← Book details Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 141

Sashe 74

Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ta karashe tana yin murmushi daidai fitowar NUR dake shinshina hannunta tana lumshe ido ta ce" Innalilahi, kanshi, Farhana abin nan kadai ai ya isa ya sa fata ta wuni cikin kanshi.......shi yasa kike da fari haka ko? Bleating ne ko? Fada min, fada min....." Ta dage gida guda, wace ke jike da abin ruwa ta yi luwaiwai a fuskar nata, ta yi wani irin fresh da ita, haka ma bakin da ta ɗan tabe pink da shi yayi dasss a fuskar Tata

Haka kawai FARHANA da ta yi dariyar neman masifa irin na Nur ta samu kanta da zuba mata ido wani abu cen na darsuwa a ranta wanda bata taba tunawa da shi ba, bata taɓa kawo shi a ranta ba sai yanzu.......

Da sauri ta juya wardrob dinta ta bude ta tsaya tana kallo

Wata jar Abaya mai Zubin baki a jikinta, Ama kuma jan ne ke kasa, wato daga sama sama kadan take da bakin , Ama tun daga kasan mama har kasa ja ce, kuma mai kauri ce sannan budadiya ce sosai, ba ta inda ta kama jikin mutun, ta ajiye ta a saman abin kayanta, ta sake duba wajen wandunanta, ta juyo ta kalli Nur dake tsane gashin kanta ta duba ta ciro bakin wando palazzo sai riga baka Ama mai siririn hannu duka ta hade da mayafin rigar kafin ta cirowa A'isha itama irin rigar Ama Tata mai Zubin blue ce ta amshi tawul din hannun Nur ta ce" Zauna in busar maki da gashin"

Zaunawa Nur ta yi tana kallo ta jona abin busar da gashi ta shiga busar mata da gashin da iska mai dumi sosai har sai da ya bushe tana yi tana caje shi sannan ta shafawa kan nata mai mai saka gashi yayi laushi, sannan ta hade mata shi a baya ta daure mata shi kafin ta caje mata girarta ta hade da caje mata gashin ido sai rintse idon take yi kamar za'a fada mata ciki sannan ta saka mata jan baki mai ruwan lebe kadan ta ɗora mata man lebe sannan ta yi wajen wayarta dake ringin ta ce" Ku saka kayan mana..... hello Anna ????"

Anna ta sanar mata cewar Anas na kasa su yake jira zai kawo su asibiti, sannan ta dora da fadin " Sun ci abinci kuwa? Idan basu ci ba ki zuba musu fruits a basket sannan a saka musu shawarma da ruwa ku taho, mama ce ba lafiya"

FARHANA ta ce" Ok Anna, sai mun zo in sha Allah"

Daga haka ta ajiye kiran ta juyo, sai ta ga basu saka kayan ba, tana juyowa Nur ta ce" FARHANA, wai kayan nan sababi da da ganinsu suna da mugun tsada ne zaki ara mana? Kawai mu maida kayan jikin mu abinda yanzu zamu wuce gida ko A'isha??"

A'isha ta gyada kai ta ce" Farhana idan muka tafi gidan mu yaushe zamu baki kayan nan, Ni abinda ma nake tsoro jar kasar anguwar mu, kar mu je mu kwasarwa kayan nan dati, bari mu maida kayan mu kawai"

FARHANA ta sakar musu harara ta ce" wai kayan da kuka cire? To ai suna cikin mashine din wanki tuni, haba dai kayan nan ne zasu maidu, idan sun bushe kwa dauka Ni ba aro na baku ba kyauta ne, ku saka mu je fa, an turo a kai mu asibiti Mama bata da lafiya "

Da sauri NUR da ta dauki rigar nan ta shiga sakawa ta ce" Mamanmu? Daga wajen yan sandan suka kai ta asibiti ko? Dama na san mama rashin lafiya zata yi idan aka kai ta wajen sojawa, tsoronsu take yi fa"

Farhana ta sakar mata harara hadi da jan tsaki ta ce" Ai sai ji yi,.ke da bakya kishin mahaifiyarki, mamanki dai ama ni gaskiya mutun mai irin zuciyar matar nan ba zata taba haihuwana ba, kama ki shafa turare a ko'ina mu je" ta miko mata wata tsumamiyar humura mai sanyin kanshi , mai naci a fata, mai jimawa sosai a jikin mutum , wato humurar manyan mata masu daraja da suka san darajar turare.........( idan kina son humurar ki tabo numbana....., ama ki shirya😁🤗)

Sosai Nur ta shafa turaran nan, domin ita dama Mutun ce ma'abociyar son kanshi, kawai dai basa samunsa yadda ya kamata ne a gidan su ya sa basu takurawa iyayensu da barnar wanda ake samu a dan ajiye wanda kusan kowa ke dasina in fitar zuwa wajen wata sabga mai daraja ta kama su......, domin ba na kullum bane, dan ko a gidan idan aka dace turaren wani ya shiga hannunta sai an yi da gaske ake rabata da shi, SULaimana ya sha mamaka mata mari idan ta bulbule masa turarensa, hakan baya hanata gobe ma ta bincika idan ta samu ta shafe shi kuma tace abinda turaran warin yan bori yake yi????? , ai kuwa yanzun ma sai da A'isha ta zarro ido tana duban kwalbar da NUR ta samu take kara tultula a hananyenta tana ta bin jikinta da shi kasa kasa ta ce" Nur ya haka? Kar ki karar da turaran mana........?"

