← Book details Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 141

Sashe 52

Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Metaforce kasuwancine ingantacce halattacce Wanda yake biya 100 💯 Wanda ake Gudanar dashi da wayar hannu,METAFORCE is also a part of network marketing,is a 100 percent decentralized project da aka daurasa Akan Blockchain technology Wanda babu wani mahalukin daya Isa YAYI editing,hacking ko deleting wani abu acikin sa,Kuma yanada matakai yanada rassa Wanda kowane reshi ka rike a METAFORCE to ka samu GUDUMAR DUKAN TALAUCI*🌎

METAFORCE ANASAMUN KUDI ACIKINSHI SOSAI MATUKAR ZAKAYI ABUNDA AKEBUKATA

zaku iyahada miliyoyin kudi aranadaya acikin wannan kasuwanci me albarka in sha Allah

Duk wacce tashirya zata iya tuntubanmu akan wannan number
09136899615
Hajja Data

*JAMA'A NAZOMUKU DAWANI TSARI NASAMUN KUDI TA HANYAR AMFANI DA WAYAN HANNUNKU
WANNAN TSARIN SHINE METAFORCE

MENENE KASUWANCIN METAFORCE* ????

*Metaforce kasuwancine ingantacce halattacce Wanda yake biya 100 💯 Wanda ake Gudanar dashi da wayar hannu,METAFORCE is also a part of network marketing,is a 100 percent decentralized project da aka daurasa Akan Blockchain technology Wanda babu wani mahalukin daya Isa YAYI editing,hacking ko deleting wani abu acikin sa,Kuma yanada matakai yanada rassa Wanda kowane reshi ka rike a METAFORCE to ka samu GUDUMAR DUKAN TALAUCI*🌎

METAFORCE ANASAMUN KUDI ACIKINSHI SOSAI MATUKAR ZAKAYI ABUNDA AKEBUKATA

zaku iyahada miliyoyin kudi aranadaya acikin wannan kasuwanci me albarka in sha Allah

Duk wacce tashirya zata iya tuntubanmu akan wannan number
09136899615
Hajja Data

31

Da mamaki Malan ya ce" Kamar ta titin kurame nake gani a gidan namu???"

Maman yara ta rintse kdannuwa tana aro duk wata jarumtarta ta ce" Malan, yanzu har sun tarda kai munafukan nan???"

Malan ya Dube ta da mamaki ya ce" Wasu munafukai ne suka tarar da Ni ??"

Maman yara ta kalli aminiyarta da sauri, itama ta kalleta tana gyatsina ta ce" Malan , kana nufin tsabar kurata ta yi kuka har idan na zo wucewa kar na biyo ta gidan nan mu gaisa da aminiyar yarinta?, zumunci ne ka gama kashewa Malan??"

Malan yayi yar dariya yana girgiza kai ya ce" A'a a'a, Ni ban hana wannan ba, abinda na hana zuwa da zowar ba dalili ya zamo kullum kuna hanyar juna a'a, haka kuma na soke zuwa da wuni, zumunci daga nesa ba laifi ba, sannan na soke zumuncin waya, idan an jima ba'a ga juna ba a hadu a gaisa ba laifi ba,....bari in shige ciki ki yi gaggawar juyowa bana son doguwar rakiya, Allah ya bada ladan zumunci"

Daga haka yayi ciki, ya barsu suka bi shi da ido kamar idannuwan nasu zasu fito daga jikinsu

Wata irin ajiyar zuciya maman yara ta sauke tana dafe kirji, wace ta sa Mama ta titin kurame zuba mata ido da mamakin ta ce" Hum, lalle maman A'isha, kina bani mamaki idan kina fada da fadin cewa Malan baya gabanki, a kullum kalaman bakin ki ba wani abu da ya shafi Malan da ya rage a zuciyarki, bayan abu ƙalilan ke iya faruwa yannayinki ya nuna har yanzu mijinki na nan a zuciyarki......., wallahi ko me zaki yi ki kiyaye saboda malami kike aure, kin ga idan kika yi abinda zaki shiga uku ko? A kankanin lokaci Allah zai bayyana ki, kuma ke kuwa ba zaki iya rayuwa in ba mijinki ba, mu je ki taka min ni in samu abin hawa in tafiyata !"

Binta Maman yara ta yi ba tare da ta iya ce mata ufan ba, saboda ita bata san Bama abinda zata fada mata ta gane yaren ta......wai kaunar Malan, Allah sarki hum

Malan na shiga gida ya samu auntyn yara na kwashe tuwo

Da sauri itama ta mike gabanta na faduwa da tsoron kar dai aje tarda shi mutanen nan suka yi wajen neman na abinci????

Da sauri Malan ya ce" Dan cika min butar nan auntyn yara, cikina sai juyawa yake a fujajan na nufo gida....kawai yanzu ba damar in taba abu mai yaji sai cikina yace bai gane ba, dan cika min"

