Sashe 29
Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A lokacin da Aban yara ya zauna yana duban kofar makarantar ya'yansa zuciyarsa na cika da tunanin idan an tsaurara lamarin kudin makarantar nan tasu ina zai bi ya samo ya ci gaba da biya musu? Ga Imtee har yanzu a aji uku kawai take na secondry, ta ki ta maida hankali bale ta yi gaba, A'isha ce ma take daf da barin secondry din, ......shin nawa za'a yanke musu ne? Me da me za'a ce su kawo?.....shi dai koda bashi da halin biya musu ta bokon zai so ace sun ci gaba da islamiyyar su a nan, burinsa ace yau ya'yan nan suna sauka, wai, da ina zai kai ransa dan dadi??????
"Barka da warhaka baba" wata murya ta gaishe shi da girmamawa
Dubansa ya kai kan fuskar, lokaci daya ya shaida mai fuskar harma ya ɗan sake dubansa da hannun sa da ya miko mashi.
Amsar hannun baba ya yi yana amsa gaisuwar sa, sannan suka dan yi shiru
Da ky din mota ANAS ya dan sosa bayan keya kafin ya ce" Baba, dama ina so mu yi magana mai mahimmanci dan Allah"
Baban yara ya dubi inda suke, kafin ya dubi ANAS ya ce" tototo....., magana? Ta mece?"
ANAS ya ce" Baba dama Ni ne ke son IMTEE, ni ne ke so a bani dama in fara zuwa neman amincewar ta"
Baban yara ya yi dan jim kafin ya ce" Ka yi hakuri yaro, nan ba wajen da ya dace ace mun yi magana mai mahimmanci da ta shafi HALLAH ba, zan samu wanda ya girme Ni da maganar, abinda muka yanke zan neme ka in sha Allah"
ANAS ya ji dadin haka, dan haka ya yi godiya ya juya ya nufi motarsa , dama yana kaiwa har kusan karfe goma a nan saboda yana daya daga cikin masu kula da harkar gine-ginen da ake yi, yanzu haka ya tashi zuwa gida ne ya tsaya ya yi sallar shima shine ya ga baban yara , haka kuma ya ga ƴaƴansu a ciki, wato sular din nan.
Shiru baban yara yayi yana ta nazari bayan ya tafi, shi dai musulmi ne, kuma ya san a aure ba maganar wane ya fi karfin wane in dai har an samu amincewar juna da kuma soyayyar to kuwa tabas mai kudi na iya zaunawa da talaka har su yi sabo mai daraja........, sai dai haka kawai wandon jikin Anas da takalmin ya bashi tsoro.....anya kuwa kalar mijin da zai iya aurawa Imtee ne wannan??????, wando harda yar sarka a jiki??????
"Na gama baba" sulaimana ya fada da dan shaku shaku dan tsoro yake ace baba ya ji abinda yake fadawa Ashiru
Baba ya dan saci kalonsa gabansa na faduwa........
Ya rasa ina zai nufa da abinda ya ji, wa zai fadawa?????, gaba daya kansa acoshe yake hankalinsa a tashe yake......
Mikewa ya yi suka dauki hanyar gida
Tafiya ce suke yi ta kurame ba mai cewa dan uwansa kala har sai da Sulaimana ya nisa a raunane ya ce" Ni kam baba Dazu mintinka nawa kafin baban Ashiru ya fado dakin ba Salama???"
Baban yara ya dan Dube shi, sai kuma ya kawar da kai, ya rasa me zai ce, har sai da ya gama yankewa kansa cewa ba zai nuna masa ya sani ba yanzu, sai ya samu wanda zai iya yin maganar da shi an bashi shawara, abinda zai yi shine kara saka ido a kansa , shigensa da fitar sa, ya zamo ko wani motsi zai yi an sanar masa ko ya sani......dan gudun a haifa masa d'a ba ido.