Nur ta mika mata tana murmushi ta ɗora abayar nan a saman kayan sannan ta ɗan yafa mayafin ta karasa wajen madubi ta tsaya tana duban kanta.............

Murmushi ta yi a hankali ta furta" Kamar yar indiya.....ikon Allah ashe fara ce ni ?"

A'isha ta yi dariya ta ce" Nima baki ga sai kalonki nake yi ba, gaki da dorinar ado, gaba daya yau kin cenza "

Farhana ta yi murmushi a ranta ta ayyana ' Haka nake so'

A bayane kuwa ta ce" Kandalar Anna, kar ki wani ji dadi, babu wani kyau da kika yi, ku wuce mu je!"

Nur ta sakar mata harara ta ce" FARHANA saboda sunan nan sai na baje ki a kas tabbas "

Farhana ta tabe baki tana jira, suka fito ta rufe dakinta suka nufi elevator, tana duba wajen msg da mamakin irin yadda saurayinta ya bace bat, rabonta da shi tun a daren da tace da shi ƴaƴanta fa ya zo kasa sai sun rage kiraye kirayen junan nan, bale na dare dan kuwa idan tana ganin baya sane da abinda take yi tsaf zai iya kamata da laifin da ba zata iya amsar kanta ba, tun daga lokacin ko ta masa flashing kamar yadda ta saba idan ta kadaice kanta dan su yi fira sai dai ta yi ta jira ba call din nasa ba msg ko yayane ba komai, kuma wayarsa na shiga a kasar yake tabasssss, abinda bata gane ba shin yada wayar yayi ko me yake faruwa? Ko kuma tsoron ƴaƴanta da yake yi ya sa yayi nesa da ita har sai ya bar garin? Ama kuwa da ya ja abinda bashi da rana saboda ƴaƴanta ai ya zo da zaman gaba daya ne ko??????????........................

Tun kafin su sauko ta sanar da mai aiki abinda za'a saka musu a basket, tuni ta saka ta mikawa ANAS ya kai cikin mota, yana tsaye jikin motar yana chating da wata tsohuwar budurwarsa ba tare da ya gaji da jiran Farhana ba, domin dama idan zasu fita ta saba tsayar da shi jira sosai yana dan murmushi saboda tana ta mitar yaushe rabonsa da ya shiga cikin gari wajen ta ne, yana dan karkada ky din mota a ransa yana Ayyana' ai ko zaki gani sai baban nan namu na Magarya ya shafa min fatihar IMTEEna, Ama ba yanzu yanzu ba '

Ya dago sakamakon jin taku ana nufo inda motar take ya sauke dubansa a kan fuskokin dake tahowa din lokaci daya ya zarro ido da mamaki ya ce"Kisan mummuke 44-45

Ya dago sakamakon jin taku ana nufo inda motar take, ya sauke dubansa a kan fuskokin dake tahowa lokaci daya yana zarro ido da mamaki kasa kasa ya furta" NUR? "

Da sauri ya sake duban A'isha ya furta" A'isha?"

Murmushi A'isha ta yi tana wuce Nur da ta ɗan dakata hadi da sada kanta ta furta" Yaya Anas Barka da warhaka......., ya aiki"

Sai da ta furta Ya aiki ya bi jikinsa da kallo, a Boye ya sauke ajiyar zuciya saboda ganin shigarsa bata da laifi ya sake leka NUR dake bayansu kasa kasa ya ce" Ban gane ba, yaushe, to, wai , ban gane ba"

Farhana dake kallonsa da mamakin yannayin da ya shiga ta dubi Nur, wace ke ta neman boyewa, haka kawai ta sake dubansa tana jin wani abu mai kama da jin haushi haushinsa har ma ta samu kanta da tare lokacin da ya so budewa Nur gaba ta shiga, ta bude mata baya tana dubanta kasa kasa sosai ta ce" Kar ki ce min wannan ne saurayinki??"

Nur ta dube ta, yannayin da ta yi maganar kamar ranta a bace, sai dai bata bata damar bata amsa ba ta ce" Shige mu je......."

Nur ta shiga tana sake duban FARHANA, haka itama A'isha dake inda yake yana ta yi mata tambayoyi tana dariyar yannayin yadda ya kidime ta ringa bashi amsoshin da suka so saka shi idasa gigicewa, a dole ya shige wajen direba ya tayar da motar yana ta so Nur ta Dube shi, ga mamakin wai dama su A'isha ne ake bashi labarin an ga yarinyar wajen mama? Cabdijan.
Chapter 74 · 0% Book details