← Book details Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 137 OF 141

Sashe 137

Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da mamaki ta dubi Aban yara ta ce" Malan, wai Ni kake wulakantawa? Malan dan na zagi Imtee kake wulakanta Ni? Ita din Imteen ka tabbata y'arka ce? Daga ita har sulaimanan na tabbata cikin su ta karbo a waje ta kawo gidan, domin kuwa in cikin kake iya yi ai da ka min ko??????, ke IMTEE wuce mu je gida, aure? Hehehe aure ma zaka mata bana nan? Ai baka isa ba, baki isa ba, kuma babu wanda ya isa ya mata aure sai na yarda, ai ba zata yi aure ba, ai ba zaka taba samun darajar ganinta da aure ba, ina mai tabbatar maka ba zata taba yin aure ba, ke wuce mu je gida, kai kuma zaka fito daga nan din ne ai, Malan Ni da kai sai dai idan gawar daya za'a dauka a bar daya!"

" Ki kama mana baki a nan, macuciya azaluma da bakya jin kunyar Allah Bakya tsoron Allah!"

Muryar sulaimana da sai yanzu ya karaso ta karade falon ransa bace

Ya dora da fadin" ke da kanki idan kika kalli mahaifiyarmu kin san tsaftataciya ce, ke da ba dan zato zunubi bane da sai in sha rantsuwar cikin ma kin nemi amsowar, samu ne baki yi ba kika je kika dauko yar mutane kika gudu......, azaluma da bakya tausayin kanki baki san mai sonki ba"

Imad kalonsa yake yi a nutse, duda irin yadda jikin Nur ke rawa na daga masa hankali

SULAIMANA ya dora da fadin" Sai dai ki mutu, kin ga NUR, tana da aure kuma ga mijinta nan, abinda kike fatan ki goya sai dai ki goya na halak domin yanzu haka da shi a jikinta kuma ga ubansa nan...., sannan A'isha da kike gani, um aishana Ni aka ba abina....., ke fa baki sani ba kin ga gwara da kika ɗauke A'isha, da ke kika haifeta ai da kin cuceni wallahi........, kashedin da zan maki idan kika je gida zama, ki kiyayeni ki kiyayi shiga harkar iyayena da kanaina, kin san Allah na kai matakin da zan iya tataka......"

"Sanu rasa kunya , sanu sulaimana, rashin kunya zaka yi a gaban sirikanka?"
Auntyn yara ta katse shi da dan karfi, Inna kuwa kicin ta nufa ta dauko muciya du ba wanda ya kula da ita, dama tana burin haduwa da matar nan kafin ta mutu, ashe dai zasu gana?

Mama ta girgiza kai da takaici ta ce" Auntyn yara, haka kika zauna da wannan matsiyaciyar????"

Jikin maman yara rawa yake yi kamar me, ta dubi IMAD ya fi a irga, ta dubi NUR

Kai da kyar ta iya bude bakinta ta ce" Wai, wai, wai da gaske wannan dan iskan yake kai ne mijin HALLAH?"

Murmushi IMAD ya sakar mata yana sake duban ta, tun dazu bai katse mata hanzari ba dan so yake yi Nur ta ga komai a idannuwanta, ai kuwa ihu mama ta saka tana dane wajen zuciyarta hadi da silalewa tana fasa kuka tana faman fadin" Mutuwa zan yi, mutuwa zan yi, wayo kirjina, wayo kirjina mutuwa zan yi, wayo zan mutu, mai kudi IMTEE ke aure?, mai kudi take aur....."

A rikice Nur ta fashe da kuka, ta nufi inda Mama ke burgima da nufin kama ta

Kusan a tare, Anna, auntyn yara, da IMAD suka nufeta, Anna ta riko hannayen ta, Auntyn yara ta rungume nata hannayen a kirjinta hawaye na bale mata, IMAD kuwa ya shige ya tare gabanta yana duban fuskarta

Anna zata yi magana suka ji an shiga tafkawa maman yara muciya , cikin fada Inna tace" Tunda ke ja'irar halitta ce bari in zane ki, munafuka barauniyar ya'ya"

Ido IMAD ya zarro kafin ya karaso ya rike Inna yana dubanta a tausashe ya ce" Inna maman Nur ce fa"

"Uwata ita da Nur din, aikin banza sakeni ka ga in ƙaryata" Inna ta fada a zafafe

Malan dake duban Maman yara yayi murmushi ya ce" idan kika gama haukan, kina tashi sai ki je tasha ki dauki mota ta kai ki kauyen ku, kafin ki tafi ki amshi takardar sakinki, mai sheda kunce igiyoyin aurena a kanki kwaya uku, kuma ki ji da kyau zan fadawa hukuma ko da wasa kika nufi gidana ko gidan y'ayana su shiga tsakanina da ke, idan duniya ce kuma, ta ishe ki riga da wando gaki gata...."

Daga haka Malan ya fice daga falon gaba daya

Auntyn yara kuwa, sai ta kama hannun Nur a hankali ta jata ta yi hanyar kicin da ita wace zata fitar da su ta kai su bangaren da yake nata a yanzu.

