← Book details Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 141

Sashe 39

Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A cikin zuciyarta kuwa aiyanawa take yi' To Ama, me yasa yarinyar nan take min haka ne?, ko na taba yi mata wani laifin da ya kai haka?, ko wanda baka hada komai da shi ba zama gida guda ya haɗa ku ai kwa gaisa bale ni ? Me yasa yarinyar nan take irin haka ne....? Ko shi ne yace da ita kar ta zo inda nake???, ok sai yana gari ne zata kusanci inda nake kenan?, ba zan taba yin daraja a idannuwan yarinyar nan da kannenta ba kenan?????'

"Ai Anna Ni mamaki take bani, duba ki ga gaisuwa harda dukawa har kasa dan ta birge miji da abokanan miji, bata san su larabawa dukawar nan wata fasara zasu mata daban ba? , wallahi matar nan munafuka ce, hum, du ranar da yaya ya gane ta zan so ace ina nan, ya yi mata dukan mutuwa wa bilahilazi!" FARHANA ta fada tana sake dora hannun Anna saman kanta dan ta yi mata dangwashi

Anna ta dungure kan ta ce" Allah ya kiyaye ya daki mace, macen ma matarsa, ke kam Bakya ji, yanzu meye amfanin sanar min tana gidan nan dama? Sai ki kyale Ni a zuwan yanzu ta zo ko? Da Bama zan damu ba FARHANA!"

Farhana ta dago tana duban Anna, kafin ta gyada kai a ranta tana ayyana ' To ai shiKenan, yau kuma kamar ana nufin in yi karya kenan dan jin dadi ko???, Allah ya kyauta'

Bata ce komai ba ta ci gaba da neman barcinta, Anna kuwa sai sake sake suka nemi damunta, sosai zuciyarta ta yi nauyi da jin batun nan, harma ta yankewa kanta hukuncin zata sa IMAD ya yiwa iyalinsa wani gidan su koma, ko kuma ita ya yi mata wani ta koma, Ama in sha Allah ba zata kuma hada filin tsakar gida da yarinyar da take yiwa kallon y'arta Ama kuma tarin wulakanci irin wannan na shiga tsakaninsu...........

A bangaren MAZNA ta ji dadi da akace ta fara tafiya kafin ya zo, hakan ya sa tana zuwa ta samu sun yi du yadda tace din, FU'AD har ya koma dakinsa, sai Jauhara dake jiranta

Jauhara ta ce" Ga pad cen na zuba Betadine a jiki, ki yi anfani da shi, kuma ki yi iya yinki ya yarda, shine kawai abinda docter yace , dan yace ba yanzu ba, ki bari ki kara warkewa!"

MAZNA ta yi dakinta ta shige wanka, a dan gagauce ta shirya da pad din sannan ta dawo falo ta salami JAUHARA zuciyarta cike da tsoron abinda ke iya faruwa........................

Kwarai da wahala ta iya kubuta, idan kuwa ya kai ga cimma burinsa a yau ya kashe ta ya gama.

Bayan zamanta ma ta jima kafin yake shigowa dan a kala ta dauki minti ashirin sannan ya murda kofar dakin ya shigo fuskarsa a sake sosai ya jingina da jikin kofar dakin yana kallonta, shi bai saki fuska ba, shi bai mugun daure fuska ba.........domin ba wani hucewa yayi da rashin kular da ta nunawa mahaifiyarsa ba, yaya ma za'a yi ace wai ta yi rashin lafiya Anna bata sani ba, ta yi tafiya Anna bata sani ba????????

Duk wani kalar tausayi ta gama arowa ta yafawa fuskarta

Idannuwanta kuwa sun gama cika da kwallah , a hankali ta taso ta nufo inda yake tsaye kafin ta sada kai murya na mata rawa ta ce"INDAI KUNSAN KUDIN KUKESON SAMU A ONLINE BUSINESS TO KAWAI KUYI JOINING GROUP DIN NAN 👌🏻😅KUNSAN bani kawo abun banza
💃🏻https://chat.whatsapp.com/L64v3OVQ52pJqtMT51yL2x

23

A raunane sosai ta ce" Barka da sauka rayuwata, Barka da sauka a kasar ka"

Idannuwansa kawai ya lumshe a hankali ya furta" Barka "

Kafin ya zagayeta a nutse ya nufi dakinsa

Gabanta ne ya ci gaba da faduwa.....

Ya Allah, dama fa ta sani sarai baya saukowa da wasa a lamarin da ya shafi mahaifiyarsa....., shin yaya aka yi ta tafka wannan laifin daya kan daya? Yanzu idan asirinta ya tonu cewar da ta zo ma bata je inda Anna take ba wace amsa zata bashi da zai Dube ta?????

Da sauri ta nufi kicin, ta shiga nema masa abinda ta san cewa al'adarsa ce kafin ya kwonta yana anfani da shi, irin su shayi, da ruwa mai dan dumi....., ta bashi space dan yayi wanka ya kimtsa....., domin ta san dakin ba dati saboda ko kwana biyu ba'a yi ba da ta sa su JAUHARA suka gyara dakin da bayi da komai , zanin gado ne kawai ba a shinfida ba, shima zata shinfida be yanzun saboda akoy sababi, akoy wankaku a dakin dake dauke da kayansa.

