← Book details Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 141

Sashe 3

Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bismillah, ya Allah ka siyar mana, ka dafa mana

*JAMA'A NAZOMUKU DAWANI TSARI NASAMUN KUDI TA HANYAR AMFANI DA WAYAN HANNUNKU
WANNAN TSARIN SHINE METAFORCE

MENENE KASUWANCIN METAFORCE* ????

*Metaforce kasuwancine ingantacce halattacce Wanda yake biya 100 💯 Wanda ake Gudanar dashi da wayar hannu,METAFORCE is also a part of network marketing,is a 100 percent decentralized project da aka daurasa Akan Blockchain technology Wanda babu wani mahalukin daya Isa YAYI editing,hacking ko deleting wani abu acikin sa,Kuma yanada matakai yanada rassa Wanda kowane reshi ka rike a METAFORCE to ka samu GUDUMAR DUKAN TALAUCI*🌎

METAFORCE ANASAMUN KUDI ACIKINSHI SOSAI MATUKAR ZAKAYI ABUNDA AKEBUKATA

zaku iyahada miliyoyin kudi aranadaya acikin wannan kasuwanci me albarka in sha Allah

Duk wacce tashirya zata iya tuntubanmu akan wannan number
09136899615
Hajja Data

*2*

Zurbat ta mike hadi da bude idannuwanta lokaci daya tana fitar da ihun jin zafin dukan tana sauke dubanta a kan wace ta dake tan domin dukan ya shige ta gaskiya......

Gaske, ta ji abu mai gigitar da zuciya, gaske ta ji ana neman tarwatsa kwonciyar hankalin ta, to idan ba mahaifiyarta ba anya akoy mai farmakin nutsuwarta a duniyar nan? Babu wanda ya kai mahaifiyarta tsanarta a kaf duniyar nan.

A gigice ta fashe da kuka tana sosa wajen hadi da mikewa tsaye tana neme neme dan gane laifin da ta yi.

Maman yara da ta yi mutuwar zaune ce ta mike har kamar zata kifa ta shigo da sauri tana fadin" Subahanalahi, ke ramatu, me nake gani haka? Me yarinyar nan ta maki tana kwoncinta tana barci ki ratso har nan ki daketa? Wai dan Allah me yasa kika tsani yarinyar nan kamar ba da cikinki kika haifeta ba? Kin uzura mata kin Hanna mata kwonciyar hankali, kin takurata Ko hanya ta haɗa ku sai kin ci zalinta? Kin ga ki bari, kar ki yarda ki kuma dukanta tunda ba abinda ta maki!"

Ran Mama karama ya bace sosai, ta fuskanci Maman yara, a tausashe ta ce" Maman yara, ki yi hakuri, ama kalmar tsanar da kike fada ta yi tsauri sosai harma tana bani mamaki fiye da tunaninki......, "

Ta ɗan saurara ta sake dubanta ta ce" Anya kuwa rai zai ci gaba da daukar wasu shaguden ? To ai maman yara bana tunanin gangar jiki zai tsani tsanin Ran da ya ratsa jiki ya fito duk tsanani kuwa......, sai dai idan wata sharar ke kama da farmakin nutsuwar yan gwongwon ne zaki ga sun mamaya, Ama duk rintsi sai dai rai ya bace a zartar da hukunci a kuma yi hakuri......"

Ta dubi imtee dake ta shashekar kuka, duba irin na cikin ido, duban da zata iya rantsewa bata taɓa ganin mahaifiyarta ta yi mata shi ba

A kausashe sosai ta ce" du Wanda zai yi maka fada dan ka gyara kayanka ba makiyin ka bane, shekara goma sha takwas kin yi tsufan da ya dace ace zuwa yanzu zaki iya gane mece rayuwa...., !"

Ta dago yar yatsarta ta nuna mata a kausashe ta ce" Bana tunanin zan iya gani in kyale a duk abinda yake ci gaba da wanzuwa a kan ki, wanda ya shafe ki, idan baki je islamiyya ba me zaki anfana da shi gobe kiyama? Ki je ki koyi ilimi, ta yiwu ki gane abinda kike ciki!, ki je ki dauko ilimi, shine kadai abinda na umarceki da shi, idan har kika kiya NUR a nan ne zaki ga kalata, na baki minti biyu ki saka hijabinki ki bi yar uwar ki ku wuce makaranta!"

Daga haka ta juya ta fice daga dakin

Sai dai tana fitowa maman yara na biye da ita rai bace ta ce" Ke ramatu dakata, dakata ki gaya min abinda kike nufi!"

Dakatawar Mama karama ta yi tana juyowa, a lokacin da Sulaiman ya shigo dauke da buhun shinkafa a kafadarsa ya karaso kofar dakin ya sauke sannan ya ja ya tsaya yana kalon su dan tsayuwar tasu ta masa kama da wa'inda ke fada

A tausashe Mama karama ta ce" Maman yara, dan Allah ki yi hakuri, wallahi ban yi mata haka dan in bata maki rai ba, Ama rashin mutuncin Nur yayi yawa ne, Maman yara dan ta ga Bakya son bacin ranta ne har take irin wannan sangartar dake iya kaita ga halaka, ki duba ki gani, shekarunta da ajin da take a boko, ga na islamiyyar bata da wani abin a zo a gani, to shi karatu lokaci baya taba kurewa dan yinsa in dai da rai da lafiya, Ni kuwa in sha Allah Ni da ita za'a ga wanda ya gaza ki barni da ita!"

