← Book details Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 141

Sashe 37

Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abdul Fatah ya yi murmushi ya bude bangaren da yake ya furta" Ka sauko man, kar ka sa su fado cikin motar nan dan dokin ganin ka"

Shima yana murmushin ya fito daga motar ya kai dubansa kan jama'ar gidansa

Gaba daya sai ya rasa Barka da saukar wa zai amsa, haka kuma daya bayan daya sai da suka yi hannu da duk wani dake wajen nan , murna fal rai, farin ciki kamar zai kashe suuuuuu

Da wani irin sauri Fu'ad ya ringa buga dakin MAZNA, wace ke kallon tiktok tana tikar dariya abinta, dan a nan ta fi auki, bangaren da zata sha dariya

Mikewa ta yi ta bude masa tana kallon wayar bata dago ba ta ce" Wai meye ne ?"

Har inda inda ce ta kama bakinsa yana nuna waje ya ce" Sir, sir ya zo, ke sir ne ya zo!"

Faduwar gaba ce ta sameta hadi da rawar jiki, ta saki wayar lokaci daya tana ruko ido hadi da dafe kirjinta........ Ta ce" Fu'ad Ni zaka yiwa mugun wasa???"

Fu'ad ya duka ya dauke watsetsiyar wayar da kudinta yayi kudin wani gidan yana dubanta ya ce" Wallahi tallahi shi ne"

Da gudu ta koma ciki jikinta na wani irin rawa , tana kugin kannenta yan matan da suke nasu dakin

Shi ya je da gudu ya tado su, su ma suka nufo nata dakin a rikice jin wanda ya sauka

Wata abaya wace take bin jiki ne ta saka tana fadin" kun yi shara yau? Kun yi mopping yau? Kun kwashe duk wani tarkace? Kun saka turaran wuta kuwa....., oh my god! Ke kun ji wanda ya sauka? Kun san baya son kazanta, baya son.....wayo Allahna na shiga uku.............."

Jauhara ta ruko ido, ta shige dakin nata da sauri tana tayata kwashe kayanta da ta zubar a nan kasa suna yin dayan dakin da tarkacen ta suke suna zubawa sannan ta ce" Yaya zaki yi, da maganar docter......yaya zaki yi? Kin ga dai abinda ya haifar maki????"

A mugun tsorace ta kalleta....., tunawa da ta yi abinda docter ya fada ya sa ta nemi dukewa jikinta na rawa ya fara abin kuka ta ce" kashe Ni zaya yi, ba zai taba hakura ba, sai ya yi....... innalilahi wa Inna ilaihi raj'une"

Karamar cikin su, wato iman itace bata gane abinda suke magana a kai ba, dan haka ta ce" Wai dan yayan ya zo ne kuke ta wanan abin kamar wanda yake dukan mu? Yaya ne fa, Ni da na fito da gudu saboda farin ciki da nuna murnar ganinsa? Yaya ne fa....................."

"Ya'yan kaniyar ki, nace ya'yan kaniyar ki, iman fice min a dakina ba nace idan muna maganar manya kar in ganki a nan ba????"

Baki Imam ta turo ta juya ta fice sumui sumui

JAUHARA ta saka turaran wutar sosai, shi kuwa Fu'ad sosai yake ta kara goge du inda ya dace yana kuma tatare komai, ga falon ba karamin kato bane, ana koro Imam ya bata aikin nan ya nufi dakin na MAZNA da wasu kayan mopping din

JAUHARA ta dubeta da yanayin serius ta ce" Kin ga, tunda kika fara, ki jure ki gama, wallahi kar ki yarda ki lalata jikinki dan idan kika daina amfani kin sani sarai yayinki mijinki zai daina, kin san waye mijinki aunty, gwara ku yi fadan yan kwanaki ya sauko da ku yi na dindindin, shima wanan ai bai dace ba yaya za'a yi ya zo kasa ba sanarwa?, bari Ni in kira docter, ki maida hankali ki je bangaren cen fa, kin ga tunda kika zo baki je ba kuma bamu bari kowa ya shigo nan ba, ki rufawa kanki asiri kar ya gane abinda kike ciki da mahaifiyar sa, kin dai sani sarai baya jira yake tsayar da duk wani neman raini ma a kan mahaifiyarsa bale wannan, gashi fushi yake da ke tun a kan kin je Saudiya bata sani ba, Ni wallahi aunty kin cika cakula al'amuran ki ne, to wai yaya za'a yi a so d'a a ki mamansa? , kina gani fushin da yake yi da ke na baki sanar mata baki da lafiya ba da kuma baki sanar mata kin je wajensa ba, ina ga ya gane tunda kika zo baku haɗu ba?????, hum"

MAZNA sai ta ringa jin numfashinta kamar zai tsaya dan tashin hankali.....,

Da sauri ta amshi katon hijabinta da Fu'ad ya ciro mata ta zumbula ta bude wajen da take jera sababin carbinta ta ciro guda sabo dal ta makala a yatsarta Sannan ta ce" ku tabbatar kun bar falon nan kafin mu shigo, kuma du abinda docter ya fada maki ki tabbatar kin fada min kafin ki kwonta....., ku saka turare sosai ku kuna karatu....bari in je, in sha Allah Ni ce da nasara a kan maman nasa saboda Ni ba abinda na mata!"

