← Book details Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 141

Sashe 73

Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan rubuce rubuce ta nemi jin abinda ya faru da ita kafin su zo, a nutse IMAD ya sanar mata komai hakan ya sa ta sauke ajiyar zuciya tana dubansa da girmamawa irin ta aljihu ta ce" Sir, a gaskiya a yanzu zamu Sakata dakin observation ne, ta yadda zamu sake yi mata gwaje gwaje sosai dan mu gane abinda take ciki, domin suma ne ta yi mai karfi ta yadda kwakwaluwarta ya tsayar da baban motsin dake iya ba gabobinta damar motsawa da farkawa baki daya....., kuma ka ga ba hawan jini bane, a bayane dai a yanzu kam ba zamu ce ga abinda ya hanata farkawar ba, Ama na fi daukan haka da chok din da ta samu....., idan an yi dukan binciken da ya dace zamu iya gane abinda yake faruwa har mu yiwa tufkar hanci........, ina fata zaku iya daukan dukan diyar kudin da binciken lafiyar zata buƙata????"

Ita da kanta ta fadi maganar kudin dan a bayane ta gane matar mutumen nan ce, wato Malan, kuma alamunsa sun nuna ba mahaifin IMAD bane, Ama kuma suna tare, ta yiwu taimaka masa suka yi ko makamancin haka

Huci ya fitar a hankali kafin ya furta" Dukan abinda ya dace a yi mata a fara, idan ma za'a fitar da ita ki min bayani ........"

Daga haka ya dana Numbar Aliyu

Tana fara ringin ya nemi izinin shigowa , aka bashi dama ya shigo din , yana zuwa ya ja da girmamawa yana sauraron IMAD

A nutse ya ce" Asibitin nan ita ta fi kusa da Ni ne ko tana da kwarewar da ya dace ?"

Da girmamawa ya ciri Babar wayarsa ya dano Google ya dan rage tsayinsa ya nunawa IMAD ya ce" Sir na yi binciken asibitin da ta fi kusa da mu sannan wace ta fi kwarewa....... shi ne aka bani sunan nan, kuma na dana gps ya kawo ni....., idan bata yi bane sai in cenza wata yanzu yanzu"

Likitar nan dake kallon su tana kara tambayar kanta eh lalle wani baba ne a garin nan....... ta yi gaggawar fadin" Sir, in dai wajen kwarewa a aiki ne, ina da tabbacin a nan kun zo inda zaku samu abinda kuke so, bari yanzu yanzu in yi kiran wasu manyan likitocin su zo mu rufu a kanta dan a yi dukan abinda ya dace........, zamu yi bincike sosai muna da kayan aiki masu daraja a nan sosai..........kaf Niamey nan ne Numbar 1 a wajen kwarewar aiki da kayan aiki, in sha Allah ko menene zamu gani kuma zata samu lafiya"

Idannuwansa ya lumshe bayan ya gama sauraronta sannan ya dubi Aliyu bayan ya mike ya ce" Dukan abinda suka bukata ka saka musu.....cashhhhj, ko check, ko trensfer..... Aba Bismillah "

Ya yiwa Malan nuni da ya mike su je

Malan ya mike yana ta sauke ajiyar zuciya ya dubi likitar dake ta rawar jiki a lokacin da ta biyo su ta ce" Sir, a yi kokarin kawo mata yarinyar nan kusa, saboda idan ta farka koda yaushe zamu so mu ga irin réaction din da zata yi idan ta ga yarinyar"

Tuni IMAD ya yi gaba, sai Malan ya amsa ya bi bayansa da sauri suka karasa wajen da aka ce su zauna a nan su yi jira, waje ne na alfarma wanda aka tanada domin mutane irinsu
Waje ne mai dauke da tsafta da tsari ga kuma sanyin AC da kujerun alfarma ........

A nutse Malan ya karaso ya zauna a kujerar dake kusa da ta IMAD , a tausashe ya ce" Elhaji , ka yi hakuri ka ji? Na san abin nan na damunka sosai, Ama ka yi hakuri komai zai wuce ka ji ?"

Murmushi ya yiwa Malan , da carbin dake jikin yatsarsa ya duba time dan ya ga idan lokacin sallar la'asar yayi, ya ga da saura hakan ya sa ya ci gaba da jan carbin kafin ya dan dakata a hankali ya ce" Yarinyar nan, kamar bata damu da ganinku ba sam"

Malan yayi murmushi ya ce" A'a fa, na tabbata zata damu da mu sosai, a yanzu abin ne ya zo mata kai tsaye a ba zata, kana ji fa abinda shi baban nata ke fada cewar basu taba koda hasashen cewar ba su ne iyayenta ba har sai da ya'yan nasu yace yana son ta, daga nan ne hankalinsu ya tashi har suka fara tsamtsamtar nan, ka ga a hannu mai kyau take shi yasa da aka ce mu muka haifeta bata bar jikin matar nan da gudu ta nufo mu ba, abinda na gane shi ne tana da shakuwa da matar nan sosai, haka kuma tana da shakuwa da y'ar uwarta da kuma mahaifinta, wato shi Malan din, a hankali zata yarda da mu muma, kuma a hankali zata so mu, kar ka ji haushin yadda bata zo inda mamanka take ba, a jiya ne fa ta ji maganar nan, kuma a yau ta ga abin nan, sai an musu uzuri su duka ka ji???"

