← Book details Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 141

Sashe 80

Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani gauran numfashi ta sauke sakamakon tunawar da ta yi a cikin gyaran da ta yi harda na matsi, bayan a da din ma du idan aka yi bajewar mamaki sai ta jima tana gasa kanta, ita kam yau ta san ta mutu ta lalace.......

Wani ihu ta saka tamkar yau ne daren farkonta da shi

Har sai da ya sake dakatawa kadan yana dubanta domin du yadda ya so yi mata bajaja sai ya ringa tausaya mata a cen cikin zuciyarsa saboda sam bai iya duban mace da duba irin na mugunta ba, yana yiwa mata duban abinda za'a lalaba, matan da suka zagaye rayuwarsa a kullum kallon da yake musu kallo ne na mutane mafi daraja wa'inda yake nema tukuru dan kar su nemi komai su rasa a rayuwa.....shi yasa a rayuwarsa koda wani abu ya hada shi da wata macen ko a waje ne ya sabawa kansa yin shiru, ya kawar da kai, domin shi bai ga wani abin rashin jin dadi da zai iya tsayawa yi da mace a rayuwa......, mata iyaye ne, abokan rayuwa ne, yayu ne, kanai ne, duk wata daraja a duniyar mace ta tare, dan haka a hankali ya ringa kokarin bin ta har sai da ya gama isawa ne ya shiga sauke mata gajiyarsa mai dumbin yawa da nisan zango, wace ta sa MAZNA jin tamkar ranta zai fita, domin kuwa a lokacin cikinta ya dau ciwo, ya zamo du idan ya shige ta sai cikin ya kara ciwo......, tsoron kar wani jinin ya bale ya sake busar da ita kamasssssss, ya zamo kyan da take nema din da nutsuwar da take hari sai ta zama mafarki, domin a zahiri ga bushewa ga azabar da ta sa ta ringa kuka tamkar zata hadiyi zuciya, kuka irin na zucin nan, tana yi tana jimke hannayenta a jikin sa.....,

A hankali yake kallon fuskar ta, da gaske wahala take sha wace ta wuce misalin yadda ya ƙiyasta zata iya sha.........

Hawaye ke bin kumatunta tamkar zata sike

A hankali ya dakata da motsin da yake yi a cikin jikinta ya sake zuba mata ido cike da son gane ainahin abinda ya sa take cikin wannan halin

Matar da idan suka zo fagen bed wani lokacin har dariya take bashi idan ta nuna irin yadda take injng?, matar da in suka kadaice koda bai nema ba take nema?
A yau din ma ai dan ta nuna ya mayar da ita gefe har yana ba watanta ne ya sa ya zo dan kuwa ya gama sakawa ransa sai ya gama bincike a kanta idan hankalinsa ya zo waje daya, sai kuma wannan réaction Tata ta saka shi tunanin kar fa aje yana cikin tashin hankalin hakinta a kansa da ya jima bai sauke ba? Dan haka kawai ba zata yi irin wannan tunani mai girma ba

A hankali ya ce" Me yake damun ki?"

Bugawa kirjinta yake yi, da sauri ta rike damatsunan hannayensa tana son yin magana sama sama kirjinta na bugawa da karfi karfi.....

Da sauri ya daga mata kirji da ya dan dora mata yana sake dubanta da mamakin yannayinta........

Jikinsa ya janye gaba daya daga jikinta ya ringa fifita mata fuska da hannunsa yana dubanta

Hannunsa ya saka ya zaunar da ita yana dubanta ya nufi wajen fitila bayan ya dauki gajeran wandonsa ya saka ya kuna fitilar ya juyo inda take, ya je wajen frij ya bude ya dauko madara mai sanyi ya zo ya zauna ya bude ya kafa mata a bakinta yana kallon yadda jikinta ke ci gaba da yin rawa

Da mamakin yannayinta ya mika hannu ya janyo rigarsa, wato jalabiyarsa wace karamar wayarsa ke ciki ya ciro wayar ya shiga latsa wasu numbobi

Da sauri ta rike hannunsa tana dubansa murya cen ciki ta ce" Akul, me zaka yi???"

Idannuwa ya zuba mata a hankali ya ce" Ban san baki da lafiya ba ai, dama baki da lafiya ne? Aliyu zan kira ya zo kai mu asibiti"

Da sauri ta girgiza kai tana zarro idannuwanta murya a harhade ta ce" asibiti? A'a, a'a, ka ga zazabi ne kawai nake yi, kuma bai yi zafi sosai ba"

Ido ya zuba mata, a hankali ya ce" Ina ce , idan kina zazzaɓi ne ma kika fi nema na??"

Gabanta ya yanke ya sake faduwa....., a hankali ta girgiza kai tana fadin" Eh, am, a'a, ka san abinda yake faruwa ......zazabi ne da ciwon ciki, taba cikina ka ji zafin da ya dauka shi ne ya sa nake jin wahalar abin, kuma Dazu ne ya same Ni shi yasa ma baka gan Ni a falo ba da ka dawo"

Cikin nata yake shafawa yana jin zafin da ya ɗauka, a hankali ya ce" To ki bari mu je asibiti, a haka kike so in bar ki ki kwana????"

Yanzun ma da sauri ta girgiza kai ta ce" A'a fa, ba sai mun je asibiti ba, zuwa safe zan ji sauki"

Yanayin tsoratar da take ciki ya fi komai daukan hankalinsa da saka shi zuba mata ido..............