Dubansa ya yi a lokacin da suka karaso zaure ya ce" Zuwan mu kenan ya shiga wurin ku"
Sulaimana harda yin yar dariya ya ce" Allah sarki babanmu dama na san ai ba zaka taba aikata aikin munafukai ba, wato labe, Allah sasaka baba"
Baban yara ya girgiza kai ya ce" Ka je wajen mahaifiyarka, ka fara kwontar mata da hankali kafin ka yi wanka.....maida hankali"
Shigewa Sulaimana ya yi yana dan waiwayar baban nasu....., shi kam wani lokacin sai ya ga kamar baban nasu na halayyar matatu, Allah Walahi baya fada baya rigima , Ama idan auntyn yara ce yanzu kuma zai dauko halayyar mutanen da basu da wani rabo.....Ama ba komai zai fada masa gaskiya cewar ya dace fa a bar masa babarsa hakan, a sakar mas uwa kawai tunda abin kiyaya ce!
Washe gari Baban yara ya tisa keyar Sulaimana rike da jakar nan suka nufi makaranta su IMTEE, a lokacin tuni sha biyu ta yi , Ama da suka je sai da suka sha zama kafin su samu shiga wajen Hajiyar.
Bayan sun gaisheta ne Aban yara da girmamawa ya ce" Hajiya, sunana malam Adamu, Ni ne mahaifin HALLAH...., jiya ta zo min da kayan nan, shine na ce yau kam zan zo in ji karin bayani dan ba zan barta kai sake ta yi anfani da su ba, bale lamarin yaran yanzu sai addu'a, ba cika jin magana suka yi na"
Anna ta yi murmushi a tausashe ta ce" Masha Allah Malan Barka da zuwa, ai kuwa kwarai na ji dadin haka, hakan na nuna min mahaifinta mutun ne mai kula, Allah ya kara lafiya....."
Ta ɗan dakata kafin ta ɗora da fadin" Idan muka ga yaranmu na hannun Iyaye masu kula, mukan ji a zukatan mu kwonciyar hankali da nutsuwa, domin ta haka zamu gane cewar zasu bamu hadin kai mu taru mu tarbiyantar da ya'ya ta hanyar da musulunci ya koyar............., "
Anna ta ɗan dana computer ta ga har yanzu da mutane sannan ta Dube su ta ce" Yana da kyau, ko ba komai iyaye su ringa dan zagayawa makarantar ƴaƴansu lokaci zuwa lokaci, ta haka ne zasu gane halin da yaransu ke ciki a makaranta......."
"Kwarai Ni na bata littatafan nan, bayan mun yi fira da ita ta tabbatar min cewa gabanan zata maida hankali wajen koyon karatunta sosai da sosai..... sannan da na tambayi kayan karatunta sai tace bata da shi, shine na bata, domin dama akoy wa'inda ake sadaka da su, na taimakon ya'ya, a ciki aka bata na bukatar ta "
Malam Adamu ya ce" Masha Allah, alhamdulilah, an gode Allah ya sa a mizani......"