Tana gama fada ta juya ta fice tana sake jin wani tsoro a cen kasan zuciyarta.....sai dai abu daya ta sani ba gudu ba ja da baya a lamarin mijinta da ita....., mama kuwa dan ta nuna bata son abinda zai matse musu guri ba laifi ta yi ba , ra'ayinta ne haka dan samun saman lafiya tsakanin ta da danginsa, saboda tunda ta gane cewar abinda ke iya datse igiyar aurenta ba waiwaye ba hakuri Anna ce, sai ta yi nisa da ita dan ba zata taba yarda ta mata laifin da zai shafi aurenta ba!

FARHANA dake waya tana dan zagayen dakinta daga sama ne idannuwanta suka kai balbalin gidan a lokacin da saurayin nata ke tambayarta yanzu fa shi ba zai iya samun ganinta ba bayan gidansu ba kowa yayanta baya nan, shi yana so ya zo yanzu.........

Idannuwanta ne suka sauka a tarin mutanen da suka zagaye wasu bakin motoci.....lokaci daya idannuwanta suka sauka a kan BAWAN ALLAH tsaye yana ta doka murmushi haskensa ya cika wajen , kwarjininsa ya doke na kowa a wajen....., kamar ya kara tsayi ma, kamar ya kara mugun cika ido ma......, suturar da ya saka kuwa sai ta kara masa kima a ido

.. .........hannayen ta dora saman kai tana zarro ido lokaci daya ta furta"..............INDAI KUNSAN KUDIN KUKESON SAMU A ONLINE BUSINESS TO KAWAI KUYI JOINING GROUP DIN NAN 👌🏻😅KUNSAN bani kawo abun banza
💃🏻https://chat.whatsapp.com/L64v3OVQ52pJqtMT51yL2x

22

A firgice ta ce" Na shiga uku, ......"

Sai kawai ta yi gaba da dan gudu Dudu ta nufi dakin Anna

Tana karasawa ta tura kofar ta ga a bude nan ta gane Anna bata ciki, sai kawai ta nufi dakin tsohuwar gidan nan

Ai kuwa da ta je ta bude a hankali ta shiga tana yatsinar baki ta hangota saman gadon ta tuni ta yi barci,

Da sanda ta yi baya dan ba zata so ta farka ta ganta a dakinta ta yi mata wani sharin da zai sa yana zuwa ya kasheta kowa ma ya huta

Da dan gudu gudu ta nufi elevator , dan ba zata so bin matakala ba.........

Tana shiga ta dana kasa kirjinta na bugawa, so take yi ta fara sanarwa Anna wanda idannuwanta ke gani, dan ta tabbata Anna bata san yana hanya ba, da ba abinda zai kaita makaranta yau , kai da wuni zata yi tana zancen zuwansa..............., zata so ganin surprise din da Anna zata nuna jin ya sauka, sannan zata fi so idan sun hade ita da shi ya zamo mamanta a kusa da ita gaskiya.

Yana tsayawa ya bude, tana niyar fita da gudu idannuwanta suka sauka a kan mutane biyar , wato YAYA IMAD, Mutalab, Abdul Fatah da Abdul bassit, sai MAZNA dake cikin katon hijab, ta ja hijab din kusan rabin fuskarta ta rufe da shi................., ya zamo elevator na budewa du suka kai dubansu wajen saboda shigowar su kenan

Bakinta ne ya fara rawa rawa, lokaci daya , ya zamo kafarta daya ta fitar dayar na ciki da sauran jikinta..........

Irin kallon da IMAD yayi mata ya sa ta ji hankalinta gaba daya ya tashi...............

Mutalab ya juyo da nufin tambayarsa shin FARHANA da suka sani a waya ce????, ya zamo su sauran yan uwan sun yi gaggawar dauke dubansu a kanta saboda shigar jikinta wando ne da riga na barci...., kanta ko hula babu gashinta a sake yake........, idannuwansa suka sauka a kan ANNA da ta fito daga kicin dauke da butar shayinta , har zata kwonta ta yi niyar yin nafila sosai, sai kawai ta sauka dan ta hado kayan bukatar ta a kusa..........

"IMAD??" Anna ta fada a tausashe , tsigar jikinta na tashi na farin ciki da dauki da tsantsan kauna.....................

A lokacin da ya ji Muryar Anna, da sauri ya juyo inda take tsaye

Da dan sauri ya nufo ta, zuciyarsa na idasa cikewa da dukan farin cikin da zai iya samu wadatace a nan gidan duniya , ya karaso ya rungume Anna a jikinsa a hankali , ya dora hancinsa saman kanta ya lumshe idannuwansa a tausashe sosai ya furta" ANNA "

A hankali FARHANA ta yi baya tana kifta ido ta dana elevator din ya koma da ita da gudu ta yi dakin ta, domin sai a yanzu ta tuna kallon da ta samu abinda yake nufi, shi ne sutura rufafiya.........dan kuwa du abinsa baya taɓa yi mata irin kallon nan idan bata yi komai ba.

Idannuwan anna a lumshe suke, NUTSUWA na ratsa zuciyarta, hankalinta na ƙara kwonciya......, a zuciyarta kuwa kamar ta yi ta takun farin ciki wanda zata ji kunya ita da kanta bayan ta gama......
Chapter 37 · 0% Book details