Sashe 124
Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Daga haka ya fice ya fita ya mako kofar ya barta a nan a tsaye tamkar an zare mata rai .........................................domin a kalaman da ta ji daga bakinsa a yau, bata taɓa jin irinsu ba, bata taba haduwa da tsoro mai girman wannan ba........
A hankali ta silale a wajen, tana jin ta tsani kanta, ta tsani jikinta haka ma ta tsani halayarta................
A dakin Farhana kuwa, A'isha na rufe dakin FARHANA dake tsaye hannaye saman kai ta saka wani uban ihu tana karra duban NUR da ta yi suman tsaye
A guje ta karaso ta dauki hannayanta tana ihu ta ce" Na rantse ya furta, innalilahi ya furta, NUR, Nur kin gama min komai, dan Allah baki kalli fuskar yaya ba? La'ila ha illalahu, idannuwansa sun cika da kwallah, fuskar ta dau ja, kuma baban abin da ya birge ni a gaban mamansa lamari ya fito innalilahi yau na ga abu"
A'isha ta rasa zaunawa zata yi, bin FARHANA zata yi su yi ta zagaye, ko sumewa zata yi, sai kawai ta zuba wa Nur ido, a hankali ta ce" Auta"
Nur ta dago kamar an zaburar da ita ta zuba mata ido
Murmushi ta sakar mata a tausashe ta ce" Kin kuwa gane abinda yake faruwa?, Auta yaya IMAD ne ya zo , wajenki ya zo, yace yana son ki, yace ba zai yarda a aurawa Anas ke ba, Auta za'a ba Yaya IMAD ke........kin kuwa ji da kyau?"
A hankali ta rike hannayen A'isha, jikinta ya kwashi rawa mai yawan gaske, haka kuma kirjinta ya ringa bugawa kamar zai balo ta bakinta ya fito
A rikice ta ce" A'isha, ruwa , ruwa.....sanyi, sanyi nake ji.....A'isha na shiga uku wayo Allahna ku raka Ni wajen Auntynmu, ku taimaka ku raka Ni wajen Auntynmu"
Kamata suka yi, domin kwarai da gaske take ba wasa, kuma nan da nan jikinta ya dauki zafi, hakan ya sa FARHANA rikicewa har ta nemi zuwa ta sanar da manya, sai A'isha ta nuna mata a'a , su bata magani kuma su zauna kusa da ita, in sha Allah zata saku, haka dai suka zauna, Kan nur na saman cinyoyin Farhana, A'isha kuwa na rike da hannunta tana ta yi mata addu'a hadi da tambayarta me yake faruwa? Sai kawai ta girgiza kai, gabanta sai dokawa yake yi, gaba daya ji take kamar zuciyarta zata buga dan bugu da irin yadda take dokawa, haka kuma kamar da wasa suka ringa tsinkayo kiraye kirayen sallar la'asar, sannan lokaci daya aka buga kofar , a dole A'isha ta je ta bude, nan suka ga Inna tsaye ta sha doguwar rigarta ta leshi , fuskar nan washe kamar gonar auduga ta shigo da kanta dakin Farhana wanda Farhanan zata iya rantsewa bata taba ganinta a ɗakinta ba, da kula tare da matan dake tare da ita ta ce" Bismillah, jikokina ku taso mu koma dakina a kula da ku, ku taso maza.....jikata me yake faruwa baki da lafiya ne? Taso taso Ni dama na san ba haka kawai Allah zai diga min kaunar ki a raina ba, taso mu tafi Allah ya muku albarka, FARHANA zo nan, taho yar albarka taho in rike hannayenki, Allah ya Miki albarka taso"
Kasa tashin da ta yi da kanta ya sa matan nan kamata a hankali, haka kuma FARHANA daga zaunen nan bata iya tasowa ba, kawai kallon Inna take, ikon Allah har Inna ta zo ta kama hannunta tana dubanta ta ce" Taso mana"
Du sai take ganin abin wani iri, sai dai bata kiya ba, tashin ta yi jikinta du ba karfi suka bi su Inna suka tafi ɗakinta , gaba daya yau farin ciki Inna take ciki, sai dai Nur din kanta yau jikinta ba a sake ba, du yan matan sun yi la'asar, kowace kamar bata cikin hayacinta, Inna kuwa hakan ya fi mata dadi domin ba zata so ta ga rawar kai a tare da yan matan ba, jikin Nur da yake da zafi dai ya fi damunta, shi ma kuma ta murje mata shi da camfo sai kawai ta luluba mata abin rufa sannan ta ja kofar ta sauka kasa da ky din dakin, matan nan na mara mata baya..........
