Sashe 111
Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
IMAD da tarin takaici ya Dube shi
Abdul bassit ya ce" A'a fa, ba ina nufin kana sonta ba, dan in sani ne, ka san komai na rayuwa ya zama ana taka tsantsan ya fi........, yanzu ka tabbatar min saboda idan har kai baka yi Ni wallahi ina yi, kuma fa gaske nake, ya Subahanalah wai ka ga yarinyar nan da kyau kuwa?"
A yanzu duban da ya tsare Abdul bassit da shi sai da Abdul Fatah ya sune kai yana fitar da yar siririyar dariyar da ta rike masa wuya
Ya maido dubansa kansu, duba na ido cikin ido, sai dai idannuwan IMAD a kausashe suke sosai da sosai
Kai ya dauke yana murza yan yatsunsa cike da tarin takaici
Abdul bassit ya sassauta murya ya ce" Ka yi wani abu mana, ka ga kai ka hana Ni neman auren FARHANA, to tunda ga wata a yi da Ni"
Yanzu kam kasa yin shirun yayi yana dubansa ya ce" wani irin kana ciki, cikin ina?, plz ka bar maganar, yarinyar da ko yarenka bata iya ba ka aureta ku yi fira yaya da ita"
Abdul Fatah yayi murmushi ya ce" To wannan ai ba shi ne hujjar da zai sa a ki auren mace ba, Ni da kaina ina yi mana kwadayin kalar wannan a cikin mu daya ya samu, tunda kai baka ra'ayin haka gaskiya a shigewa Abdul bassit gaba, lalle wannan ya dace ace an samu iri irinta a cikin mu......"
Yanzu kam da mamaki ya dubawa Abdul Fatah ido, to ko a cikin tafiyarsu daga shi sai Abdul Fatah wajen kamewa da gujewa aikata zunubi ai, ama meye yanzu yake son aikata wani abu mai kama da katon zunubi kansa tsaye?
Agogon hannunsa ya duba yana sake dane harshensa, cike da takaici yana hangen kaffafuwanta da tunanin ba ga irinta nan ba, har zata sa malami guda mai tsoron Allah faɗin wai ya dace a samu iri irinta a cikinsu?, aikin banza yarinyar nan dai ta haɗa masa bacin rai a banza a wofi, du yadda ya karar da rayuwarsa wajen kare Farhana dan kar rashin jinta ya dagawa Anna hankali yarinyar nan sai ta sa hankalin Anna ya tashi ko??? Mtssssss!
Mikewa Abdul Fatah ya fara yi yana murmushi ya ce" Tashi mu je wajen Uncle din, ka san abih yace kar ya jima, dan a ji komai na sadaki da kuma ranar da aka tsaida fa"
Sam bai wani gane abinda ya fada gaba daya ba, sai ce masa yayi" Gani nan zuwa, ku je"
Abdul bassit ya mike yana budewa, ya dan yi gaba kadan ya ɗan leka Nur dake zaunenta tana kokarin hada harufa dan ta yi karatu ya wani yi murmushi ya kanewa IMAD dake kallon sa ido kafin ya yi gaba yana ta murmushi kala kala ya bude kofar ya sake tsayawa yayi wata mika ta iskanci sannan yayi gaba
Abdul Fatah kam kafa ya daga ya fice da sauri dan shi da kansa sai da ya zarro ido yana kallon Abdul bassit fa tarin mamakin shi kam ya iya neman fitina kala kala ..........
Haka kawai ransa ya ringa ɓaci
Tsabar bacin rai sai kawai ya ringa girgiza kafafuwansa yana cije lebensa cike da tarin takaici da bacin rai ya dubi inda take ya ce" Ke zo nan"
Shiru bata mike ba, saboda har ga Allah ita bata ma san wai da ita yake ba
Ransa a wani bacen ya ce" Nur zo nan!"
Sai yanzu ta dakata ta leko dan tabatarwa da ita yake
Mikewa ta yi ta ajiye litafinta, Anna kuwa na hangen haka sai ta fito rike da fruits din nan
Karasa ta yi ta amshi fruits din dake hannun Anna ta kawo ta ajiye kusa da shi tana kokarin amsa kiransa ya Dube ta ya ce" Me yasa ke Bakya jin magana ne? Me yasa idan kika tashi kowani lokaci kike son daka matsatsun kaya ne?
Da tsoro ta ɗan mike tana dubansa, Anna ma na dubansa, Ama bata ce komai ba
Ya dauke kansa bai ce musu komai ba har Anna ta zauna tana dubansa da ido ta yiwa Hallah alamun ta zauna domin bata yi niyar ce mata ta tafi ba, so take yi ta zauna
Da kula ta ce" sorry Andadi, me shigar yarinyana ta yi ne?, Ni Bama wannan ba, Andadi yaya maganar kaurar da na maka ne?......."
A hankali ya kawo dubansa kan Anna, duba irin na tsanaki mai tafe da tarin gajiyawar da zuciyarsa ke ciki
A tausashe ya ce" Anna, zamu kaura, na sa a min cigiyar ginane idan AKOY, sai mu je ki gani in ya yi sai mu kaura"
Anna ta hade fuska tana dubansa ta ce" Ba zaka batun mu kaura ba kenan? Na fada maka Ni ba zan kaura da ku ba, Ni da y'ayana kawai zan kaura, ka daina maganar zamu kaura!"
Hannayen Anna biyu ya riko, a tausashe sosai ya furta" Anna, yaushe na taba raba waje da ke in ba na yi tafiya ba?"
