta karasa tana murmushi ta zauna gaban Inna ta ce" kakata Ni ce, kin ga kuwa dama inda zan kwanta nake nema, wai koro Ni suka yi ba zasu bani karshen gadon ba, bayan ina iya fadowa cikin dare"

Inna ta washe baki tana shafa kumatun Hallah ta ce" wani marar tsoron Allahn ne? Allah na tuba karshen gado kuwa, je gayacen ki hayewarki, na baki shi ma gadon dan Ni kin ga inda nake kwonci , bana son hawa gadon yanzu"

Farhana ta saki murmushi ta dauki ruwan dake gaban Inna ta sha ta ajiye ta nufi bayi

Fitsari ta yi ta fito tana jan pant din da ya shige mata ta gyara sannan ta haye gadon tana baza hananyenta da kaffafuwanta tana murmushi ta daga murya ta ce" kakata kina ji?"

Inna na dariya ta ce" kwarai kuwa jikata"

HALLAH ta ce" gadon nan kuwa ai kin bar dadi kakata kin ji kuwa?"

Inna na dariya ta ce" To sha dadinki ke yarinya Bakya ciwon jiki ki more "
Chapter 104 · 0% Book details