Sai da ta gama dafa shayin da komai sannan ta jero saman tire ta nufi dakin nasa

Sai dai ga mamakinta tana zuwa ta tsaya ta buga sau uku sannan ta murda zata shiga, Ama dakin a rufe ruf

A hankali ta jinginar da kanta jin kofar a sanyaye ta furta" Akul, plz ka bude min kofar mu yi magana mana"

A lokacin yana cikin shafa turare a jikinsa, ya dubi kofar , ya ci gaba da abinda yake yi a nutse, yana gamawa ya juya ya haura dakinsa na sama ya bude ya shige

Sai dai alamun an jima ba'a shiga ba ya sa ya sauko kasan a dole ya bude abin shinfida sabo ya shinfida sannan ya kashe fitila ya haye saman gadon a hankali ya kwonta yana lumshe idannuwansa da neman fitar gajiya daga jikinsa hadi da neman barci, domin zuciyarsa a sam bata bukatar wani zancen da zai iya bata masa rai bayan a yau ya dawo, ya ga Anna da jama'ar gidansu, ........kwarai yana missing din iyalinsa a tare da shi, sai dai ba zai taba yarda ya bata fuskar da zata bata damar aikata wani laifin kwana kusa ba, da shi take magana , shi in dai ba zata mutunta masa mahaifiya ba bai ga soyayyar da zasu iya yiwa juna ba

Jikin MAZNA ya kara mutuwa, a dole ta juya ta ajiye komai saman table ta nufi nata dakin

Bayan ta zauna a bakin gadonta ta shiga tunanin mafita, domin ita sheda ce, baya hada lamarin iyaye da komai a duniya, idan kana so dama ka ga yannayin nasa bacin ran ka tabo wannan fagen, in kuwa kyautatawa kake son gani mai suna kyautatawa kuma ka kyautatawa iyayensa.....haka Allah ya halicce shi............, ita da kanta sai ta fara tunanin to ina anfanin kashe kanta ta hanyar taba lafiyarta dan ta birge shi kuma su ringa wanyewa a haka????

Kai koda ace idan yana nan zata yi zumuncin dole da Anna zata kwatanta, in baya nan kuma shiKenan sai ta yi lamarin ta ita kadai, abin haushin ma da zamansa ya dawo nan yanzu, du wata sakewa da take tunanin tana iya yi zata zama tarihi.

_________________________________

Anas na fita daga gidan Anna gidan su ya je ya shige wanka

Shiryawa ya yi cikin shiga mai kyau da kamala, domin manyan kaya ya saka hadi da bade jikinsa da turare kafin ya fito ya yiwa mahaifiyarsa Salama cewar zai je anguwa

Bata tambaye shi inda zai je ba, sai addu'a da ta bi shi da shi, dan yannayin shigar nan ta yiwu iyayen gidansa zai kai wani wajen.

A lokacin da ya karaso kofar gidan su IMTEE waje ya samu ya zauna ba a cikin motarsa ba yana ta kallon yannayin anguwar da kuma hankalta da shige da ficen kowa da komai, sam bai nemi a masa magana da ita ba, hasalima zama yayi yana jira dan ba zai dauki wani risk din da zai bata mata rai ba.

A kadan ya kai awa a wajen nan kafin Malan ya nufo gida, dan sai da ya kaiwa abokinsa fira , wanda ke garin damagaran suka yi zumunci harma ya kara amso manyan adu'o'in tsari sannan ya nufi gidan

Mikewa yayi yana jira har Malan ya karaso shima yana kallon sa da mamakin gane ko waye.

Har kasa ya duka yana gaishe da malan, wanda ya zuba masa ido yana nazartar shi kafin ya ce" Tashi tashi mana yaro tashi, Malan Anas ne ko???"

Yaya Anas ya amsa kansa a kasa ya kasa tashin, sai da Malan ya gane cewar da wahala ya tashin sai ya ce" Lafiya dai ko?"

Anas ya kara sada kai ya ce" Baba, na sake zuwa ne a kan maganar nan, baba duk wani abu da kake da bukatar sani a shirye nake in sanar maka sannan in kawo kawuna ya zo ya sanar maka, baba Ni dai gidanmu yana nan bayan layin nan, mahaifina ya rasu, Ni ne baba a gidan mu sai kanai na uku, maza biyu mace guda Fa'iza....., baban su IMTEE kawayen Fa'iza ne, sanadiyar haka na santa, baba da ba zo nan gidan na zo ne da neman aure, ina so a bani dama baba, idan har ka tashi yiwa Imtee aure in fito da karfina, idan ba yanzu Bama a bani lokaci sannan a bani damar cike duk wani gurbin da ya dace dan zama mijin da aka tsaida mata, baba ina son aurenta, ba wasa na zo yi da rayuwarta ba, ina da sana'a, ina da muhallin da zan ajiyeta...., baba ina kiyaye adinina, ina kuma kyautata mu'amalata da jama'a, dan Allah in dai ba an yi mata miji ba a taimaka a bani dama"

Gaba daya sai ya daure baban yara da jihrar jikinsa har ya gaza sake sanar masa cewar shi fa bai yarda da shi ba

A hankali baban yara ya ce" Tashi, tashi yarona tashi"
Chapter 39 · 0% Book details