← Book details Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 141

Sashe 13

Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan jirgin ya tsaya ma'aikatan jirgin ne suka fara yin du wani abinda ya dace na binciken jirgin dan kula da duk wata bukata ta mutanen cikin jirgin, domin jirgi ne ba karami ba, kuma mutun hudu ne kawai ya dauko tun daga Dubai ya kawo su JIDA , mutanen nan kuwa ba kowane bane sai mutun ukun ahalin gidan SAWIRIS wa'inda kidaya ta nuna cewa a wannan shekara su ne ahalin da suka fi kowani ahali dukiya a kasar ta Saudi Arabia, wato ya'yansa ne uku maza sai guda wanda shi kuwa tun zumuncin karatu da suka yi da biyun wa'inda su ne sa'aninsa a shekarun haihuwa, ya zamo basu zubar da aminci ba, har Babar kasuwar cinikayya take wanzuwa a tsakani mai daraja da girman gaske , fahimta, addini ya zo daya har suka zamo aminai ne na kud da kud, suna tafiya irin wannan tare ta yada alkhairi a doron kasa idan lokacin su yin ya kama....................

Daya daga cikin ma'aikatan jirgin ce ta bude VVIP din ta shigo, wajen yadda ka san a cikin dakin ka kake, harda daki mai dauke da gado, da kuma wajen dake dauke da kujeru lafiyayu irin na hutun nan, lamarin dai ba'a cewa komai kana gani zaka tabbatar magana ce ake yi ta manya ba wai ta ƙanana ba

Jikinta sanye da abaya ne har kasa, saboda idan tafiya ta kama da su ne dama masu kula da su kalar shigar da ake umartarsu su yi kenan, bale ita din ma balarabiya ce kuma musulma sai hakan ya fi mata dadi sosai , ta yi musu Salama cike da girmamawa da Yaren turanci ta ce" Barka da sauka lafiya a kasar jidah sir......, akoy wani abu da kuke bukata kowani kala ne? Sannan motocin mntion SAWIRIS sun iso tun Dazu, zasu jira ne ko zamu wuce wata ƙasar?????"

Magana take yi da girmamawa sosai, ama mutun daya ya bata hankalinsa dari bisa dari tamkar zai janyota ya cinye ta danya, har sai da dayan mutumen nan wanda bai dago kansa ba tun dazu ya dago ya sauke dubansa a kan abdel bassit, wanda shi kuwa ya zubawa mutalab ido da mamakin kallon da yake yiwa yarinyar nan , har mutalab din ya bude baki zai masa magana , wannan bawan Allahn ya dan taba shi da hannu sannan ya dubi ma'aikaciyar nan a tausashe sosai ya furta" Su jira, ki je"

Kai ta ɗan langwabe zuciyarta na sake daukan dukan yannayin da muryarsa ke sakata a ciki, Muryar da ta fi daga mata hankali fiye da girgizar jirgi a cikin hazo, Muryar da idan tafiya ta kama su bai fi ta ji sau daya jal ba, ama ta fi nacin jin ta fiye da komai a duniya, yanzun ma a yan harufan da basu fi a irga ba aka yi mata kyautar magana da Muryar wace hakan ya sa ta sauke ajiyar zuciya kafin ta juya ta fice dan aiwatar da komai bisa tsari a matsayinta Na shugabar hostesss din jirgin nan

Tana fita Abdul bassit ya juyo yana dafe goshi ya ce" Wannan wace irin rayuwa ce? Ku kawai ba zaku bar mutun ya yaba abin yabawa ba? Wannan kuwa ai ta kai mace, tabas da ita ina iya yiwa Ummul basan abokiyar zama"

Abdul Fatah ya yi dariya yana nuno bawan Allahn nan ya ce" IMAD....., IMAD ......ka ga idannuwanka? Man shi Abdul bassit yana da gaggawa ne, Ama kai? Ina tsoron ka, ina tsoron lamarin ka, shi yasa nake cewa in na tashi sai na je kasar ka na dauko mata, dan na tabbata MAZNA na ganin tashin hankali a hannunka.........U seee MAZNA, ma'anar sunan BEAUTY, ga kuma haja a baban waje????..... Ina da bukatar mace a kasar ku freind"

Murmushi kawai IMAD ya yi yana shafa sajen fuskarsa sannan ya mike a nutse da yan yatsun sa ya musu alamun su mike su wuce

Kasantuwar kasar Saudiya shigar maza kala biyu ce, wace in lokacin hadj ko umara ta yi zasu yi, irin na kowa domin ba bambancin ga na mai kudi ko na talaka, da kuma wace in lokacin ya wuce zaka iya gane mai kudin ka kuma iya gane saisai saisai wato shigar Thawb, doguwar jalabiya fara kal, da ghutra, hirami da Agal, wato bakin igiyar nan da suke ɗorawa saman hirami, wanan shiga ita ke nunin waye kai a fanin dukiya, sai agogon hannunka da kuma takalmin kafarka........, shigar da ta riga ta zama sabo a jikin IMAD koda yana garin su ne, dan da wahala ka ga ya saka wani abin da ba su ba, ya riga ya saba da su tunda yayi karatu a kasar .

