Sashe 106
Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Babu abinda kika sani......., zaki iya daina cewa kin san pain din da nake ciki?, ban kai shekaru da zan iya awa goma ban ji bukatar mace a jikina, da lafiyata, da kwakwaluwata ba..........., ke da kanki zaki iya tuna lokacin da na dauka ban samu abinda nake tunanin na fi karfi ba, ama kuma yake barazanar fin karfina?"
Zuciyarta na bugawa ta ce" Akul, bai fi karfinka ba, kuma na san kana hakuri, shi yasa nake ta rokon ka kara hakuri ka bani dama in yi maka abinda zai sa ka ji sauki sosai a jikin ka, ka ga idan na yi anfani da bakina zaka cire cutar dake damunka a dan kankanin lokaci ba tare da ka sha wata wahala Bama, ba tare da ka motsa Bama"
Kai ya girgiza yana lumshe idannuwansa, ya dan dauki lokaci kafin ya ce" MAZNA........, ni ba robot bane, abinda kike son bani kuma ba abincina bane, motsawar da kike tunanin wahala ce ke kin san in kwana ina yinta bata gajiyar da Ni, ina sport, ina fa shekarun da zuciyata da jikina ba zasu taba gajiya dan kawai ina yin wannan abin ba.........."
Yayi shiru kafin ya bude idannuwansa ya sake yi mata duban dake tsoratar da ita
A nutse ya ce" Saboda saken ki.......ina jin ina ma in samu wani jikin da ba naki ba"
Kirjinta yayi wata irin bugawar da har cikinta ya kwashi dumi
A hankali ya dora da fadin" Ina ji a jikina idan har ba gamsashiyar amsa na gani da kaina a gaban likitan da na yarda da shi da kaina ba......, ba zan iya ci gaba da maki uzurin ciwo ba"
Ta kara dubansa a wani tsoracen , kirjinta yana sama yana kasa
A tausashe ya furta" Idan kin yi niyar in san me yake damun ki, nan da kwana biyu, just 2 Dys......ki bani damar da zata hana ni auren mata har uku........, shi ne kawai hakurin da zan sake iya maki, idan ba haka ba, MAZNA zan yi aure ..................domin a ciwon da kuka hada min mace daya ba lalle ta iya kamawa ba!"
Daga haka ya mayar da idannuwansa ya lumshe a saman lebensa ya furta" ki je"
Da ace ya sake bude idannuwansa da sai hankalinsa ya tashi irin yadda jikinta ke rawa kamar mazari
Kirjinta kuwa banda sama da kasa babu abinda yake yi kamar zai balo ya fito ne daga bakinta
Ta dauki minti biyar tana jiran ta ji ko ta ga ya janyota jikinsa, ama hakan ya gagara, domin ya riga ya gama magana kuma ta tabbata idan ta matsa masa a nan ne ranta zai bace
A dole ta mayar da rigarta jikinta du a mace, hankalinta a tashe ta juya tana tafiya tana waigo shi tana kalonsa har ta fice a dakin ta rufe sannan ta nufi nata dakin zuciyarta na yi mata bugun kalangun kauye.
Tana fita daga dakin ya juye saman cikinsa hankalinsa ba a jikinsa ba ya damki marar tasa yana ta adu'o'in da suke zuwar masa bakinsa dan samun Salama......., sai dai cikin ikon Allah nan da nan zazabi ya rufe shi mai zafi ga dukan da zuciyarsa ke masa, ga irin yadda yake ji a jikinsa shi kadai ne zai iya kwatantawa bawa halin da yake ciki sai ko ubangijinsa da ya halicce shi ya san karfin jarabawar da yake ciki kusan shekara kenan.
MAZNA da ta koma ɗakinta ta samu Jauhara na waya da wani saurayinta, wayar fada ne suke yi saboda kwanaki nawa yana neman damar zuwa inda take aman ta nuna masa ita fa a'a gaskiya ya bari tana da wani abu a gabanta har ta gama, wani abin kuwa ba komai bane face kwawar da ta dage kan sai ta samu shiga duniyar Mutalab , wanda bata san abinda ake ciki ba da ta rungumi mai son ta hannu bibbiyu
Cike da gajiyawa da halin yayarta ta dubeta ta kashe wayar ko Salama bata yi masa ba ta ce" Yau ma kukan kike yi saboda yaya? Wai ba zaki yiwa kanki fada ki gane rayuwa ba ki yi hakuri ki fuskanci mijinki yadda ya dace ba? Wallahi a zamanin nan yara ke kamuwa da hawan jini, AUNTY idan kika lalace fa kanki kika fara sakawa a wani hali kafin kowa, Tom"
Rai bace Mazna ta ce" Jauhara Ni kike fadawa maganganun nan? Ni kike zagi dan kawai kin gani a wani hali? Kika san me aka yi ne da zaki ringa zagina ba tare da sanin ba'asi ba?"
Jauhara ta ce" Ba zaginki nake yi ba AUNTY, gani nake yi sam Bakya son magance damuwarki, da kina son magance ta da yanzu wani maganar ake yi ba wannan ba, kin kasa ba mahaifiyarsa daraja yadda ya dace, ke kullum kina nunawa mahaifiyarsa bata da wani daraja a gabanki, yaya kike so wai ya mutunta ki?"
