← Book details Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 134 OF 141

Sashe 134

Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mama ta yi murmushi a tausashe ta ce" Ba zata kiya ba, ita fa da kanta kullum jajenta bata ganin yaran........, takan ce shiKenan sai dai ta ji su a waya?, to tunda kace bata da lafiya fa take neman hanyar da zata ganta, yanzu kuwa tunda MUTALAB ya yi kira ya fadi maganar nan ta tardo Ni , tace dan Allah a dawo mata da ita kusa....., kar ka damu ko Mazna ina kyautata zaton a yanzu kam sun fara ganewa juna da Anna bale kuma y'arta, dama ita ta janyo har haka ya nemi shiga tsakani, yanzu da ta daidaita kanta har kiran annan take yi fa........., in sha Allah komai zai daidaita"

Kai ya gyada a hankali yana sauke ajiyar zuciya kafin ya afka tunanin maganar da suka yi da Likitar nan da ta yiwa Mazna aiki ma....., Likitar ta fada masa cewar idan ta zo ta yi mata hoton komai ta ga aiki yayi kyau zata bata Salama......, hakan na nufin zata koma gida , hakan kuma na nufin koda ba zai kwana da ita ba dole ya je bangaren ta ɗan ya bata nata lokacin ya kuma kiyaye haifar da wata fitina a tsakanin matan nasa.........., hakan na nufin zai fara raba kwana tsakanin su.............

Haka kawai ya samu kansa da duban wajen bayi, cike da tunanin ko yaya zasu kwashe?, sai kuma ya tabbatarwa kansa lalle ya zama wajibi ya mayar da ita cen, dan a yannayinta baya jin zai iya wuni bai ganta ba.............., haka dai suka gama fira da mama suka yi Salama, sannan ya mike ya tarda ita bayin ya fito da ita yana tsokanarta da faman fadin maman baby, ita kuma tana zuba nata kalar shagwabar.

Sai da yama ta yi, sannan ya nufi asibiti, kuma abinda yake bashi mamaki da ita a yanzu, sam bata bata rai ko wani time zai kai a asibiti, a yau ma sai da ta nuna tana son zuwa ta ga jikin nata, shi ne yace ta bari idan aka sakota zata je gidan Anna ta ganta

Yana tafiya A'isha ta zo domin sulaimanan bai shigo ba, kuma sai zuwa magariba zai shigo din, haka ma FARHANA dake gadin fitarsa dama sai kawai suka hade a falon Nur suka bude shafin fira cike da farin cikin lamarin, duda ita Nur kunya ke hana mata cewa komai, kawai haka ta ji kunyar na damunta kan maganar, sai ya zama su suke firar ita murmushi ne nata, har sai da suka cenza firar take tsoma bakinta

FARHANA da kula ta ce" Yanzu yaya kike ji game da maganar MAZNA?"

Nur ta yi dan tsai tana duban Farhana, sai kuma ta yi murmushi ta dubi A'isha wace a kullum take yi mata nasiha a kan lamarin da ya shafi Farhana idan ya zama su biyu ne kaɗai, hakan ne ma ya sa kwonci tashi ta mayar da komai gefe hadi da dagewa da addu'a har ta yiwa abin fahimta mai kyan gaske ta gama daukan mataki mai kyan gaske

A tausashe ta ce" Mene da ya shafi Aunty maznan?"

FARHANA ta ce" Kin ga yanzu sakinta za'a yi fa Nur, hakan na nufin zaku fara raba kwana dole da ita, yaya kike ji a zuciyarki?"

Nur ta yi murmushi tana gyara zamanta ta ce" Sumul kakal nake ji"

FARHANA ta dubeta kafin ta dubi A'isha ta ce" A'isha wani bin bata maki kama da munafukai yarinyar nan?, in ba munafurci na kina nufin Bakya kishin MAZNA?, to Ni a yanzu tsakanina da Allah in aka ce MUTALAB nada budurwa ma ina iya daukan makamai......bale ace wai aure zai kara min ko ace ya kara min"

NUR ta lumshe idannuwanta kafin ta ce" To ke da aka karawa ma kenan, bale Ni da aka dauko mata tana zamanta da mijinta?, ai a yanzu ita ce ta dace ma a rike domin gani nake yi ta fi Ni shiga wani hali.........., tana zamanta da mijinta an mata kishiya........."

A'isha ta dubi Farhana da ta dau salati, sai kuma ta dubi Nur

FARHANA ta ce" Wallahi haka ne, to Ama ke ma zaki ji zafin nan ko?"

Nur ta sauke ajiyar zuciya a tausashe ta ce" To FARHANA kishi ai halal ne, dole kowace mace ko yau ta hadu da wanda ta ji ita ke sonsa shi baima san tana yi ba Ama kuma ta ga yana da wata a rayuwarsa ta ji kishinsa....., bale kuma Ni da na zauna da shi har na gane waye shi a rayuwata........, to Ama idan har zan yiwa kaina adalci koda mutun ne marar mata kasancewar mu Musulmai dole zan dau komai da sauki ta yadda ko zata faru haukan nawa ya zama madaidaici, shi ma ku ne kawai zan yiwa ku tausheni a wuce wajen, Bama zan yarda wai shi ya sani ba , saboda idan ya sani gaskiya na bashi wata babbar dama a kaina wace zuwa gaba zai iya min dariya sosai a kansa......., "