Anna ma a tausashe ta ce" ANDADI, ai ba wani wajen zan tafi nesa da gari in Barka ba, ina da bukatar raba waje da iyalinka......."
Nur kam murmushi ta samu kanta da yi, kwarai yana cikin mamakin irin yadda yake da taushi a yau....., yanayinsa na matukar bata mamaki a yau
Shigowar MAZNA ya sa du suka kai dubansu kanta, kuma ba ita kadai ta shigo ba, ita da JAUHARA ne suka shigo, a yau ita da kanta JAUHARA cikin shigar da zasu iya cewa basu taba ganinta da irinta ba
Kwarai ganin Nur zaune ya kusan mantar da MAZNA abinda ya kawota, wanda yar uwarta ta zaunar da ita tun dazu tana sanar mata cewar gwara ta zo ta samu Anna ta fada mata abinda take ciki, idan Anna ta masa magana ko menene zai saurara, du zafin abu kuwa zai yi hakuri ne, wannan dalilin ya sa suka taho bayan ta kara jaddada mata gwara ya ji a bakinta da ya ji a bakin wani ......................
Jauhara na ganin ta yi turus ta kama hannunta tana matsawa da karfi a Boye, hakan ya sa ta dubi fuskarta da sauri
Da ido ta yi mata alamun ta wuce mana, hakan ya sa ta kai dubanta kan Anna da ta Dube su da kula tana fadin" MAZNA, ku karaso mana......yanzu kuke tafe????"
Sake duban Anna yayi da jin maganar yanzu suke tafe kamar wasu da suka taho daga wani garin?......... Ko dai Hausar Anna ce a haka?
Da kyar MAZNA ta hadiye abinda ya tsaya mata a kahon zuci, ta karasa, sai dai idannuwanta na kan NUR wace ta dauke kai tana tuna abinda ya faru da su kwanaki, cike da tunanin kar dai yanzu ma ta yi tunanin wani abu? Kai da ta fada mata gaskiya cewar ba wani abu a tsakaninta da mijinta dan Allah ta bata lafiya............
Ta karaso daf da Anna, sai dai ta rasa ta yadda zata fara magana, hasalima ta fi ganewa ta bar maganar sai baya nan, sai dai Jauhara ta sanar mata duk rintsi ta yi maganar nan yanzu saboda ta san waye Aliyu, duk wani abinda take boyewa sai ya bankado shi yau, dan haka ta fara fadi sannan ta nemi yafiya tun guri bai kure mata ba
Anna kam sai ta nemi mikewa dan ta basu waje, saboda yadda ta ga ta yi kikam a kanta
IMAD dake dubanta ne yace" ke lafiyarki kalau kuwa? Ya zaki tsaya kina kallon wannan baki ce komai ba?"
Dubanta ta maida kan IMAD din, sai kuma ta kalli Anna da ta mike
A hankali ta ce" Anna ina kwana, ina gajiya, Anna dan Allah zauna"
Anna ta dube ta, yadda ta yi maganar muryarta na tafe da salon amo kala biyu ya da ta dake zuba mata ido na dan lokaci..............
Sam bata ga Inna na barci ba, dan haka bata wani damu da Inna ma na wajen ba,
Sake duban Nur ta yi ta ce" Ki tashi magana zan yi da mijina da kuma Anna !"
Irin yadda ta yi maganar cike da bada umarni ya sa Nur yi mata kallon uku kwandala ta watsar sannan ta ki tashin
Dan shiru ne ya wanzu a wajen, shi kam ya rasa me zai ce mata, ya rasa ma tunanin me zai yi.............
Anna ta yi dan murmushi saboda yadda NUR ta maida kafa daya kan daya ma abinta ta ba banza ajiyar MAZNA, a tausashe ta ce" Tashi ki je kicin ki fara gyara mana abinda zamu girka yarinyata"
Nurmikewa ta yi ta wuce kicin din, bata kara ko second daya ba, kuma bata yi gardama ba, hakan ya sa ya bi bayanta da kallo cike da tunanin wannan ma an yi yar rigima ta kirki
Maido dubansa sunansa yayi kan MAZNA wace ta kamo hannun JAUHARA kafin ta duka kasa kanta a kasa ta ce" Anna, dan girman Allah zuwa na yi in fada maki abinda yake faruwa da Ni dan ki taya Ni bashi hakuri, saboda a halin da nake ciki a yanzu ina cike da matsanancin tsoron abinda yake iya yankewa.....Anna "
Da mamaki yake dubanta, a hankali ya ce" MAZNA, me yake faruwa? Me zaki fadawa Anna ?"
MAZNA ta girgiza kai da sauri ta ce" Akul, dan ALLAH ka yi hakuri, du abinda yake faruwa da dalili Akul, abinda ya da ka ga har tsayin lokacin nan ban iya baka hakinka ba da baban dalil....."
"Ya Salam......" Ya fada yana fitar da idannuwansa a kanta cike da mamakin furucin da ta yi a gaban Anna
Idannuwansa ya mayar ya rufe a hankali cike da jin matsananciyar kunyar Anna, harma ya mike da nufin tafiya ya bar mata wajen
Wannan wace irin mace ce da sam bata da sirri
Dama MAZNA na iya budar bakinta ta yi maganar haki irin na aurataya a gaban Anna?
Ko tana tunanin ko mutuwa zai yi dan rashin abin nan zai iya yarda Anna ta ɗan dalilin da ya kashe shi ne?
Farkon tashi ta so nuna halin rikicewar nan Tata, hakan ya sa Jauhara a hankali ta ce" Ki nutsu aunty, idan kika rikice kika fadi abubuwan da basu da wani anfani sake dagula komai zaki yi"