Kamar da wasa, bakin maman yara ya shiga jirgewa,

Ihun kukan da take yi na farko sai ya zama na gasken gaske , sai dai sam ya ki fita, har ma gefen jikin ta gaba daya ta kasa motsawa

A rikice take bin Sulaimana da kallo da ya zo kwasarta, haka kuma ta kasa bude baki tace masa jikinta ya ki amfanuwa , gaba daya ma sai ta rikice ta kasa motsi, Bama zata iya bane

Miyau ya fara dalalo mata, wanda Anna ce ta dakatar da Sulaimana tana duban Maman yara a hankali ta ce" Andadi, atack take yi fa, duba , atack ne"

Idannuwansa ya zuba, sai dai lokaci daya tuni hannayanta suka sangaye , kanta ya karkace, idannuwanta suka sake fitowa waje ruku ruku

A hankali ya furta" Innalilahi wa Inna ilaihi raj'une....., sulaiman, ajiyeta....., Aliyu yi kiran ambulance "

Aliyu ne ya juya dan ya yi kiran ambulance, Sulaimana kuwa ya zuba mata ido, mama kam dama ita ma tuni ta ja A'isha da Farhana suka bi bayan su auntyn yara

A karshe dai mota ta zo, aka kinkimi maman yara, wace ta yi hannu daya kafa daya da kamani mafi muzanta, domin harta kanta ya karkace , yannayinta gaba daya ya cenza, ga bakin yanzu yanzu ya juye, sai dilalar yawu da ruko ido, wanda kana gani zaka gane so take yi ta yi magana, so take yi ta yi kuka, Ama ta kasa sai wani irin nishi take yi mai karfin tsiya

Likitar da ta tsaya ce da yannayin ba dadi a fuskarta a tausashe ta ce" Sir, wannan fa tana daf da shiga coma, zamu tafi da ita, Ama gaskiya dai dai dan kawai a bata kula dai yadda hali ya bada, Ama a gaskiya adu'a ta fi buƙata da komai yawanci irin wannan cas din basa tashi, a zo a saka mana hannu zamu wuce"

Daga haka ta juya da sauri, inda Aliyu da Aban yara da sauran likitocin biyu suke shi ma sun masa bayanin nan, kuma yace a tafi da ita, zai je kauyen su ya cigiyto wanda ya mata saura ya sanar musu, shi kam sai dai alfarma irin wace zai iya yi saboda addininsa, bayan wannan babu wani abu da zai iya dubawa tsakaninsa da ita, wanda hakan ya daga hankalin Sulaimana matuƙa, bai taba ganin mahaifinsa cikin fushi haka, ba, lalle mama ta kai abansu bango, da kyar suka lalaba shi suka shige mota suka bi bayan Ambulance din, wato sulaimana da Aliyu da abansu, Shi kuma Da dan sauri ya zagaya ya nufi bangaren da aka yi da nur

Yana shiga ya samu Auntyn yara na fada kamar zata ari baki, Nur na duke tana kuka, A'isha na rike da ita tana kukan itama, Farhana na tsaye kanta a kasa, mama na tsaye tana ba auntyn yara baki, Ama kamar ba auntyn yara ba, yau ta juya fada take yi kamar me

Rai bace ta ce" Zuwa yanzu, abin nake ya tashi daga sangarta irin ta lalacin autani, ya tashi daga rashin wayo , ya koma rashin hankali, bari ki ji HALLAH , baki isa ba, idan na barki kin sake duban matar nan sai ki ce ba Ni na haife ki ba!, na gaji, na gaji da natacen halinki a kan matar nan, to ko asiri ta maki ki ji zan iya baki baya a kan lamarin ta! Hallah ki ji zan iya....."

"Aunty plz......." Ya fada a hankali yana hade hannayensa hadi da karyar da kansa, muryarsa na yin sanyi ainun, jikinsa na mutuwa sosai, tashin hankali na shigarsa

A hankali ya ce" Aunty, dan Allah ki yi hakuri, ki yafe mata , in sha Allah ba zata kuma ba, auntu, ba zamu kuma ba, ko NUR? Daina kukan ki ba auntu hakuri kin ji?"

Aunty na haki, ta Dube shi, ta dubi nur, sai kuma ta fita da sauri ta nufi bangaren Anna tana fashewa da kuka

Da sauri Mama ta bi bayanta bayan ta musu alamun tana zuwa

A hankali ya karasa ya kama hannunta ya mikar da ita, sannan ya dubi su Farhana ya musu alamun su tafi

Sumui sumui suka fice daga falon ya rage shi da ita

A hankali ya rungumeta a jikinsa, yana dan bubuga bayanta, cen kasa yace" Idan dai haka zaki ringa yi, zan mayar da ke, domin ba lalle in iya hakurin ganin kukan ki koda yaushe irin haka ba, ki duba ki gani yadda aunty ke kuka, me yasa kike son saka damuwa har haka a ranki ne?"

A hankali nur ta sake rungume shi a jikinta,muryarta na rawa sosai ta ce" Na tabbatar a yau, na yarda da abinda nake son yarda a yau, na yarda cewa Mamana bata taɓa so na ba, burinta in lalace in wulakanta, burinta in bi duniya , ta nisanta ni da mahaifiyata ta sa na saka mahaifiyata kuka ba dare ba rana, ta hana min gane kaina, a karshe du dan ta ga na tagayara dan kawai mahaifina ya auri mahaifiyata an same mu? Shin waye mai badawa a duniya ne? Wace irin rayuwa mahaifiyata ta yi ne? Wace irin rayuwa take ciki ne?, dan Allah ka raka Ni, ka raka Ni in ba Auntynmu hakuri, ka raka Ni in fada mata ta yafe min, ka raka Ni in ce mata ta yafe min , ka......"

"ANDADI....."
Muryar Anna ta saka shi dubawa da sauri, su duka ba su suke kallo ba, Ama kuma sun shigo su ukun, wato sam Anna ta ki aunty ta zubar da hawaye a banza

Da sauri ta sake shi, hadi da nufowa inda suke
Chapter 137 · 0% Book details