A nutse suke tafiya, a tausashe sunna yiwa masu marabatarsu Salama har suka fito wajen motocin dake jiran su tamkar an zo tarbar mutun ashirin

Sun saba idan sun yi tafiya tare suke shiga Mota daya su Dukansu, ama yau sai IMAD ya ki shiga tare da su a mota daya, ya nufi wata motar yana ɗan daga musu hannu ba tare da ya musu bayanin komai ba ya shige yana amsa gaisuwar da direban motar ke masa sannan a tausashe ya ce" Ka kai ni hotel ROSEWOOD"

"Ok sir" ya fada shima a tausashen sannan ya ja motar suka dauki hanya

A lokacin da suka karaso fantsamemiyar hotel din da kyanta, da tsarin ta kawai ya isa ya sanar maka cewa tana daya daga cikin manyan hotel din da suke da mugun tsada a kasar, komai nata luxury ne, idan baka kai wani baba ba Bama za'a taba bari ka shige cikin filin ta ba, suma shige ya tsayar da motar, ya kama marfin ya bude ya ce" Ka je kawai, zan karaso......."
Sai ga Abdul Fatah ya tsaya a gabansa yana rage girman idannuwansa ya ce" Man, me kake nema a nan? Inace Aby ya sanar maka kar ya kuma jin ka a hotel, hakan ya sa du wani gari a cikin kasar nan ya sama maka takardun damar mallakar gida naka kamar yadda ya sama maka ta zaman kasa a duk lokacin da ka so?, me zaka yi a Hotel......? Ya rab, ya rab, na san dai baka ......baka, plz tl me, me zaka yi a hotel?"

IMAD ya dafe gaban goshi cike da mamakin ashe suna biye da shi? Kai mutanen nan an yi yan saka ido , shi da ya so kawai sai sun hade a gidan sa ji inda ya je dan yayi niyar kashe wayarsa domin Abdul Fatah akoy shegen sarkafa ya ga damar yace an sace shi ne su shiga nemansa a garin nan, ashe baima bari ya gudun ba

Fitowa ya yi yana ture shi hadi da sakar masa harara ya ki ce masa komai

Ai kuwa ya bi bayan shi yana fadin" Ba zan taba bari ka dau wata hanyar ba, dole zan bi ka, ba zan iya bari ka shiga wajen nan kai kadai ba, kuma ko wacece ke ciki yau sai na daureta dan na tabbata so take yi ta yi maka fyade ta lalata mana kai, aikin banza, lalle bata isa ba mu je din

Yana surutun nan har suka shige lft ya haya da su cen sama sannan suka sake takawa har kofar dakin ya dakata ya dana abin kofar dakin sannan ya juyo ya harde hannayen sa yana kallon Abdul Fatah da ya gyara tsayuwa yana fadin" Eh ko waye ya fito, in mace ce yau ban san yada zan kare da ita ba, idan namiji ne kuma lalle zan fada masa karya yake ya rabamu da kai, kai dan uwanmu ne, kafar ka kafar mu, na lura da Sajid bin Umar yadda yake kokarin sai ya haɗa hannun jari da kai harda cewa wai kamalarka na burge shi, shi matsiyaci sai dai ya yi ya gama ba zaka yi kasuwancin da shi ba, ban yarda ba....ka san Allah IMAD......Bama za................."

Bude kofar da ta yi fuskarta dauke da murmushi ya saka Abdul Fatah dan zaro ido hadi da kallon IMAD ya dago hannunsa ya matso sosai daf da shi kasa kasa ya ce" Sai ka ce min matarka ce ta zo ko?"

IMAD ya tabe baki ya Dube shi ya ce" Ai baka bani damar magana ba"

Abdul bassit ya juyo ya dan sakar mata murmushi ya furta" Barka da sauka , koma rufe gayanan zuwa"

Itama komawar ta yi ta rufe din dan ko yanzu da zata bude sai da ta sako nikaf, bata san Bama yaya aka yi ya ganeta a cikin nikaf din , dan kuwa kashedin da mijinta ya mata ciki harda ko da wasa baya son abinda zai hadata da wanda ba hurumin ta ba, ko wanene........

Kasa yayi da muryarsa sosai ya ce" Ama, kai ba zaka iya hakura da mace ba wai?"

IMAD ya girgiza kai hankali kwance

Abdul Fatah ya zaro ido yana jimke hannu ya ce" Allah ya shirye ka"

A hankali ya furta " Ba amen ba, in dai ta fanin nan ne, idan ya hana min abin nan me ya rage na jin dadin? Ai kawai ya karbe ni, gwara ya maida abinsa kusa da shi , dan ya fi so na da ku"

"Innalilahi wa Inna ilaihi raj'une " Abdul Fatah ya fada da dan karfi

IMAD ya furta" Hakkun"

Abdul Fatah ya sake zuba masa ido, alamu sun gama kara ganar da shi cewa shine mai hargagi, IMAD na hargage shi cikin Salama, sai kawai ya juya da nufin tafiya sai kuma ya dawo kasa kasa ya ce" In dai zuwa ta yi dan ta tafi da kai Nijar ba zai yiwu ba, ba fa zaka je ka yi ta zama a kasar nan ba mu muna nan"

IMAD ya rike hannunsa ya dan girgiza kafin ya saki ya ce" ka gane yanzu Ban gane komai sai na shiga na sauke...., zamu yi maganar daga baya.....ama ni ai ba d'anka bane ka sani, zan je inda na so a lokacin da na so......, in sha Allah karshen watan nan zan je Nijar ne kuma zan jima sosai saboda Anna ke bukatana a islamiyarta.......zan je in yi teachng man.......by!" Daga haka ya dan daki kirjinsa sannan ya shige dakin ta hanyar murda kofar
Chapter 13 · 0% Book details