Ta dan tsagaita tana duban A'isha dake mamakin furucin ta, ta ɗora da fadin" Idan aka sake ta yau, a yau zai dawo ya min salama, saboda dole zai zama mai adalci, kuma Ni zan taya shi zama haka........., dama na san yana da aure, na san haka zan tarar dole, sai idan ya tafi zaku kara rarashina saboda .......ban san ko zan iya barci babu mijina a kusa da Ni ba"

Ta karashe tana sada kanta cike da jin tarin kishin abinta a zuciyarta

FARHANA ta sauke ajiyar zuciya bayan ta rike hannun Nur itama kamar yadda A'isha ta yi a tausashe ta ce" Alhamdulilah, tunda har kika gane abin ta haka....., wai kin san da Anna ke ta fadin mu yi iya yinmu mu rarasheki?, bale yau da ta ji maganar samun karuwar nan, ta yi kira ya fi a irga, ........ashe dai y'arta ta yi wayo yanzu.......... Allah ya baku zaman lafiya, Allah ya sa ki ci gaba da ture duk wani abu da zai hadasa muku fitina.........."

A'isha na murmushi ta dan taba wuyan Nur din saboda hannunta da zafi ta ji da gumin kuwa dan haka ta ce" Amen, ki kwonta mana Nur, jikin naki da zafi, ba inda ke maki ciwo kuwa?"

Nur ta ce" Ai ina kwontawa zazabi zai rufe Ni, shi yasa na fi so in zauna din Indo......"

Haka dai suka yi ta fira tsakanin su...., yawanci kuma firar ta kara juna ce, mai amfani ce.......

A asibitin

Bayan IMAD sun gana da Likitar nan shi da Anna, suka nufi dakin da MAZNA take

Daf da zasu shiga suka samu Jauhara gefe da bakonta suka fira, nan suka gaisa irin gaisuwar girmama iyayenta bakon da su IMAD, kafin ya fice ya zamo JAUHARA ta koma gefe su IMAD suka shiga dakin da MAZNA take

Tana zaune bakin bed din suka shigo, sai kaninta dake zaune saman kujera yana dana waya

Sunna shigowa ya mike hadi da rage tsayinsa yana gaisar da IMAD da Anna

Da kua Anna ta ce" Lafiya kalau son, yau ka sauka da wuri daga wajen aiki kenan?"

Da girmamawa ya ce" Eh Anna, yau mun fito da wuri , sai na biyo nan kafin in wuce"

Anna ta ce" Madallah"

Sannan ta je inda Likitar ke fito da takardun Maznan, taba mika mata hadi da yi mata bayani itama, shi kuma yana tsaye gefe ya harde hannayensa yana duban bayanan da komai da komai, hakan ya sa shi kuma kanin nata fita dan ya basu waje.

Da kula Likitar ta sake yi mata bayani, ta ɗora da maganar abincin da ya dace ace tana ci gabanan......, ta idasa da sanar mata zuwa gobe da yama in sha Allah za'a salameta, sai dai ta ringa zuwa control du karshen wata har a idasa yarda da warkewar tata

Kai take gyadawa hadi da furta" Thank you doctor"

A tausashe ya dubi likitar ya sake duban Mazna ya ce" Docter, wannan ramar da take ta yi zata tsaya kuwa? sai sake ramewa take yi........., dubi fuskar ta yadda ta dawo"

Da kula Likitar ta ce" Sir, ai dole ne ramar nan, sai ta yi ta sosai, idan ta dage da abincin ne za'a dan dace, Ama shi ma kamar yadda na muku bayani zamu iya cire abinda aka sa a bayanta da na nononta, Ama ba zamu iya taba na cikinta ba, saboda rage girman tumbin ta ne aka yi, ta yadda idan ta ci abinci kadan ta koshi ba sai ta ci da yawan da zai sakata yin kiba ba......, wannan kam bashi da magani , sai dai ta ringa ci a kai a kai........, zata dan mayar da jikinta , Ama ba zata taba maida jikinta irin na da cen ba........"

Kai ya gyada, yana sauraro har suka gama magana, ta amshi NUMBAR doctor saboda tana da tambayar da take son yi mata, sannan suka fita Likitar da Anna suka sake komawa office din Likitar saboda tace akoy wasu bayanan da zasu yi da Anna

Kanta a kasa yake tunda suka fita, shi kuma yana dubanta ne hadi da sake yarda a zuciyarsa kwarai ko dan albishir din da ya ji a yau ya yafe mata har cikin zuciyarsa, bale kwarai da gaske ta cenza, kai koda dan tana asibitin nan ne ta cenza ya ga cenji a tare da ita mai yawan gaske

A hankali ya zauna gefen gadon nata, wanda hakan ya sa ta dan zarro ido cike da mamaki ta Dube shi, domin rabonta da ta ga haka har ta manta

Muryarta na dan rawa ta ce" Akul,........ka y........."

Hannunsa ya kama a hankali ya janyota jikinsa hadi da rungumeta a jikin nasa sannan ya shiga dan shafa bayan ta hadi da fadin" Its ok Mazna...., ki manta da abinda ya wuce, Allah ya tsare gaba, Allah ya baki lafiya"

Hawaye nan da nan ya bale mata, cikin Muryar kukan ta ce" Ina tsoro, ina tsoro sosai Akul, dubi yadda nake ta ramewa, kar aje ko har Cancer ta shige Ni, kar aje Shikenan ba zan kuma amfanuwa a zamana da kai na aure ba, kar aje ko.............."
Chapter 134 · 0% Book details