MAZNA ta tareta ta ce" Jauhara dan Allah ki saurara min haka, kar ki saki ki daga min hankali a kan abinda Bama shi bane, waye yace maki kan Anna yake son daga min hankali, Ni na zata idan na je zai sake daure min fuska a kan laifin da banma san ko menene ba, Ama sai ya sake bilo min da wani batun da ya fitini rayuwata, gaba daya a bukace yake da Ni , Ni kuma ba zan iya ba a yanzu, shi ne na yi na yi da shi ya bani dama in bashi nutsuwar ta hanyar da ya dace ya nuna a'a ba zai yiwu ba karshe yace ya bani kwana biyu idan ban bashi hadin kai ba ya rantse min sai yayi aure, kuma kar na ji a wai sai ya sako mata sama da daya dan daya bata isa ta bashi abinda yake nema ba!, ya saurareni ma ya gagara sai kora ni yayi daga dakinsa zaki zo kina min wata maganar!"
Jauhara ta yi shiru na lokaci mai dan tsayi tana dubanta da yadda take kai kawo tana sake maimaita mafita take nema
A tausashe ta ce"AUNTY, kin fa san waye namiji, kin san me namiji ke iya yi saboda wannan abin, kin san da yawan maza basa tunani da kwakwaluwarsu sai da abin nan dake jikin su, AUNTY kina gani, ke sheda ce, tsoho na iya zuwa ya dauko yarinya karama ya aura, ya kawota cikin matan da shi ya kashe ya ragwagwaba, kina tunanin tsabar soyayya ce ta sa mutumen da ya yamutse auren yar shilar da zata iya zama Y'ar jikarsa?, AUNTY da yawansu har su kai lokacin da za'a ringa musu duban wane idan an wuni da shi ba lalle ya kai safe ba saboda tsufa da shekaru ama jikinsu bai gajiya ba.........., ba fa abin wasa bane ba.....Ki yi hakuri , Ama idan ba fuskantar mijinki kika yi ta fuskar da ya fi fahimta ba, baki da wata mafita...., wai yaya aka yi Ni da ban je dakin aure ba na san cewar idan har mace bata ba namiji wannan abin a kan lokaci a inda ya so ba, ba zai taba yi mata abinda take so ba itama?, AUNTY Walahi duk wani saurin fushinsa a kanki, saurin yi maki fada, rashin tsayawa yayi fira da ke irin na da , shawararku na nema ta gagari zamowa daya......saboda wannan abin da yake ganin ya fi karfi Ama kike masa fin karfi ido da ido, ki yi hakuri Aunty Ama kin ga idan baki yi gaggawar gyarawar ba, komai na iya faruwa kuma kar ki tuhumi kowa sama da kanki, saboda ya dace ace ke din nan da kanki ne zaki fadawa wani waye mijinki, kuma ke kin san idan hakurin ne ma ai yayi, Ama kin kasa daukan matakin da ya dace kina ta wahalar da shi, ai kin san mijinki ba mazinaci bane, da yana taba watanki da tuni ya ba kansa lafiya da ke AUNTY, Ama ki yi hakuri dan na kula ina hasala ki, Ni kam bana so ku kai matakin da zaki yi kukan mai suna kuka, shi yasa nake so ki gyara tun wuri bai kure maki ba ki daina tunanin wai ya dubi watanki ba, ki gyara tsakaninki da shi, ke ina ruwanki ma to da ya kula wata? Ke ai aljihunki a cike, kina samunsa lokacin da kika so, Ni wallahi in dai zan samu haka ko? Lafiya lau ne ka yi aurenka dan in riinga tsallake lokutan ganinka ma, domin Ni ba zan iya auren namijin da kullum zan gani Bama gaskiya, ina iya tsanarsa ne"
A hankali ta sauka daga gadon ta yi waje saboda ba zata iya zaunawa ta kwana tana mata kuka ba, bayan sai da ta hana ta wannan abin, ita a yanzu abinda ya fi bata haushi irin yadda ta ki ta sake ganin wani likitan ba wanda ya mata wannan aikin ba, tana matukar jin haushin yadda ta ki ta dauki matakin da ya dace a lafiyarta, tsoro take yi kar aje fa wanda ya mata aikin nan ba wani kwarare bane, tsoron da ya fi damunta shi ne da take ce mata kawai ta je ta yi aikin da yake kokarin daukar mata shekara bata warke ba, yanzu idan ta samu ciki a haka yaya zata iya rainonsa komai na mata ciwo ? Sai take ce mata waye zai samu cikin? Ke yanzu dan banda hankali zan je a min abin nan kuma in zo in yi garajan daukan lalurar da zata sa komai ya koma baya? A'a gaskiya ........wannan abin ya saka ta a rudu ta tarin tunani da tsoro, kar dai aje yar uwarta ta sa an taba mata harkar trump saboda son duniya da son burge namiji? Kar dai ta taba kofar mahaifarta ko an cire mata ita saboda kar cikinta ya sake zama kato? Kai da ta yiwa kanta ila mafi kololuwar da ba zata taba iya samun nutsuwa a duniya ba...........