← Book details Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 136 OF 141

Sashe 136

Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sosai yayi mamaki, har ya kasa magana ya rungumeta a jikinsa a hankali yana shafa bayanta cen ciki ya ce" I love You NUR........i love You so much"

Idnanuwanta ta lumshe tana sake riƙe duk wani tunanin dake iya daga mata hankali, ciki harda tunanin gobe in warhaka baya tare da ita yana tare da matarsa ne......., cen ciki ta ce" I love You tooo Andadi....."

Murmushi yayi, a hankali ya shiga sake lalubarta, hakan ya sa ta dago tana dan zarro idannuwanta irin ya haka?

Murmushi yayi cen ciki yace" Ban koshi ba fa........, plz bani in kara
......."

A hankali ta hade bakinta da nasa....., wanda hakan ya sa ya sauke ajiyar zuciya hadi da sake rungumota tare da zare takobin kashe arnan suka shiga yaki ka'in da na'in🚶🏻‍♀️🚶🏻‍♀️🚶🏻‍♀️🚶🏻‍♀️🚶🏻‍♀️

Washe gari

Saura kiris🤣KISAN MUMMUKE PAGE 85

A washe gari shi ne da kansa ya tayata shirya kayan da zata buƙata a yau zuwa yan kwanaki, sannan suka dauki lokaci sunna fira kafin su shirya kusan karfe goma na safe , suka fito gaba dayansu domin a yau Anna ta amince musu su rakota, harma da Mama da za'a kawo a lokacin ya sa Anna cewa eh su taho su Dukansu, duda ba'a fada musu ba, suna son yi musu surprise ne..........................

A lokacin da suka zo gidan, ba karamin farin ciki iyayen nasu suka shiga ba, bale su, haka nur ta rasa inda zata zauna, ta yi nan ta yi cen da dan gudunta cike da farin ciki, shi kuwa sai kawai ya dafe haba ya rasa abin cewa domin idan yace zai yi magana a nan bai san me zai ce mata ba, Ama irin yadda ta dage da fara'a tana tsalle tsalle kamar yace ta yi hakuri ta rufa masa asiri ta kiyaye abinda ke tare da ita mana

Auntyn yara cike da murmushi ta dauke idannuwanta daga kanta a lokacin da ta duka ta ɗora kanta saman cinyarta tana ture A'isha da ta rukunkume auntyn nasu ta ce" Ke Dilla nima dan bani in dana cinyar mana?"

A'isha ta kiya itama tana rungume auntyn nasa ta ce" Ai na riga ki, ki je wani wajen mana, ba ga Anna Bama zaune?"

Mikewa ta yi ta nufi inda Anna tana tabe baki ta haye saman kujerar hadi da ɗora kanta saman cinyar Anna ta ce" na yi
Yi missng din ki so much annata......."

Idannuwansa ya lumshe, wani sanyi na sake rantsa masa
Zuciya a lokacin da Anna ke rungumeta ta ce" Na yi missing din ki Ni ma sosai yarinyata"

"To ai shiKenan, Anna ki bari ni in rungumeta mana, matar Imadi ce fa......., kai wallahi sai rashin kunya ake koya maki karfi da yaji, Bakya jin kunya wai?" Inna ta fada tana zaunawa da kyau ɗan sake duban rashin kunyar Anna kamar yadda ta fada

Anna ta sada kai tana murmushi, sai dai bata ture Nur ba ko kadan, hasalima kunnenta na jiyo lokacin da Imad ya ce" Zaki fara ko? Kafin a bani Itan da wa kika santa ? Ke sai neman fada?"

Inna ta tabe baki ta ce" Ke taho nan kusana y'ar albarka zo Ni ma in rungumeki wannan abin dadi har ina"

Kiran wayarsa da Aliyu yayi ya saka shi dagawa ya kara a kunnensa , kafin ya ce" Su Malan na nan ko?, a shigo da ita nan din da su Malan din kawai, ka cewa sojawan da suka kawota suna iya juyawa, Thank you "

Daga haka ya katse kiran yana duban inda Inna ke gyarawa nur rantsatsiyar atamfar jikinta, wace take da masifar kyau da kudi, domin atampar zata kai 300k, kuma ɗinkin sket da riga ne kawai ta mata , rigar ce ma budadiya, sket din ya dan kamata, Ama kuma duda haka ana ganin shafafen cikinta ya dan tasa alamun da ajiya a cikinsa, gashi atamfar ja ce sai ta sake haska mata fata

A tausashe ya ce" Sun iso anna"

Anna ta Dube shi, sai kuma ta kalli auntyn yara wace ta fara mikewa a hankali tana rike da A'isha, Farhana kuwa kicin ta fada wai sai ta yiwa MUTALAB abinda zai ci na rana, ba zata barshi da neman abinci a restaurant ba dan kuwa tunda suka yi aure su Dukansu sukan tura abinci wa mazajensu daga hannun Aliyu na rana, da dare kuwa idan sun shigo suke ci.

A hankali Auntyn yara ta sauke ajiyar zuciya ta dubi A'isha zata yi magana Mama ta sauko daga elevator ta nufo su a lokacin da Malan ya bude kofar ya shigo ya dan bada hanya dan ta shigo

Shigowa ta yi, da wata bak'ar abaya a jikinta.......