Ya dan dubi sulaimana ya ce" To, Hajiya ta fada min ci gaban dake jiran mu, Ni du na damu......, Allah dai ya sa ba za'a tsaurara ta yadda talaka zai ƙasa ba????? Lamarin biyan makarantar"
Anna ta yi murmushi ta ce" In sha Allah kowa zai iya, Ama sai mai makarantar ya sauka zamu kara jin bayanin a bakinsa, abinda na sani shine shi da kansa yace bi'izinillah ba lamarin kudi bane za'a yi, lamarin neman lada ne, .... In sha Allah idan ya sauka zamu ji komai daga bakinsa, dan bai fi kwana goma ya rage masa ya sauka din ba"
Aban yara ya ce" Masha Allah, Allah ya sauke su lafiya........, Yauwa Hajiya dan Allah a taimaka a buga min lissafin kayan nan, sai in bada dan a hadowa yayar ita IMTEE din, har irin jakar , idan kuwa da yawa in sha Allah sai a ajiye min wannan din in je in tara kudin sai in kawo a bamu"
Anna ta ce" au tana da y'ar uwa kenan?, Allah sarki Allah ya yiwa rayuwa albarka......, ai in sha Allah kawai itama ta zo zan sa a hada mata, har yanzu da sauran kayan na zai gagara ba sai dai zuwa gaba idan akoy wani abin sai a siya musu in sha Allah "
Malan Adamu ya riga godiya, shi kuwa Sulaiman ya ringa mayar da kayan sannan ya dauki jakar yana sauraro har suka gama suka mike suka tafi......,
Anna ta samu kanta da sauke murmushi da jin dadin ganin jajirtacen uba......., a bayane yake bashi da shi, ama kuma kokari yake ya ga ya saka ya'yan nasa a condition din da ta dace cikin kiyaye hakin kowa.....Allah sarki, Allah ya buda wa kowa
A nutse ta dana ta sanar da security dinta a ba wasu hakuri sai da yama, saboda tana gama waya da IMAD zata dauro alwallah ta yi jiran sallar azahar.
komawa ta yi kan computanta ta turawa IMAD kira, wanda suke vidio call suna tattaunawa a kan abinda ya shifi zuwan nasa da irin yadda ake ta auna kayan da zasu zo ta ruwa da wainda zasu biyo jirgi du kayayyakin kamfani da shaguna da makarantar ne, kaya masu kyau masu tsada so luxury
____________bayan an tashi daga makaranta
Fira su IMTEE suke yi sunna dariya, ita da Fa'iza da A'isha, sai gannin Na'ima suka yi ta karaso inda suke tsaye sunna fira ta tsaya hadi da harde hannayen ta tana duban su gaba dayansu harda Fa'iza kafin ta girgiza kai ranta na susa da bacin rai ta ce" Lalle Fa'iza, to ki ce ke kika hadashi da wannan abar......, yanzu Fa'iza du irin kyautatawar da nake maki dama za'a hadu da ke a ci amanata? Kina sane cewar wannan yarinyar na bin mine kike kyale baki sanar min ba????"
IMTEE ta kalli A'isha, A'isha ta kalleta
Hannunta A'isha ta kama da nufin su yi tafiyarsu, Na'ima ta kama hannayen ta raba da karfi tana juyo da IMTEE rai bace ta rike wuyan rigarta ta ce" Ba gidan ubanda zaki je yau sai kin fada min abinda ya haɗa ki da MY ANAS!"
TO FAH
Bismillah, zo mu ci tuwo ya fi tuwon dadi in ji yan magana..........
Hajiyata ga tallah
*JAMA'A NAZOMUKU DAWANI TSARI NASAMUN KUDI TA HANYAR AMFANI DA WAYAN HANNUNKU
WANNAN TSARIN SHINE METAFORCE
MENENE KASUWANCIN METAFORCE* ????
*Metaforce kasuwancine ingantacce halattacce Wanda yake biya 100 💯 Wanda ake Gudanar dashi da wayar hannu,METAFORCE is also a part of network marketing,is a 100 percent decentralized project da aka daurasa Akan Blockchain technology Wanda babu wani mahalukin daya Isa YAYI editing,hacking ko deleting wani abu acikin sa,Kuma yanada matakai yanada rassa Wanda kowane reshi ka rike a METAFORCE to ka samu GUDUMAR DUKAN TALAUCI*🌎
METAFORCE ANASAMUN KUDI ACIKINSHI SOSAI MATUKAR ZAKAYI ABUNDA AKEBUKATA
zaku iyahada miliyoyin kudi aranadaya acikin wannan kasuwanci me albarka in sha Allah
Duk wacce tashirya zata iya tuntubanmu akan wannan number
09136899615
Hajja Data💅💅💅💅💅💅💅💅💅💅
*KISAN MUMMUƘE*
💅💅💅💅💅💅💅💅💅💅
_PAID BOOK_
*BY*
_SAJIDA NIJAR_