Da gagawa auntyn yara ta nufi wajen rijiya bayan ta suri butar da mamakin yaya aka yi ma butar bata cike? Ta je ta zura gugar nan ta cika masa ta miko masa kafin ta nufi dakin ta a ranta tana ayyana ' innalilahi, wallahi na zata mutanen nan sun same shi ne sun masa rashin hankali, hummmmm, ko Ni ba zan so IMTEE ta auri danki ba saboda idan har ta aure shi a irin kiyayar nan da mahaifiyarshi ke yi mata ba zata taba rayuwa cikin farin ciki ba, sai tashin hankali da wulakanci........ita din da kanta Imteen ba zata taba girmamata ba, saboda irin yadda ta zo har gidan su ta zubar da mutuncinta, wallahi idan ma ta hadu da mutanen banza zasu iya koya mata muzguna mata, bale idan har mijinta yana sonta to kuwa sai mahaifiyarsa ta yi kukan jini, Ama kuma ba zata yiwa lamarin Allah shishigi ba, ko me ya faru zata fara saka addu'a a gaba, ta ba Allah zabi, ta tabbata zabin na Allah ya fi na kowa , kuma idan har ya riga ya ƙaddara Imtee fa matar Anas ce babu yadda aka isa a yi, zai mayar da kowa a cikin hankalinsa ne ya shiryar da ita kafin ma a yi, saboda ita zata dage ne ta barawa Allah zabi, ta tabbata kuwa da wahala Allah ya bari IMTEE ta shiga gidan nan a haka din nan da uwar mijin ke yi mata muguwar tsanar nan, in sha Allah zai saka shakuwa a tsakani

A hankali ta saki labule ta dube su kasa kasa ta ce" Mahaifinku ne ya shigo, ku kama bakinku dan ba zan so ya ji abin nan ta haka ba...., Ni na san yadda zan masa bayani ya fahimta a tsanake....., abinda nake so da ku ba raini ba wulakanci tsakanin ku da matar nan, in me ya faru tsakanin mu da ita tsakanin mu da ita ne, kar ku saki ku shiga, haka kuma kar ku saki haka ya sa ku yiwa y'arta wani abu na rashin dadi ko shi din da kansa ............, du abinda zai hada ku da shi ya zamo na zumunci na mutunta juna ne kun fahimta?"

IMTEE da mamaki tana kallon aunty ta ce" Aunty, mu musu magana? Aunty du irin yadda suka zo suka zagar mana ku? Duba ki ga abinda mahaifiyarsa ke fada sai kace Ni ce na je nace ina son d'anta???"

Aunty ta zauna tana murmushi a tausashe ta ce" Eh na gani, na kuma gane bata son lamarin, ama ina so mu fara yin taka tsantsan ta hanyar fadawa Allah......, idan har alkairi ne zaki ga ta yi nadama da kanta, in kuwa ya zamo kun dauki zafi kun yiwa manya rashin kunya, kun yi fada da ƴaƴanta ina anfanin haka? tarbiyyar da muke son ganin ku a kai ta haɗa duk wata daraja da alkhairi, ciki harda kawar da kai a yiwa manya takakiya.....kun ji????"

Malan ne ya nufo dakin yana dan gyaran murya

Auntyn yara ta mike da sauri ta fita tana murmushi ta ce" Aban yara yaya jikin?"

Dariya yayi ya zauna yana karbar ruwan da ta miko masa ya kafa kai ya sha ya ce" Alhamdulilah, ina ya'yan naki ne? Ko aiki suke yi a daka"

Auntyn yara zata yi magana Maman yara ta shigo

Ciki ciki ta yi Salama kafin ta nufi dakin ta

Mikewa Malam yayi ya bi bayanta

Tana shiga yana shigowa shima, ya zauna yana dubanta ya ce" Ina kan bakana da kiyaye duk wata hulda dake iya hadaki da matar nan, ki kula, kar ki yarda in kama wata huldar da ta wuce a gaisa ke da ita, halayarta ya sa na saka shinge a tsakanin ki da ita, saboda ba zan so ko da wasa ta halaka maki tarbiyyar ki da tsoron Allahn ki ba, abinda ya fito fili du aka gani aka kai ma ji tsakaninta da mijinta da abokiyar zamanta wanda har yau har gobe take takama da isa da nuna ta yi kuma ko gobe ta kama zata kuma yi ba alkhairi bane a wajenta a nan duniya da kiyama......., Ni ba zan taba zuba ido ki dauki wasu daga cikin halayarta na cutarwa baiwar Allahn nan ba, abokiyar zama lokaci ne, idan yayi aka yiwa mutun ya dauka ta fuskar da ta fi dacewa....kwarai na yaba yadda kika yi hakuri kika jure, na yaba yadda kika runguma kika kawar da kai, ba yaba yadda kika rike NUR......, Ama kuma ba zan taba yarda a shigo da wani abin ba.....kin fahimta????"

Maman yara dake kallonsa kawai gani take kamar wani bakin halitta ne shi din a gaban ta, kalaman sa kuwa tafe suke da harshe biyu a kunnayenta...........

Dauke ido ta yi bata ce komai ba, shi kuwa ya tabe baki ya fito ya yi ficewarsa dakin soro, hakan ya sa auntyn yara bin bayansa saboda ta haɗa masa maganin Hausa ne dan ya sha ta ga yannayin ciwon cikin...

Bayan fitar auntyn yara A'ISHA kasa kasa sosai ta ce" Baki yi mamaki ba?, baki yi mamakin wannan lamarin ba???"

IMTEE dake kallon kasa tana ta tunani ta kalli A'isha

A'isha ta yi murmushi a hankali sosai ta ce" idan aka samu dan sabanin da muna kallo auntynmu bata taɓa bude bakinta da karfi ta yi magana da yanayin daga hankali ba, Ama me Mama ke fada mana? Du girman mutun idan ya mana mu masa, ko waye koda mahaifinmu yace zai shiga sabgar mu , mu dakatar da shi!, "

Da sauri IMTEE ta mike ta cire hijabinta a hankali ta ce" A'isha, dan Allah ki daina min haka, ki daina taba min zuciya da kokarin rushe duk wani yinkuri nawa da abinda na ginu a kai, A'isha mama ce fa, ki dauka kawai mama nada zafin rai ne......hakan ya sa bata cika son a shiga lamarin mu ba, dan Allah A'isha ki rufa min asiri ki daina hargitse min tunani mana"
Chapter 52 · 0% Book details