Abayar sabuwa ce domin da safe aka bata ita , sai dai ita din du a jeme, ta yi baki kirin ta dafe tamkar ba Maman yara ba, du garin jikin nan nata ya sabe, duk wani waje mai auki ya rame, haka kuma bakinta gum, sai Malan da take kallo da mamakin shigar jikinsa, da mamakin kanshin da yake yi, da mamakin hasken da fatarsa ta kara, uwa uba mamakin jikin da yayi madaidaici, domin du kumatunsa sun ciko da su abin sai san Barka, haka kuma tunda aka fito da ita kallo daya ya mata ya girgiza kai hadi da dauke dubansa a kanta, sai Malan baba ne ma wai yace da ita ta shige su je ciki....... Lalle Malan, ashe zata iya yi masa laifin da zai manta da ita a duniya? , kwarai a kilace take a dakin da take ita kadai jal da ranta, ba'a hana mata abin alwallah ba, ba'a hana mata abinci idan lokacin ci yayi ba, sai dai ko kare bata gani bale mutun, wannan kadaicin ya sa ta ringa fita a hayacinta, a hankali a hankali ta ringa zuba hauka domin sai ta raba dare tana kuka da magiyar a fitar da ita, ba duka , ba zagi, kawai mutun ne ma ba zata gani ba bale har ta gane a duniya take, a dan daki ne takurare ama ya isheta mikewa da zaunawa da tankwasawa da gabatar da Sallah in ita take so, sai dai kamar zata mutu haka ta rayu a ciki, wai a haka bama kabari bane....., gaba daya bata hayacinta, ta yi wani irin zuru zuru kamar mai ciwon dépression, ta yi wani iri da ita kamar mahaukaciya sabon kamu........, ko yannayin kallonta wani iri ne, ga irin abin fada fadan nan, sai ya zama ita kadai ma gyatsine take yi...., wani abin takaicin du zaman nan da ta yi burinta ta koma gidan malam ta ɗora daga inda ta tsaya, domin kuwa a ranta bata yi nadamar abinda ta aikata ba, ta fi yarda cewar ko me ta yi malam ne ya ja, da bai yi abinda yayi ba da yanzu suna nan asirinsu a rufe suna rayuwarsu......., kai ita Bama ta A'isha take ba, ta sani yarinyar dama ba wani kaunar ta take yi ba, shi yasa itama bata taɓa kashe kanta saboda ita ba, ko a yanzu bata gabanta ita da uwarta, yanzu haka da aka nufo gidan nan da ita a ranta take tambayar kanta me kuma zata yi a gidan nan? Me za'a kawota yi a gidan nan?

Shigowa Aliyu yayi, ya ja ya tsaya a bakin hanyar shigowar, sannan ya ce" Bismillah ki shiga mana"

A lokacin ne du hankalin wanda bai kai wajen Bama ya kai, ciki harda Nur, domin fira suke yi ita da Inna tana dariyar tambayoyin da Inna ke mata tana girgiza kai ta ki ta fada mata din,

Da farko, auntyn yara da A'isha maman yara ta zubawa ido, jikinta ba daukan wani irin mijirya kamar ta saka hannun a cikin ruwan ƙanƙara, sai kuma Nur ta shige gabansu a lokacin da ta taho tana dubanta, sai kuma ta juya wajen abansu da yanayin farin ciki, ta kuma kalli IMAD dake kallon ta, du TAKUNTA dan ta isa inda maman yara yake na fadar masa da gaba dan haka kawai baya jin ya yarda da matar

A hankali ta ce" Mamana ne?, Ya'yan FARHANA mamana ce?"

Sai kuma ta karaso da dan sauri , wanda kafin ta iso abanta ya saka hannunsa ya rike nata yana dubanta a tausashe ya ce" Ki bi a hankali, kuma ki bari ta zauna tukunan"

Nur da mamaki ta Dube shi, sai kuma ta dubi mamansu kamar bata cikin hayacinta a hankali ta ce" Aba, mama ce fa, ....mama, yanzu kika zo? Daga ina kika zo? Me ya same ki kika rame haka?"

Da dan sauri maman yara ta karasa inda Nur take ta rike hannayen ta hadi da haɗawa da na malan , hakan ya sa IMAD mikewa tsaye lokaci daya, sai kuma yayi saurin kai idannuwansa fuskar Aliyu da ya taho da sauri

Dakatawa yayi, ya ja baya, hadi da dauke dubansa

IMAD kuwa a tsayen nan, idannuwansa ya zuba musu a lokacin da Mama ta ce" Me kike yi a nan,? Me kuke yi a nan?, wa ya baki wannan rigar? ya aka yi kika kara haske kika yi kiba?, me ya same ki kika yi kiba? Dan ubanki har kiba kika yi Ni ina cen rufe? Har kiba kika yi IMTEE?"

Hannunsa ya saka ya kwace nata da dan karfi hadi da matsar da ita da karfin gaske kafin ya ce" Ke ki kama kanki, to idan bata yi kiba ta yi haske ba mutuwa kike so ta yi? Ai yanzu matar aure ce ita, kuma mai daraja a ɗakinta dan haka ki daina zaginta!"
Chapter 136 · 0% Book details