Kai ya gyada a hankali ya ce" Ana iya kawo ta, addu'ar da nake yi, Allah ya sa idan ta farka ta ganta ta samu lafiya, "

Malan ya yi murmushi ya ce" Ni da kaina abinda nake ta fata kenan, Allah ya sa idan ta farka din ta zamo cikin nutsuwarta, bari in je in sanar da Anna sai ta sanar da Anas ya kawo ta"

Daga haka ya mike ya fice ya bar IMAD na ta addu'arsa .........

Malan ya sanar da Anna abinda likita yace, hakan ya sa Anna daukan wayarta cikin jakarta ta danawa ANAS kira ta sanar masa ya je gida ya dauko su Farhana ya kawo mata su nan.

Daga nan ta fuskanci su Malan da suka sanar mata zasu je gida su dawo saboda an bar gidan ba kowa, ga Malan na Magarya zai wuce ne shi ma, haka kuma bayan sun fada Malan Aban yara a raunane ya ce" Hajiya, nace su su A'isha din, za'a bamu su kuwa??"

Anna ta Dube shi da mamaki ta ce" Malan, su A'isha ai naka ne, babu wanda ya isa ya maka fin karfi da su, babu wanda zai shiga tsakaninka da su, abinda ka yanke za'a yi da su, idan har ka bamu dama zamu so mu zama ahalinsu mu ma......, ka ga abinda docter yace yanzu idan ta farka ta fara haduwa da A'isha, shi ne ya'yan nasu yace a daukota, idan har ka amince za'a kawo su nan din har ku dawo????"

Aban yara ya gyada kai yana jin nutsuwa na shigar sa a tausashe ya ce" Na amince Hajiya, Allah ya saka da alkhairi"

Anna ta yi murmushi ta dubi Aliyu ta ce" HAIDAR, ka kai su gida plz, ina nan du abinda aka bukata zan yi kafin ka zo"

Cike da girmamawa ya ce" Ok Mam "

Sannan ya dan jira suka fara fita , saboda ya san za'a fadi wani sakon ne,

Ai kuwa suna fita a tausashe Anna ta ce" Idan ka kai su, ka jira ya gama sai ka kai shi inda zai dauki mota, ko ka hada shi da wani direba a cen gida, in ya kai shi a hada masa da alkhairi mai yawa "

Ya sake rage tsayinsa ya furta an gama kafin ya fice ya je ya bude musu motar suka shiga ya dauke su ya nufi gidan Aban yara da su bisa kwatancen da suke masa.

A bayi suke , A'isha na tsaye da katon madubi tana haskawa Nur yadda Farhana ke wanke mata kai, idan ta ɗan ja sai sun sha kokowa kafin ta bari a ci gaba da wanke mata, tamkar baby sam bata son abinda zai taba lafiyar kanta, Farhana kuwa ta maida hankali sai da ta wanke mata kan nan tassss sannan ta ciro sabon tawul ta bata ta ce" Yi wankan ki fito muna jiranki"

Suka fice suka bata waje ta rufe bayin da kyau sannan ta tube ta shiga yin wankan cike da jin dadin irin kanshin da sabulun wankan ke yi, wato shower gel , ga wani santsi da take ji a fatarta du idan ta kwaba, hakan ya sa ta ringa diba tana shafawa a ko'ina na jikinta kafin ta dauki abin wanka sabo da Nur ta bata ta shiga darzar jikinta sosai da sosai

A dakin kuwa Nur ta ba A'isha mai, da abin shafa sannan ta zauna tana duban ta ta ga tana dan gyara fuskarta Ama ba yadda ya dace budurwa kamar ta na yi ba, dan haka ta taso ta ce" A'isha, bari in gyara maki fuskar nan, so nake yi idan muka sauka a kasa gane ku a falon nan, in gani.....wai hala bakwa kwaliya ne na ga kin kasa saka kwali da gira mai kyau??????"

A'isha ta yi murmushi ta gyara Farhana ta shiga gyara mata fuska, harda hodar ruwa kadan ta shafa mata sama sama dai-dai da fatarta sannan ta shiga kame mata kanta da ta shafa mata mai ta caje mata shi da kyau domin mu ita suka fara wankewa kan, ta yi wanka sannan suka wankewa NUR

Bayan ta gama sai kawai A'isha ta zuba wa fuskarta ido har tsigar jikinta na tashi tana kallo kamar ta ga bakuwar halitta a gabanta

A hankali ta dubi FARHANA , a sanyaye sosai ta ce" Shekara ta Ashirin da daya, na kusa rufe da biyu, shekarar NUR ashirin yanzu, tana cikin da daya.........Ama daga NUR har Ni bamu iya wannan abin ba........., bari ki ji, sam bamu taba yi ba sai shekaran jiya da Auntynmu tace maza sai mun saka kwali, aka yi ta kokowa a gidan nan sai da muka saka din ta bar mu muka tafi makaranta ido yana ta mana ruwa, saboda bamu saba ba, bamu iya ba, mama cewa take yi bashi da wani anfani, bayan Ni ina matukar sha'awar in ga na saka kwali, idan na ga Fa'iza ta shafa hodo sai in ji ina ma muma zamu samu abinda zamu shafa kamar hodar nan, kai da mun tabbata cewar mu ma yan mata ne......"
Chapter 73 · 0% Book details