A hankali ya ce"MAZNA me yake damun ki ? Akoy abinda ya dace in sani dangane da halin nan da nake samun ki a ciki? ......."

A hankali ya dan shafa goshinsa ya sake duban ta ya ce" wancen karon, jini ne ya bale maki...., yanzu kuma kafin in zo nan jikinki ba wani zafi, ba komai...... But yanzu duba ki gani.....me yake damun ki? Idan da abinda zaki fada min ki fada min, kamar wace kike jin tsoro na, kamar wace kike tsoron in....in......in yi hvng sx da ke.....me yake damun ki"

Hannayensa ta riko da nata biyun a hankali ta ce" Akul, Ni da kaina ban san abinda yake damuna ba, ama in sha Allah zan gyara ko menene, plz kar ka daga hankalinka a kan wannan kar ka saka tunanin komai a kanka, kawai rashin lafiya ce aka yi katari da muna cikin aikata haka take faruwa.....Ama ka ga zan gyara plz zan gyara kar ka wani damu plz"

Dubanta yake yi har ya dire maganarta jikinta na dan rawa rawa

A hankali ya janyo ta jikinsa ya rungumeta yana shafa bayan ta

Kasa kasa ya ce" Wani magani zaki sha to in fita in nemo idan baki da shi a nan? Ba fa zan yarda ba sai kin ga likita gobe in sha Allah"

Kara kwontar da kanta yake yi a kirjinsa, wata irin nadamar da bata taba ji ba tun aikata aikin nan har zuwa yau na ratsa ta da tarin tsoro.........
Kwarai mutun ne mai hakuri da daga kafa, Ama idan har ka yarda ka kai shi bango sai ka raina kanka da irin amsar da zai baka iri daya da rainin wayon da ka masa ko sama da haka............

Innalilahi shin yaya zata yi da ranta ne? A duniya bai hada mutuncinta da komai ba, shin idan har ya ji yadda ta yi da nasa mutuncin yaya zasu kwashe????

A hankali ta ce" Ba sai na sha komai ba, zai wuce Akul"

Shiru ya yi yana shafa bayanta a hankali yana yi mata addu'a a cikin kunnenta a tausashen da ya sa ta ringa sauke sanyayar ajiyar zuciya

Jiki ta saki ta langwabe alamun barci ya fara yin gaba da ita

A hankali ya furta" Baki yi tsarki ba fa, kar ki kwana da najasa........bari mu yi wanka"

Daga haka ya mike da ita a jikinsa ya nufi bayi........

Cikin nutsuwa ya bata kular da ta dace yana bin ta a hankali har ya fito da ita, a nutse ya mayar mata da rigarta sannan ya gyara mata kwonciyarta

A hankali ta riko hannunsa a lokacin da ya motsa zai tashi murya ciki ciki ta ce" Na san a wahalce kake, ka bani dama in baka kulawar da zaka samu sauki kafin in samu lafiya....."

Yana duban ta hadi da bin bakinta da kallo....., a hankali ya dan shafa lebenta ya ce" mun sha gwadawa, bana taba iya samun nutsuwa da nan......, zan yi hakurin , Ama zan kai ki asibiti tomorow in sha Allah, nw sleep ......ki huta "

Daga haka ya ringa dan shafa fuskarta har barci ya dauke ta

A hankali ya mike yana rintse idannuwansa saboda irin yadda mararsa ta cure waje guda ya fice ya nufi nasa dakin dan kuwa zai cenza tufafinsa ne sannan ya koma domin ba zai barta ta kwana ita kadai ba bayan bata da lafiya

Yana shiga nasa dakin a hankali ya zauna yana rintse idannuwansa hadi da kai hannunsa wajen mararsa.........

Tabbas idan ba Allah ne ya tsare bawa ba, ba abinda zai hana mutun neman abinda zai raba shi da wannan wuta dake rurun masa a zuciya, da kuma mararsa ba.......
Wani lamari ne mai tafe da taku biyu, neman abinda za'a anfana ido rufe dan shaukin zuciya, da kuma samawa jiki lafiya da karfin jiki........, shi yasa da yawa da ta motsa musu suke saukewa ko a kan waye..........

Shi da kansa a yau, da ace yana da wata matar bayan MAZNA da da wahala ya iya hakura sai ya nemi izini ya kai wannan jaraba ya ajiye a inda ya dace......, sai dai ba halin haka, a dole ya sake daura alwallah dan samun sauki a wajen da ake samun saukin kowace cuta, wato wajen Allah.

Dakin nata ya koma ya zauna saman kujera ya mike kafa a hankali ya bude yana karatunsa har ya samu nutsuwar zuciyarsa da gangar jikinsa sannan ya rufe litafin ya ajiye a waje mai kyau ya je ya sake taba jikinta ya ji da zafin, Ama kuma barci yake yi, sai ya koma ya zauna yana bude Babar wayarsa ya yiwa Abdallah msg dan ya ji shin ya kwonta ne ko kuwa? Domin bambanci time din dake tsakanin Nijar da Saudiya ke sakawa wani lokacin ya kwonta da wuri haka.

______________________________

Washe gari kam Anna bata tsaya ta jira shi ba, suka shirya da wuri suka je asibiti da kayan Mama din, saboda abin kari da komai a cen zasu bata likitocin
Chapter 80 · 0% Book details