← Book details Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 141

Sashe 59

Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga haka Anna ta shigewarta tana sake jin NUTSUWA na shigar ta da tarin tunanin irin zaman da zasu yi da FARHANA........

Lokuta da yawa tana godewa Allah da ya bata mafita mai girma irin IMAD a duniya.........

Shi fa ba dukan farhana yake yi ba, ba zagi ba, ba wani wulakantata yake yi ya sa take mugun gudun bacin ransa ba..... a'a
A lokacin da shi din da kansa bai wuce a kula da shi bane ya kula da ita........
Ya zamo irin yayun nan dake hakura da alewa su ba kannensu suna kallon su da murmushi har su tsotse ta......
Ya zamo irin yayun nan dake nan a koda yaushe Ama kuma basa nan a koda yaushe, domin ko kadan bai zama mai janya fa kokowa, ko fada, ko wani abu ya haɗa su rigima ba, tun abin yarinta na nuna mata garaje irin na ta nemi yin ja in ja da shi har zuciyarta ta amince mata cewar ba zasu taba yin ja in ja ba sai dai ta bari dan girmamawa ko kuma ta bari dan cencentar abin ba kanta ya dace ba........
Irin shakuwar dake tsakanin su ya sa ko da yake nesa idan ya ji wani abin sai dai ta waya su yi maganar da bata daukan lokaci, kawai dan ya fahimceta ne ta fahimce shi, harma ya fadi abinda yake so a yi, kuma ta yi ba tare da ta kiya ba, domin gudun bacin ran zuciyarsa wanda take dauka da mahimmanci sosai............
Ta zabi makarantar da take so , ya biya, ta zabi suturar da take so, ya biya, ta zabi abinda zata ci, ya biya, ta zabi son kwonciya cikin sanyi ya saka........a hankali ya ringa daukan gurbi na mahaifi har ya zamo ta gama zubar da du wata hanya dake iya zama wata rana su samu matsala ita da shi na raini a duniya............
Sai kuma da ta je inda yake rayuwa ta ga irin rayuwar da yake yi da jama'ar dake zagaye da shi, sai ta kara daukan kiyayarsa mai girman gaske ta saka a zuciyarta, har ya zamo idan ta yi abinda take tunanin laifi ne a wajensa jikinta ke bari, tsoro ke mugun kamata wani lokacin har ma ta yi kuka dan ta kiyaye fushin sa, wanda haka ne ke matukar kara sakawa Anna NUTSUWA, dan kuwa idan da bata samu haka na, a yanzu da bata san inda FARHANA ta taka a duniyar rashin ji da neman fitina ba............

Alwalarta ta dauro ta dawo ta haye darduma dan ta yi Sallah sannan ta ajiye karamar wwayarta da Contact din iyayen yara ke ciki, masu yawan gaske kusa da dardumar da nufin idan ta gama sallah zata yi kiran Numbar Aban yara wace ta yi svng da Malan Ahmadun HALLAH, dan ta nemi alfarmar idan har ba damuwa a bata wata yar dama daga Hallah din har yar uwarta ta basu wata yar kula........, wace bata wuce misali ba, dan shakuwar dake tsakaninta da Hallah, wace take matukar mamakin irin yadda take girmama zumuncinta da ita..............., kwarai har take jin yarinyar a cen cikin zuciyarta..... Dan Allah ya bata dama koda ba yau ba ........ta kula da wasu abubuwa a lamarin yarinyar............ciki harda sake fito da ita a fuska madaukakiya cikin kiyaye adininta.....ta hanyar saka ta a gurbin da ya dace da ita a duniyar tsafta da iya kwalliya....dan haka kawai take hango Hallah a gaba ta macen da ta iya wanka, take da muguwar tsafta.........

Murmushi ta yi a ranta ta ayyana ' zata fi fito da darajar da daidaikun mata suke da shi, wato darajar da ta nuna min tana da ita a yau..........ta yiwu ta zamo shigiwar wanda bai zata ba a lokacin da bai zata ba......hum'..................da haka ta shiga yin sallar ta a nutse bayan ta ture komai daga ranta................................

HALLAH

Kisan mummuke 1k ne sajida Nijar 93811618KISAN MUMMUKE 35

Bayan Anna ta gama sallah wayar Aban yara ta turawa kira

Abinka da waya irin tamu jira muke yi ta yi ringin, Ana ya dana wajen dagawa ya kara a kunnensa da yin doguwar Salama

Anna ta amsa da mutuntawa kafin ta gabatar da kanta

Aban yara ya amsa shi din ma, dan haka Anna ta ce" Aban Hallah, dama kira na yi dan na roki alfarma, idan har hakan ba zai sa in shiga wani hurumi ko in take wata doka taka da ahalinka ba, zan so a baki dama a kan yaran nan....., dan Allah a bani dama koda gobe ne in sha Allah in kula da harkar kan HALLAH, harda yar uwarta.....idan har an bani dama zan kai ta ne da kaina saloon in an gama in dawo da ita gida....., Ama fa in har hakan bai zama wata hanya da ba zaka so ba, bisa gaskiya da amana nake rokon wannan dama a gare ka"

Shiru ya fara wanzuwa a wayar, kafin Aba cikin yanayin mamaki ya ce" Wai Nur dai ta gidan nan Hajiya?"