Fitowar yan matan da jakar karatunsu yayi daidai da shigowar mahaifinsu shi kuwa dauke da kayan miya masu dan yawa, dama kasuwa suka je shi da Sulaimana suka yo sarin kayan saidawar da yake zubawa a kantinsa, shine ya musu cefane na kirki dan a kara dan lasawa yau ma, dama yawanci idan ya samu kudi mai dan auki haka suke yi, wani lokacin har kashin miya ake samu a watsa a girkin, ko a yi dambu ya sha hadi a ci har a mikawa makota, yau din ma cefanen ne harda naman miyar, ya shigo da Salama

Har ga Allah sai da gaban Mama karama ya fadi, nan da nan ta so daburcewa, bale da ta ga irin kallon da ya bita da shi sai da hankalinta ya tashi lokaci guda, uwa uba irin yadda maman yara ta shiga share hawaye ta kunto yan cenji a habar zaninta ta mikawa Imtee ta ce" Ki amsa, idan kun je kin ji ciwon zai kayar da ke ki sayi panadol ko ciwo takwas ki sha, Allah ya gani ina kaunar ki da zuciya daya, sai dai tabas mahaifiyarki tana da gaskiya, ta fi Ni iko da ke a gidan nan, ku je Allah ya tsare"

Amsa suka yi suka wuce, Sulaiman ya tabe baki ya juya ya shige dakin mahaifiyarsa saboda yana son daukan abu a ciki, ko kuwa haka kawai ne baya so a yi maganar a gabansa? Ya san kuwa inda mahaifinsa ya tsaya a nan zai fara maganar nan.

Rai bace ya ce" To, menene? Menene? Safiya ta yi gwana zaki daga min hankalin ko?, wani irin kin fita iko da yarinyar nan? Ke ko kara baki iya ba? Hala zaginta kika yi a kan yarinyar nan? Nuna mata iyakarta kika yi ko?"

Mama karama ta girgiza kai, bayan ta gama mamakin maman yara kamar yadda ta saba ta ce" Yaya zan iya budar bakina in zageta? Ta yaya zan iya zaginta?"

Maman yara ta fashe da kuka tana kaiwa zaune hadi da duban baba ta ce" Da wani abin ai gwara zagin, daga cewa yara su fito su je islamiyya na nuna mata imtee bata da lafiya a barta ta sha magani Shikenan matar nan ta shiga hawa tana sauka da tarin bakaken maganganun da kunnenka ba zasu so ji ba?, a yau harda min gorin ba Ni na haifi imtee ba, harda nuna min sunan da nake kiranta da shi baida wani tasiri ta hanyar kiran imtee da Nur?, tabas kina da gaskiya, sai dai ki sani Allahn da ya baki nima ya bani, kuma d'a daya gari ne in da rai da lafiya, idan imtee ta dawo ta kwaso kayanta ta koma dakin ku, Allah ya rayata, in dai zan ringa ganin wulgawarta ai Shikenan hankalina ba zai tashi ba, Ama ki sani masoyi ba makiyi bane"

Daga haka ta nufi dakinta tana sake daga muryarta wajen yin kukanta.

Gaba daya mama karama sai ta gaza koda motsa yar yatsarta ne
Bale da mai gidan nata ya budi baki ya ringa masifa tamkar zai ari baki, ya tabbatar mata duk ranar da ta yarda imtee ta dauko kayanta da zumar komawa dakinta sai dai ta bar gidan dan ba zata fito masa da fitina a cikin gidansa ta barshi da wahala ba, ya kuma sheda mata yana iya sake kayar da rago ya sakewa imtee sunna daga sunanta na gaskiya wanda aka rada mata zuwa imtee kuma ya ga ubanda ya isa ya hana shi, yaran nan dai ya'yansa ne, bai ga wanda ya isa ya shiga tsakaninsu da uwar gidansa ba, dan haka a kiyaye shi wallahi a kan haka yana iya Salamar mace, in ba ma rashin tsoron Allah ba da ta samu ya'yan biyu ita ta ba kanta ne? Aikin banza aikin wofi kawai.....

Ya karashe yana juyawa bayan ya watso mata cefanen ya fice a gidan dan dama ya barawa kaninsa kantin ne du hankalinsa na cen, dan kuwa ya sha bara masa ya dawo ya tarar da muguwar barna.

Jiri ke dibanta, a hankali bayan ta kwashe cefanen ta nufi dakin nata tana dafa bango

Fitowa yayi kansa a kasa ya ratse ta ya nufi kofa

Ba tare da ta bishi da kalo ba ta samu ta shige dakin da kyar sannan ta duke tana dafe kirjinta dake mugun bugawa.

Bata ji shigowa ba, sai hannunsa da ta ji a saman nata yana kalonta fuskarsa da alamun tarin damuwa

A hankali ta furta" Sule....."

Kansa ya dukar a hade ya ce" Baki da lafiya ne?"

A hankali ta girgiza kai, ta zauna da kyau cike da mamakin ganin wannan lamari, Duda halin da take ciki kuwa, domin ba abinda bai faru ba a gabansa Ama bai taba nuna ya gani Bama bale har ya dubeta

A hankali ta ce" Lafiyana kalau"
Chapter 3 · 0% Book details