Tamkar daurin auren da aka ɗauki wata ana sanar da gayatarsa, tamkar daurin auren da aka jima ana shiryawa
Yan Magarya mota biyu suka zo da ita, dangi ne da abokan arzikin da yaya SULaimana ya Tarawa kansa a zaman da yayi tare da su, domin kuwa a lokacin da Malan ya sanar masa cewar a yau fa ake shirin ɗora masa darajar igiyar aure sai kawai ya ringa sanarwa mutanensa cikin farin ciki da doki, su kuwa suka nuna masa kara irin ta damagarawa suka cika mota biyu makil suka biya suka dauki Malan suka kamo hanya, hakan ya sa taron kara cika da jama'ar anguwa da kuma jama'ar su Malan
Duda abu ne na wayewa ke faruwa a kofar masallacin nan hadi da cikakken addini , bai hana uncle kara ji daga bakin IMAD a lokacin da suka zauna cikin Layin gaba gaba ba, da kuma yare mafi daraja wanda ya hana duban mutanen da basu iya ba gane abinda suka fada ciki harda Anas, wato tsantsan Larabci
A hankali ya tabbatar cewa shi yake so, kafin ya sada kai dan girmama duk wani wanda ya girme shi a wajen nan, ciki kuwa harda sir SAWIRIS dake kallo ta waya murmushi ya kasa daukewa daga saman fuskarsa
A nutse, aka gabatar da daurin auren nan a dunkule kamar yadda ake yi, wato daurin auren IMAD MUHAMMAD da HALLAH AHMAD, Sulaimana Ahmad da A'isha Rabi'u, sai FARHANA Muhammad da Mutalab SAWIRIS......., bisa sadaki mai daraja a gaban duban shedu, wanda daurin auren ya saka Anas gigicewa lokaci daya ya kalli wannan, ya kalli wannan, har ya zamo hankalin Aliyu ya kai kansa, a hankali ya janyo shi daga cikin mutane ya yi gefe sosai da shi , yana dubansa a yau da kula da kuma kiyaye haki na dan adam ya ce" Zuwa yanzu na san ka fahimci dalilin da yasa ba zaka iya yin aiki a duk inda matar sir take ba, zuwa yanzu na san ka fahimci cewar abinda mahaifiyarka ta ki aka taya ka yi mata biyayya aka saka katangar karfe tsakaninta da kai......, Anas na san kai mai wayo ne, ka san darajar neman ka, ina so ka kiyaye duk wani abu da zai iya hana maka nutsuwa a wajen aikin ka, ka yi biyayya, ka yi nesa da sir....., a yanzu ta zama matarsa.......kuma ina mai tabbatar maka shi ya nemi hakan ba ita ba....., hakan na nufin babu wani abu da zai nemi shiga huruminsa da ita ba tare da shi ma ya shiga nasa ba....., ko in ce, mu ma mun shiga nasa ba..........., ka je ka huta, ka yi hakuri ka sakawa ranka dangana, mu hadu a office gobe in sha Allah "
Daga haka ya dan daki gefen kafadarsa sannan ya nuna masa hanyar tafiya
Anas na kadawa ya karasa wajen motar da yake ja ya shiga da kyar ya iya kunna motar sannan ya taka ya nufi gidan su.
A masallaci kuwa, bayan daurin aure du waje aka nufa aka shiga kwasar girkin da ya zama odernsa aka yi daga tafkeken restaurant, domin du a cikin take away ne, kuma ba abinci kala daya bane, wanda ka dauko shi ne daidai da bakinka...., ya zamo bushasha sabuwa dal aka bude ana diba daidai gwargwado
A cikin masallacin, mazan nan biyar ne kawai suka rage, wato IMAD, ABDUL FATAH, ABDUL BASSIT, MUTALAB, da SULAIMANA wanda yake zaune cikin shiga ta lalausan yadi fari kal , sai kanshi yake yi, fuskarsa dauke da annuri matuka
Idannuwan IMAD ne suka sauka a saman fuskarsa, a tare suka sakarwa juna murmushin da basu san lokacin da suka yiwa juna ba
A hankali IMAD ya furta" kanwata ka aura?"
SULAIMANA ya gyada kai, a hankali shi ma yace" Ni ma kanwata ka aura?"
IMAD yayi murmushi a nutse ya dan shafa kansa kafin ya dauke dubansa,
SULAIMANA ya mike yana murmushi ya fita daga masallacin
Idannuwan IMAD na juyowa suka sauka a fuskar Abdul bassit dake dafe da haba yana kallonsa
"Meye?" Ya fada yana dubansa
Abdul bassit yayi dariya yana dafe kai ya ce" Mamaki kake bani, ashe ma ka magantu?"
IMAD yayi murmushi yana duban Abdul Fatah da ya kai masa duka yana fadin" Kai wai ba zaka bamu lafiya ba?"
A hankali IMAD ya ce" Ni da kaina ban san zan iya magana ba, sai da na yi na gane......"
Ya dubi Mutalab dake ta msg yana wani kada kafa da murmushi, a hankali ya ce" Ban san girman abin ba, ...........ban san haka bane"
Abdul Fatah na murmushi ya ce" Aliyu yace.........a irin tsarin matan da kake fadin kana iya aura......sam bata ciki?"
IMAD ya lumshe idannuwansa kafin ya Dube shi bayan ya bude ya ce" Bata ciki, ko a cikin maye ban taba tunanin zan so mace irinta ba............, hum"
Abdul bassit ya mike yana kade rigarsa kamar wanda ya zauna a waje mai dati ya ce" Ku tashi, a yau zamu amso yar Anna fa"
IMAD ya Dube shi da mamaki ya ce" Me kake nufi?"
Abdul bassit ya ce" Ina nufin a yau zamu kai ta gidanta, ku tashi mu je mu ga gidan ya yi, mu sa a gyara....tabasss a yau namiji sai ka shiga alfarmar buje"
Yanzu kam daga IMAD har Abdul Fatah Mutalab suka kalla da sauri, ganin bai dago ba ya sa suka kalli juna kafin IMAD ya damki hannun Abdul bassit ya yi gaba da shi, Abdul Fatah ya bi bayansu yana kara waiwayen Mutalab da jin dadin bai ji su ba......, sai dai suna fita Mutalab yayi nurmushi yana sake kada kafa kasa kasa ya ce" Zaku yi ku gama, alfarmar bujen nan nima zan fara ci daga yau har numfashina na karshe"............😁
ANAS tuki yayi na garari, cike da firgici da dacin zuciya da kuma shiga a tarin rudani mai zafin gaske
Ko kofar motar bai rufe ba ya shige gidansu yana dafe garu, kirjinsa ya masa nauyi , idannuwansa kuwa sun gama rufewa da tarin hawaye da tashin hankali