Anna ta tabbatar masa

Aba ya sake yin shiru na dan lokaci...
........, har ga Allah ba kiyawa yake da niyar yi ba, ba kuma rashin yarda ta saka shi haka ba, kai shi fa du irin zagin da ake yiwa mutanen nan abinda ma ya hana shi tashi bai taba ji a jikinsa yana jin tsoro ko fargaba idan wani abin ya hado su da su ba, na haduwar masallaci ko na haduwar anguwa idan motarsu zata wuce, shi yasa du abinda ake fada yake sauraro sai ya dora da fadin ya dogara da Allah in sha Allah ba abinda zai same shi

Abinda yake tsoro daya ne jal, irin yadda duniya ta zama abin a kiyaye, idan har baka yi taka tsantsan ba zaka samu abinda ya fi karfinka a lokacin da baka shiryawa hakan ba

Shi dai ya gane cewar kwarai haduwar jini ke yawo tsakanin yarinyarsa da matar nan, haka kuma da ya je har inda take ya kara yarda cewar haduwar jinin ce kawai, Bama kamar yadda yake ganin ci gaba a wajen yarinyarsa wace ba irin abinda basu yi ba a da dan su samu irin ci gaban nan Ama ya gagara......., a yanzu fa ana fara kiran sallah Hallah ke fara mikewa, da ya tambayeta ta sanar masa Anna ce ta ce an halicci bawa dan ya bautawa Ubangiji ne kawai, ba zuwa yayi duniya dan ya ji dadin rayuwa kawai ba......, sallah kuwa na daya daga cikin baban ababen da Allah zai duba gobe kiyama, idan sallar bawa ta yi kyau, ana masa kyakkyawan zato....idan kuwa ya zamo mai wasa da sallah ne tun a duniya Allah zai nunawa duniya shi kafin ya je ya girbi abinda ya shuka.....wato shi dai a lokacin murmushi yayi kwarai ya ji dadi har ransa, cike da mamakin wai saboda kalaman nan ne ta yarda, harma yake tunanin to da wani yare ne ba'a fada mata hakan ba a gidan nan?, tabbacin cewa Anna ta san hanyar da zata bi dan Hallah ta saurareta har ma ta yi mata biyayya.....to kuwa ai abin alkairi ne haka sosai.

Shirun da ya wanzu ne ya sa Anna fadin" Aban HALLAH idan har da wata damuwa a bar shi fa, Ama a tabbatar da an kula min da tsaftar kan yarinyana da duk wani abinda ya dace ........, zan so in samu Numbar mahaifiyarta saboda irin haka.........."

Da sauri aba ya ce" Ai ba komai Hajiya, Nur taki ce ai, dama ina tsoron kar in dora maki wani nauyi ne, da sai in ce Zan kora ta gidan mai wankin kai idan ta zo......matsalar yarinyar taki ce bata son taba kai ko da wasa......har yanzu bata daina kukan kitso ba, idan kika ji ana dauki ba dadi da ita a gidan nan saboda maganar kunce kai da wankinsa da kitsa shi ne........., Maman yara kuwa bata da waya ai, Ama in sha Allah zan sanar mata na tabbata farin cikin hakan zata yi, bale da yake da yar uwarta ne ma"

Anna ta yi murmushi ta ce" Masha Allah, eh da ita ne, ba wani dora nauyi ai, Allah ya saka da alkhairi"

Aban yara ya yi godiya shima kafin ya kashe kiran......

Shiru yayi yana nazari na dan lokaci kafin ya dubi auntyn yara dake zaune a tausashe ya ce" Babar malamar islamiyar su Nur ce"

Auntyn yara ta Dube shi da kula ta ce" Allah sarki, kar dai wani abu ta aikata????"

Malan ya girgiza kai ya ce" Ko daya, ta yi kira ne dan ta nemi alfarmar zata kai yaran nan gyaran kai..........., shin ke me kike gani?"

Auntyn yara ta Dube shi, sosai take son cewa a'a, idan sun dawo itama tana da niyar yi musu da kanta....., sai dai bata fadi haka ba saboda a gabanta yayi wayar nan, ya gama yanke hukunci, idan ma tana da wani abin fada ba yanzu zata fada ba gaskiya

Da kuma, da girmamawa ta ce" Malan, idan har ka ga ba wata damuwa ai ba abinda zan ce sai Allah ya tsare"

Malan yayi dan shiru na dan lokaci kafin ya ce" A gaskiya mace ce mai addini, mace ce mai kare mutuncin ta, Ni dai a zama uku da na taba yi da ita a kan maganar yaran nan na gane mace ce mai saka iyayen yara a halin nutsuwar zuciya.....ba Ni kadai ke fadar haka ba, du wani wanda ya'yansa ke cen in dai zaki yi magana da shi zai yaba maki kamalarta da mutunta jama'arta........"

Ya dan yi shiru kafin ya ɗora da fadin" Kwarai Allah ya saka shakuwa tsakanin ta da yaran nan, Bama kamar NUR........, wanda na dauki hakan matsayin shakuwa ce kawai da Allah ke iya haɗawa tsakanin bayinsa koda kuwa basu hada komai na jini na, ko kuma yanayin arzikin su bai zamo daya ba................"
Chapter 59 · 0% Book details